150

6.6K 318 0
                                    

Tana tsaye ya fito ta kamashi kafin taje ta kira nurse ta maida masa drip...

Sun jima suna hira kafin su umma su dawo, umma da kanta ta bashi abinci...

Ganin ya soma lumshe idanuwansa kamar maison yin barci yasa suka fita Dan yasami Hutu,

Bayan minti biyar da fitarsu ummy tadawo dantayi wanka sai tasameshi yayi barci,ta duba kayan daakaxo matadasu akwai towel tacire kayanta ta daura towel din duk akan idonsa azatonta barci yake lumshesu kawai yayi

Sadab sadab tayi sando ta sulale xuwa bandaki wai kada motsinta ya tadashi tashiga bandaki, bata jima ba tafito da sauri take shafa mai kada ya farka yaganta da qaramin towel,kamar daga sama taji

''' yace zo ummie.''' man hannunta na subulce na fadi ta soma Neman kayanta ta kare jikinta taji yana fadin

'''kixo a haka ummie,just want to show you something.'''

Ta juyo a sanyaye tana kallonsa dai dai lokacin aka banko qofa da qarfi, ko ban fada ba kunsa xuhura ce, da gudu taje ta rungumeshi tana kuka sosai

'''Kayi haquri sadiq dina, i dont know abinda ke faruwa,i just saw the news today mrng am sorry sadiq dina....'''

Ummi na tsaye cike da mamaki ita wannan batajin kunya taje ta rungumeshi ba yayanta ba...

Ta juya ta sanya kayanta ta juyo har hr lokacin tana rungume dashi tana hawaye, sai abin yabawa Ummi haushi batasan kishiba amma tanajin wani abu ya tokare mata a xuciya batasan sanda tace

Iskancinma hr a gadon asibiti sai anyi? Zuhura ta dago a fusacce zatayi magana sadiq ya rufe mata baki da dayan hannusa da baya ciwo hade da girgixa mata kai..

'''banason hayaniya xuhura leave me alone and go away from me pls'''

Tace meyasa sadiq menayi _believe me_ bansan komai akai ciwonka umma takirani bata gayamin komai ba,yau nagani shiyasa na biyo jirgi _immediately_ bayan naga Dr .

Ta durqusa qasa ta hada hannunta da nashi tana kuka

'''please don't send me away from you, I love you bansan yaxanyi da rayuwataba please''' (mata da miji sai Allah) sai yaji tausayin ta ya riqo hannunta yana kallonta

Yace x o.k amma kisani daga yau baxaki qara tsalle garinnan ba kije wani gari ganin likita...xatayi mgn ya katseta banason jin komai umarnine a matsayina na mijinki,

Haushi ya cika ummi ganinma sun manta da ita,taja dogon tsaki ta juya xata fice ya kira sunanta

Yace ina kuma zakije ummi? Batare data waiwayoba tace waje, bata jira cewarsaba ta Fita hade da bugo masu qofar dakin gam馃檳

Ya sake ajiyar xuciya yana kallon xuhura

Yace kije ki kula da gida tunda su umma nanan ga kuma ummi ba wanda zaiyi girki ya bawa ma,aikatan gida,masu maki girki bazasu iyaba batare dakeba

Sannan ananma dole xaa riqa kawo abinci asibiti...

Tace meyasa sai ni?bakaso nazauna na kula dakai,danme ummi baxataje ba?

Yace keda ummie ba dayaba ummi batasan yanda ake tfyrda rayuwar gidanba '''you know it,''' sannan idan jinyatace na yafe maki ga mahaifiyata da qanina xasu kula dani,canma da xaki xauna lada xaki samu idan kinbi umarnina,sannan kullum faruq xaixo dake ki ganni kinji.

Ta gyada kai tana kallonsa cikin gamsuwa
Yace nagode *'''matar sadiq'''* taji dadi sosai tayi murmushi hade da sumbatarsa ,

Ummi kuwa tunda taxo dakin su momy take kumbure kumbure, dayake merah yasa an basu aminity daya Dan yanajin nauyin ace suna xaune a waje, faruq ya dubeta da murmushi ynda yaga take tsaki ajima ajima

Yar damana meke damunkine haka, tayi Masa banxa ya matso yana fadin gayamin yar qanwata ko sadiq ne? Tayi rau rau da idanunta kamar xatayi kuka,ya qara cewa Allah yasa dai ba wata nurse ke sonshiba tace xata zama *matar sadiq* ko infasa mata baki, haushi ya sanyata miqewa tanufi toilet fuuuu ta shige tana kuka,kukan da batasan dalilin yinsaba.

Tun bayan fitar xuhura yaketa xuba ido shiru baiga ummi ba hr akaxo akabashi maganinsa yasha yayi barci...

Da dare ma babuta babu alamarta sai yaji ba dadi duk yadamu kada dai ummie tayi fushi dashine?bazai iya tashiba dayaje ya rarrasheta

Yace faruq ina ummie ne?
Yace ummi fa yau hali akeji naga sai kumbure kumbure takeyi tin daxu,
Yace shigowar xuhurace fa take wannan fushin,
Faruq ya soma dariya yana fadin su ummi manya har ansa wani abu kishin miji, mijin da akace ba'a so,

Sadiq yakaimasa duka yana fadin ba wannan naceba ummi nace

Yace tor nawa zaa bani nayo biko kasan ta damanace,
Sadiq yace kayo bikon tukunna kafin na biya

Cikin dariya faruq yace _no yaya pay before serve,_ naqi wayon

Shima dariya yayi yace yau waxai kwana a asibitine?

Faruq ya dubi agogon hannunsa _to eleven_  ynxu ashema dare yayi yaya ya fada yana kallon sadiq,inaji momy ce xata kwana, umma da bebi ynxu xamu wuce gida naga kuma general ya qaro securities suna wajen qofa

Yace tor ka turomin ummi ynxu idan kafita,faruq ya juya da sauri yana fadin shikenan yaya munbarka lfy,

Umma da bebi suka shigo suka Masa sallama,

Tun sanda faruq ya gayamata sadiq na kiranta take xaune batada alamar tashi sai dataji momi tace ni bawai naji faruq yace sadiq na kiranki bane ummie?ta tunxure baki ta tashi.

Idanunsa a lumshe yaji shigowarta ya budesu yana kallonta itama shi take kallo fuska a daure

Xoki xauna nan ummi ya nuna mata kusa dashi ba gardama taje ta xauna fuskarta a daure.

Ya Sanya hannunsa cikin nata yana murxawa a hankali yana kallonta

Gayamin ummi menayi kike fushi dani,ta qara tunxure bakinta idanunta sunyi rau rau

'''ni bansan dalilin fushinkiba ummi shine kuma kikaje kika barni inda badan bebi da ta xauna daniba bansan yaxanyi da yan dubiya ba,gayamin miye laifina gayamin menayi sai inabaki haquri ummie''' ta juyo tana kallonsa idanunta taf da hawaye shima kallonta yake ga mamakinsa sai ji yayi tace meyasa any xuhura zata cema '''i love you'''

MATAR SADIQWhere stories live. Discover now