PAGE 67&68

178 13 0
                                    

🌸 *HASEENAH*🌸

    Story &written
          By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS- 08144932303
# http://

Follow me on wattpad@ Aysherabbakar

*67~68*

Hanun Haseenah ya fara tsami saboda tun da ta mik'a mishi bata sauke hanun ba, gashi yayi kaman bai san tana wajan ba, ga shi ba magana take ba ballantana ta mishi magana.

Hanun ta ne ya fara rawa nan hawaye ya cika mata ido.

Ran Sameer ya Kai mak'ura wajan 6aci, duban shi yayi cikin tsawa yace" Mahmud wai baka ganin ta ne? Ko ba dakai take ba tsaban iskanci zaka bar mutum tsugune wajen sekace dabba eyee?"

Sai a lokacin ya d'ago ya dube shi sannan ita ma ya dube ta, maida duban yayi kan Sameer sannan yace" to bro Ni me Zan mata? Gani nayi ba aikanta nayi ba,  to ya zanyi da shi?"

Wani baƙin ciki ne ya tokare mak'oshin Sameer, a karo na biyu zai yi magana Muryar Ammi ta dakatar dashi, ji yayi tana faɗin" wlhy Mahmud in baka kar6a abun da yarinyar nan take baka ba sai ranka ya 6aci, shashasha wawa kawai"

Da sauri ya d'ago ya dubi Ammi jin ta kirashi da wannan sunan, ya maimaita a ranshi, tunda yake Ammi bata ta6a faɗa mishi irin wannan sunan ba.

Wani kallon banza ya watsa wa Haseenah da har lokacin kanta na ƙasa, hawaye na zubowa daga idon ta.

Kar6a yayi a wulak'an ce sannan ya mik'e ya bar wajan.

Kasa mik'ewa Haseenah tayi a wajan, dalilin k'unan da take ji cikin zuciyar ta, tanbayan kanta take me tayi wa wanann yaron? Me ta tsare mishi? Ko ganin ta da zaman gidan su ne baya so? Nan take ta bawa kanta amsa hakan ne ma.

Lokacin hawayen ya tsananta da zuba, haka ta kasa tashi dan Bata so Ammi da Sameer su gane halin da take ciki.

Amma ta k'uduri Niyan in Allah ya yarda nan ba da dad'ewa ba zata bar musu gidan su.

Lokaci take jira, itama baisan na dole take zama ba, tana buƙatar dangin ta.

Kuka ne taji na shirin k'wace mata, da sauri ta mik'e haɗe da toshe bakin ta da mayafin kanta ta yi hanyar d'akin ta da gudu.

Lokacin da Ammi da Sameer suka kula da halin da take ciki ba k'aramin damuwa suka shiga ba.

Dafe kanshi Sameer yayi a hankali a furta " Ya Salaam"

Ammi kasa magana tayi, to why it's Mahmud behaving like these ne?

Da sauri Ammi ta mik'e ta nufa hanyar d'akin Haseenah, amma cikin rashin Sa'a ta datse k'ofar da key, amma kanajin shesshek'ar  kukan ta daga wajan.

Sameer ma da ya biyo bayan Ammi kasa k'arasa wa yayi, jin irin kukan da Haseenah take yi.

Ga Ammi na bugun k'ofar amma bata ma ji ballantana tasan Ana yi.

Dan haka duka juyawa sukayi jiki a sanyaye suka bar wajan.

Sameer sama ya wuce ya nufa d'akin Mahmud.

Lokacin kuwa Mahmud na rungume da perfume d'in da Haseenah ta bashi, k'amshin turaren ta wanda ta shafa a hanunta kawai yake bi.

Kana ganin shi zaka yi tunanin gaula ne ko ya zauce.

Jin an bugo k'ofar da ƙarfi ya sashi mugun razana, a lokacin turaren ya fad'i k'asa.

Kallon shi Sameer yayi sannan ya jingina da jikin k'ofar, nuna shi yayi da yatsa sannan ya fara faɗin" wallahi Mahmud tunda muke baka ta6a ganin 6acin raina ba, akan yarinyar nan na rantse da Allah xan iya dagaka daga k'asar nan in maida ka wata ƙasar, in Kuma kana ganin wasa ne try it nd see, I mean my words, u know who I am nd what am capable of, so don't tryna provoke me"

Yana gama faɗin haka ya fice a d'akin.

Tsuru-tsuru Mahmud yayi da ido, dan yasan zai iya aikata abinda ya faɗa, to meye yake nufi da yarinyar ne eyee?

To wallahi se yayi sanadiyar barin ta gidan kowa ma ya rasa, sedai duk abinda zai faru ya faru, yarinya sai kace aljana.

Da wanann tunanin ya koma ya kwanta abin shi.

Can Haseenah kuwa tafi 1hr tana kuka, ba wai kukan abinda Mahmud ya mata bane, abunne ya tuna mata abubuwa da dama da ya faru a baya, na farko Umman ta, na biyu Aaman, sannan Abbanta, ga su Mummy Zuwaira, baby Umaimah, uwa uba Haseen wanda bata san a wani hali yake ba.

Ba abinda take tunawa sai ranan da suka rabu na k'arshe, wannan dalilin ya sa hankalin ta ya tashi, taji garin ya d'aga mata hankali, gidan ya mata zafi da k'unci, ba don ko dan batason ganin dangin ta bane ya sa ta kasa tafiya.

A'a so take ta gama samun lafiya kunnenta ya dawo, saboda tasan in ta koma yanzu tashin hankali ne dan batada bakin bayani, ga Mummy makira tsab zata ƙaryata ta kuma ba bakin bayani, dan haka lokaci kawai take jira.

Da wanann tunanin ta mik'e ta shige toilet ta d'auro alwala.

Nafilfili ta hau yi tana addu'a tana kuka, roƙon Allah take Allah ya tausaya mata ya dawo mata da jinta dan samun mafita.

Haka ta cigaba da kai kukan ta wajan Allah har tsakiyar dare.

Nan kan sallayar bacci ya kwashe ta, da asuba Ammi tazo dan duba Haseenah amma bata buɗe k'ofar ba.

Haseenah ko bata farka ba sai wajan k'arfe 6:30am.

Da haka da sauri ta mik'e ta shige toilet....

For comments 08144932303

HASEENAHDonde viven las historias. Descúbrelo ahora