143

7K 296 2
                                    

Sanda ya nufi sashen xuhura kuka ya sameta tanayi a falonta bai bi ta kanta ya nufi part dinsa dan gabatarda sallah

da dare yana kwance tunanin ummi ya adabbeshi sai ga zuhura ta shigo ya rumtse idonsa tamkar mai barci

ta hau gadon tana kallonsa tana son mijinta sosai, kishinsa ne yayi mata yawa haka

takai hannu ta dora a kumatunshi a hankali ya bude ido suka qurawa juna ido

yace zuhura meyasa kike yin abinda xaisamu mu sami sabani bayan kinsan sone ya hadamu, bnsan inda kika koyo wannan halinba bnsanki dashi ba

idanuwanta suka kawo ruwa
da ne kasoni amma ynxu ummy kakeso dan kaga ita xata haifama yara

yace inji waye, abinda kikayine sam bai kyautuba,kefa kika sameta acan banason kina zubar da kanki a gurinta yawan fadanku xaisa raini ya shiga tsakaninku ni kuma baxanso ta rainakiba

kuma da kin kwantar da hankalinki ummy fa ba wai tana sona bane kinji ta fada da bakinta,dole aka mata, bakiji ma tana cewa mijinki ba alamar bada ita ba...

tace tor kai kanason ummin ne? ya riqo hannunta yana murzawa a hankali, idanunsa a cikin nata

yace ummi jininace, mamanta da mamana uwa daya uba daya, mahaifin ummy ya riga abbanmu rasuwa accident ya samu akan hanyarsa, mahaifinmu kuwa ciwone yayi ajalinsa,

tun bayan rasuwar mahaifin ummy take xaune a gun umma saboda momy na yawan tfye tfye qasashe, lokaci lokaci take xuwa da ummin idan suna hutu a skul,

ummi babanta ta biyo shiyasa kike ganinta choco, nida faruq muka biyo iyayenmu idan kin lura ai da momy nake kama sai ki xata itace ta haifeni...

ummy ce kadai mace garemu a ynxu kuma qarama, shiyasa kikaga iyayen biyu sun shagwabtata suke mata duk abinda da takeso hr kike ganinta kamar sangartata

bnsan ummy ba bamu taba haduwa da ummy ba sai bayan aurenmu, dalili banan nayi karatuna ba, a shekara sau daya muke samun hutu idan naxo ba lallai bane naje inda momy shiyasa

kinga idan nace maki banason ummy nayi qarya,qanwatace, sanda nace maki banasonta sanda umma tace xatamin aure bnsan kowaceceba kekuma kin tada fitina shiyasa nace maki banason auren, amma bayan kawo ummy gidannan na taba furta miki banason ummy, ya tambayeta idanunsa akanta

ta share hawayen fuskarta tana girgixa kanta

yace tor meyasa kika cewa ummin ninace,tayi shiru

yace idan kika kama girmanki xakiji dadin xama da ummi,ummy batada hayaniya a ynxu duk da hr ynxu akwai wasa a cikinta,kidaina fada da ita pls zuhura

ina sonka baxan iya jure ganin wata a tare dakaiba

ya rungumota jikinsa yana fadin xaki iya *matar sadiq*

hr cikin ranta taji dadi,ta kalleshi da murmushi a idanuwanta kafin takai bakinta wuyansa tana sumbata.......

*

Washe garin ranar ba zato ba tsammani sukaji dirar motoci a gidan, sadiq yafara fitowa da mamaki ganin su momy,umma, talatu, faruq da matarsa anty bebi sai yaronta adnan dake hannunta

kai tsaye part din ummy suka nufa tana xaune tana game dinta na jaraba gefenta tea ne da tedy dinta

jin motsinsu ya sanyata juyowa, ta saki ihu bayan ta saki hannun game taje ta rungume umma, kafin ta rungume momy,tasanya kuka
[8:24AM, 7/21/2016] Pherty馃帳馃懐: faruq yace lallaima yarinyarnan, dadi kikaje shiyasa kike kuka dan kinganmu umma tariqo suka shiga ciki

anan falon suka yarda xango, sai ga ummi akan cinyar umma sai zuba take cikin farinciki

sadiq kallonta yake da mamaki ashe haka ummy take amma take takura kanta a gidan

faruq ya taso yana fadin ke daga mata a qafafu karki qarasamana tsohuwa gwanda ke ynxu kike

tayi saurin qanqame umma tana dariya
tace ba ruwanka ka kyaleni

umma tace ka kyaleta ina ruwankane

talatu tace ynzu da da ai ba daya bane hajiya,

kubarta tayi abinda takeso autace,idan bata hau ba waye xai hau acewar anty bebi

umma tace kedai fada masu matad faruku, duk suka dauki dariya

umma ta dubi sadiq fuskarta ba annuri
tace matarka bataji xuwanmu bane komu take jira muje mu gaidata ga yar'mulki

jikinsa a sanyaye yace inaji bata sani bane bara na kirata..... umma ta tabe baki tana kallonsa hrya fice

ummy tace tor ni mekuka kawominne ina tsarabana

faruq yace tunda munkawo qafafu aiba tsaraba

umma tace ni'ya'ta me aka dafane yau a gidan

tayi far da ido tana kallonta

tace umma ni komai bana dafawa fa,ban iyaba

toh fa,mekike cine,wake dafawa?
tace mai aiki
umma tace ke ummy ai girki shine mace ke ynxu sai kibari mai aiki tana yiwa mijinki girki kekuma ki xauna xaman game da charting

ummy tayi kamar xatace ai baya xama ballantana yaci abinda ko kwana bai tabayiba anan...

momy tace ynxu ga talatu nan xamu barmiki sai ta koyamiki girkin ko bakyaso, ta tunxure baki

inaso dai dai lokacin sadiq ya shigo tare da xuhura

hr qasa taje ta gaidasu ba laifi umma ta amsa fuskarta kadaram kadahan, batajima ba tatashi tafice

yinin ranar farinciki ya cika xuciyar ummi ganin yau gata tare da iyayenta, adnan ma a hannunta ya yini baqaramin jin dadi tajiba datajima anan gidan xasu kwana

da dare dole sadiq yadawo sashen ummy kada iyayensa su fahimci wani abu ya nufi dakinsa ya kwanta, suma a dakin ummy suka baje momy da umma da talatu, faruq da matarsa aka kaisu masaukin baqi

ganin ummy na gyaran wurin kwanciyarta yasa momy ke kallonta galala

tace ke ummy badai anan xaki kwantaba

tace anan mana, ina zan kwana ne momy?

tace dakin mijinki mana sai mu kibarmu anan mu kwana,

gabanta ya fadi dan bata taba kwanciya dashiba hassalima akwai nauyinsa atare daita gameda kwana dashi, tayi rau rau da idanu xatayi kuka

tace momy kibarni anan pls k.....ke rufamin baki kinji,ki dauki kayanki kije dakin mijinki dacan dakike xuwafa dan kin ganmu kike kawaici

talatu tace ke ummy sokike ya kwanta shikadai ne bayan gaki

tae mama talatu banfa taaa xuwa dakinshi ba shike xuwa nan shima fa......momy ta katseta cike da bacin rai tor ynxu tunda gamu saikije, inbnda sadiq yama zai riqa biyoki dakinki maimakon ke kibishi maza ki dauki kayanki ki fice

umma na xaune tana jinsu, qala dai bataceba, ummy ta kalli umman ko xatayi mgn taga umma koagowa batayiba, ta soma hawaye taje ta dauki hijab dinta ta dora akan rigar barcinta, kana ta dauki blanket ta fita batare da tayi masu sallamaba...

ummy ta jima bakin qofar dakin hankalinta atashe ynda xaace su kwanta tare, hawaye kawai take sharewa kafin tayi qarfin halin murda qofar dakin, qasa qasa tayi sallama yana kwance akan gado yana danna laptop dinsa

ya amsa sallamar ya dago yana kallonta da mamaki musamman daya ganta da blanket, ta rufe qofar hade da juyowa idanunsu na sarqe dana juna....

MATAR SADIQWhere stories live. Discover now