PAGE 89&90

249 25 0
                                    

🌸 *HASEENAH*🌸

story &written
      By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ,  ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303

Follow me on Wattpad@Aysheabbakar

*89~90*

Cikin kid'imewa da damuwa saratu ta k'araso wajan mum sannan tace" Mummy me ya faru?"

Cikin gigita Mummy ta Bata amsa " wallahi Haseenah ce, bata mutu ba itace"

Shuru dukan su sukayi na d'an wani lokaci sannan saratu ta sake cewa" to amma ya akayi haka bayan kuma har kabari aka saka su?"

"Nima abunda ya d'aure mun kai kenan da har yanzu na kasa fahimta da kuma gano amsar"

Mik'ewa Mummy tayi ta shige cikin d'akin, fitowa tayi hanunta rik'e da key na motor da gyalen a kafad'arta dan ko yafa shi ma ta kasa yi.

Dubanta saratu tayi sannan tace" Mummy Ina zaki a wanann yammar?"

Ta bata amsa a tak'aice" ai zama bai ganni ba, dole inje in bincika inji ainihin labarin"

Bata sake cewa komai ba ta fice daga gidan, a guje ta figi motar ta saura kad'an ta bige me gadi yayi tsalle ya koma gefe.

Bata tsaya ko ina ba sai gidan mum Haseen.

Ko parking me kyau bata yi ba ta kutsa cikin gidan, tun daga k'ofar palour ta fara k'walla mata kira.

Da sauri mum Haseen ta fito jin irin kirar da ake mata, karo suka ci tana k'ok'arin shiga d'akin.

Tsayawa tayi suna duban juna, Mummy sai faman wangale hanci takeyi, murmushi mum Haseen tayi dan abun ya so bata dariya, gintsewa tai sannan ta ce " mun wuni lafiya?"

D'aga mata hannu tayi sanann tace" ba abinda ya kawoni ba kenan"

" To ki zauna mana yaya" mum Haseen ta fad'i haka.

Ba musu ta zauna sannan ta dubi mum Haseen tace" ki fad'amun ya akayi Haseenah ta dawo kuma kinsan tana raye amma baki sanar dani ba"

Cikin d'aure fuska tace" yanda abun ya taho miki a bazata nima haka naji, dan Haseen ne ya kirani lokacin da ta dawo naje gidan hajiya Zuwaira na tarar da ita"

Gyara zama mum tayi dan anzo wajen, dama labarin take so taji.

Jin mum Haseen tayi shiru ya sanya Mummy cewa" uhm ina jinki se kuma me ya faru?"

Bata tsaya 6oye mata komai ba nan ta sanar da ita yanda abun ya faru.

Tun kafin ta gama bata labari riga da d'an kwalin Mummy suka jik'e da gumi, ga sanyin AC amma ji take kaman wuni tayi tana yawo a rana.

Gyalenta ta janyo ta fara fifita ba shiri tana girgiza kai.

D'aura hannu a ka tayi tana furta" na shiga uku, wanann shine anyi ba ayi ba ai"

Cikin rashin fahimta mum Haseen tace" ban gane me kike nufi ba"

" To ai an kashe maciji ne ba a sare kan ba, wanann ai shirme da aikin banza nayi"

Kan mum Haseen ya kulle dan bata gane yanda maganar ta dosa ba.

Amma ganin rikicewar da Mummy tayi ya sanya ta yin shiru.

Mik'ewa Mummy tayi ta nufa hanyar fita.

Mum Haseen na mata magana amma ko sauraron ta batayi ba.

Mota ta sake shiga ta nufa gidan k'awarta me bata shawara a fad'anta wai.

Nan ta kwashe labarin komai ta fad'a mata.

Shuru tayi tana jinjina Al Amarin, can ta dubi Mummy tace " to ke wani mataki kika d'auka?"

Wani ajiyar zuciya tayi ta furzar da iska mai zafi sanann tace" ai tunda kika ga nazo wajanki to mafitar nake nema"

Can tace " kinga dai yarinyar nan tuntuni tsoron ki take ji, to meze hana ki azabtar da ita ga yanda sai ta nutsu ta bada kai dan dole?"

Shuru Mummy tayi sannan tace" ke yanda fa naga yarinyar nan ta dawo wlhy na Razana, ga wani kyau da ta k'ara kamar ba ita ba"

Tsuka Hajiya Xulaihah tayi sanann tace" to meye na karaya da wuri, ki gwada abinda na fad'a miki mana in Abu ya gagara kema kinsan akwai mutumin mu ai, ze gyara mata zama"

Sai a lokacin hankalin mum ya kwanta ta saki murmushi sanann tace" shiyasa nake k'ara sonki tawan"

Nan suka ci gaba da maganar su sai magrib sanann Mummy tayi shirin komawa gida.

A tare suka danno da hancin motar su gate d'in, Haseen ne ya fara shigewa sanann Mummy tabi bayan su.

Fitowa sukayi a motar dukan su, Umaimah da Baby Suka kwashi ledodi da kayan suka shige.

Haseen da Haseenah da kuma Aaman na tsaye.

Kasa fitowa a motar Mummy tayi ta zuba musu ido, Aaamn da ta gani duk shi yafi tsaya mata a rai dalilin shi d'in na miji ne.

K'wafa tayi ta girgiza kai cike da takaici.

Sallama sukayi sanann Haseenah ta kama hanun Aaman suka shige gida.

Juyowa Haseen yayi ze koma mota suka had'a ido da Mummy.

Kau da kai yayi kaman bai ganta ba, hakan ya dad'a 6ata mata rai.

Da sauri ta fito ta tarar dashi na k'ok'arin rufe murfin motar.

Kama murfin tayi sanann tace" mara kunya ɗan iska, kaje ka 6oye yarinya kun gama iskancin ku hakan bai maka ba seka biyota gida?"

Maganganun Mummy sun masa zafi amma ya dake ya gyara zama ya dubeta sanann yace" to ai Ni nawa iskancin me license nakeyi wata kuwa uwarta na kallo ake zuwa har gida a d'auke ta sai kuma Randa Allah yayi ta waiwoyo gida"

Shuru ya ratsa tsakani sannan ya dubi Mummy ya cigaba da cewa" kinsan ya ake kiran masu irin wanann iskancin? Karuwar gaban iya"

Yana gama fad'in haka ya ja murfin motar shi ya tayar ya sa kai.

Nan Mummy ta tsaya kaman an dasa ta a wajen, kaman bishiya haka ta tsaya ta kasa motsa wa.

Kusan minti biyar tayi wajan da k'yar ta ja k'afar ta ta shige ciki.

Maganganun haseen ba k'aramin dakatar mata da tunani yayi ba, gaba d'aya ya birkita mata lissafi, wanann shine ake kiran in kasan na fad'a baka San na mayarwa ba.

Wato yau Haseen ne ya kira saratu da karuwar gaban iya?

Girgiza kai tayi ta shige d'aki.

A ranta kuwa neman yanda zata bi ta k'untata musu take.

For comments 08144932303

HASEENAHWhere stories live. Discover now