157

5.5K 270 2
                                    

Har lokacin xuhura kuka take, a zuciyarta abu daya tayarda dashi cikin al'amuranta game da ubangijinta, wato wani jinkiri alherine, gaggawa kuma na shaidanne kamar ynda tayi a baya, tayi yawo wurare da dama tana neman haihuwa, shekara kusan nawa tana neman abu ido a rufe, sai ynxu Allah yabata kacokan kyauta badan komaiba sai dan dagewa da addua datayi hade da kai kukanta garesa,

gskyr sadiq dayake fada mata komai *lokacine*, ita kenan sai ynxu lokacinta yakai, shiyasa gaggawa bata da amfani wataran, musamman ga matan ynxu dake gaggawa akan aure, burin wasu suyi aure batare da sunsan halin mutum ba, musamman idan yaron mai kyaune, sai kaji suna fadin indai akwai kudi da kyau sai na auresa komenene halinsa ba ruwana shiyasani...,meke nan?

mudaina gaggawa akan abu, duk abinda kagani da wani kai bakadashi bawai Allah baya sonka bane shiyasa baibaka a'ah lokacine baiyiba da Allah xai baka, sai kayi haquri ka jinkirta hr xuwa lokacinda Allah xai baka domin xaifi xama alheri gareka kamar ynda annabi s.a.w ke cewa,

'''ku jinkirta domin wani jinkiri alherine, na haneku da yin gaggawa akan abu domin gaggawa dabi'ar shaidan ce,'''

yau gashi Allah yabata abinda ta dadebtana buri da muradi bada kudintaba kuma bada wani taimakon likitaba ashe gskyr sadiq, taji ta qara son mijinta ta tashi ta rungumeshi, shima rungumeta yayi yana tayata murna.....

*

2 wks later

Ummi na zaune da tedy a hannunta dayan bangarenta plaintain chips ne, sadiq na nesa da ita kadan yana duba list din yaransa dana samu promotion.....

yayaaaa, ta kira sunansa, ya amsa batare da ya juyoba

wai anty xuhura itama tana da ciki? ya juyo yana kallonta
waye ya gayamiki?
umma ce ta gayamin, tace ynxu sun shirya xasu daina fada saboda anti xuhura ta sauya wai tana da kirki ynxu,
ya tabe bakinsa kawai ya juya yana abinda yakeyi

tor yaya da gskene itama xata haihu?
ya gyada kai yana kallonta cikin ido..
ta xumbure bakinta
tace tor yaya na fasa ni baxan bata nawa ba,

a'a fa ummi ke kikayi alqawari xaki bata, sannan itama tace tanaso duk xata hada ta riqe tor danme xaki tada rigima....

ta tashi tana kallonsa
Allah baxan bayarba yaya, nace xn batane dan batada ynxu kuma da takeda nata baxan bayarba kowa ya riqe nasa...

mgnr banxa kikeyi ummi sai anbata komenene kika haifa ta hada can ta riqe, kinga idan yaron ya tashi baxai sokiba xaice itace mamanshi tunda ke kince bakyasonsa bakyason kukan jariri,

ai ynxu inason abina, wlhy ni baxan bayarba

tor ainine uban, nixan bata, tun farko kekikace bakyaso kuma inbanda abinki wake kyauta kuma ya karbe,

xatayi mgn kuma sai ta fasa saboda kukan daya xomata......shikuma hr a ransa yaji dadi ynxu ummi tafara son cikinta, dama bayason wannan riqe riqennan, yafison yaronsa ya sami kulawar *UWA*

tor kibar kukan kigayamin ynda kikeso ayi, ynxu so kike naje nacewa xuhura kin fasa bata baby

ta gyada kai tana share hawaen fuskarta
kuma yaya kagayamata tayi haquri ynxu inason abina,talatu xata tayani reno..

nikam inajin kunyar fada mata ummi,ashe haka kike kyauta ban saniba nikam kokin min kyauta baxan karba tunda haka kike,

tayi shiru kawai tana share hawayenta.....

MATAR SADIQWhere stories live. Discover now