PAGE 123&124

220 14 0
                                    

🌸 *HASEENAH*🌸

Story & written
      By👇🏻
'''Aysher Abbakar ChuChu (Meerah)'''

® *Real Pure Moment of Life Writers* *P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

Follow me on Wattpad@ Aysherabbakar

*123~124

Jin muryar baby na ihu ya Sanya su mummy fitowa da sauri,  ganin baby sukayi tana kuka, "lafiya?  Meye yafaru? "

"Haseenah ce"

Da gudu suka nufa d'akin ba tare da sun sake tanbayan ta ba.

Su umaimah da su saratu ke tsaye suna jijjigata ta,  tsawa mummy ta daka musu ganin duk cikinsu babu me hankali a jikinshi Sannan tace" ku tashi ku bata waje ta sha iska"

Mik'ewa sukayi suka matsa,  mummy ta d'auko robar ruwa ta watsa mata.

Wata salati haseenah ta sake lokaci d'aya ta saka kuka.

Kama hanunta mummy tayi tana matsawa.

Rungume mummy tayi tacigaba da kuka.

Shuru duka sukayi suna sauraron kukan ta. Mummy ko kasa janyeta tayi a jikinta,  shafa bayan ta kawai take alamar rarrashi.

ba Wanda yayi yunk'urin bata hak'uri, saboda ita kad'ai tasan abunda take ji, shiyasa suka barta Tayi kukanta ko zataji sanyi a ranta.

Ganin its almost 11 gashi 12 akace za'a wuce ya Sanya mummy janyeta a hankali,  sai faman ajiyan zuciya take.

Kama hanunta Tayi suka fita a dakin,  kai tsaye dakinta ta wuce da ita,  suka shiga toilet ta wanke fuskarta.

Tana fitowa suka shige bedroom ta kulle k'ofar,  zaunar da ita Tayi a Bakin gado sanann itama ta zauna a gefen ta.

Rarrashin ta ta fara yi Sannan ta fara mata nasiha,  wani kukan haseenah ta farayi mummy ma na tayata.

Mutuwar ummah ya dawo musu sabo.

Kasa cigaba da magana mummy Tayi sai kuka da dukan su sukeyi.

Mummy ce kawai ke furta " Allah ya isa mana,  Allah ka saka mana ka bi wa er uwata hakkinta,  ka gwada wa matar nan ishara ya Allah ka mayar mata da nufin ta,  kayi maganinta ka Nuna mata ikonka ya Allah "

K'arar wayarta ne ya katseta Daga sambatun da take,  ganin daddy ne ke kiranta ya Sanya ta d'agawa.

ji Tayi na fad'in" ki shirya su motoci suna hanya"

Kafin ta amsa ya kashe wayar.

Kallon haseenah Tayi tace" tashi ki shiga toilet ki sake wanka Kiyi sauri Karki bata lokaci ina jiranki"

Ba musu ta mik'e ta shige toilet.

Waya mummy ta d'auka ta kira sister ta wato mummy hajara ta sanar mata su shirya su umaimah da baby ynxu mota na hanya.

Cikin k'ank'anin lokaci aka fara shiryasu.

Mummy da kanta ta shirya haseenah Cikin voil lace orange colour da touches d'in bak'i a jiki.

Fesheta Tayi da turaruka masu kamshi.

Kallonta Tayi duk se tausayinta ya Kama ta.

Ganin tana shirin kuka ya sanya ta Kama hanunta suka fita.

HASEENAHWhere stories live. Discover now