*🅰MRAH NAKE SO!♥*_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*5⃣1⃣
Wattpad: PrincessAmrah
***
A nan inda suke har duhu ya fara, rana ta fara ƙoƙarin faɗuwa. A wannan lokacin kam matan da suke cikin motar ma kuka suke. Su kansu mazan ba ƙaramin jarumta suka yi ba. Kowannensu ya buga uban tagumi, ana zancen zuci.
Tagumin ya rafka shi ma Sans. Ya fara tunanin halin da ya baro mahaifiyarsa a ciki, da kuma yadda take shiga tsananin ciwo idan ulcer'rta ta tashi. Da kuma ƙanwarsa Yamaira, ta daɗe da jigatuwa ita ma.
Bai san sadda ya fashe da kuka ba. Kuka mai ƙarfi, mai cike da zafafan ruwan hawaye.
"Yaro ka yi haƙuri ka ji? Be strong. You're a man, don't act like a woman. Just look at how the women are crying, and you, kai ma kukan kake. What's the different between you and them? There's no! Don Allah ka yi haƙuri, mu taru mu dage da ambaton sunan Allah, muna sanar da shi halin da muke ciki. Mu haɗu mu ma matan can nasiha, tare da nusar da su cewa kuka babu maganin da zai mana baki ɗaya."
Wani dattijo da suka zauna a gaban mota tare ne ya ma Sans wannan maganar, cike da ƙarfafa masa guiwa.
Rage ƙarfin kukan nasa ya yi Sans. Ya dubi mutumin da idanunsa da suka kaɗa suka yi jajur. Cikin wata disasshiyar murya ya ce,
"Baba ya zan yi? Mahaifiyata na can cikin wani hali, yunwa da ƙishi har suna neman galabaitar da ita, ga shi kuma dama tana da matsananciyar ulcer. Ƙanwata ta jigatu, har tafiya ma ba ta iyawa da kanta. A cikin kunnuwana na ji harbin bindiga, wanda ya kawo ƙarshen wayar da nake yi da Abbuna. Na baro su ne cikin wani tsohon gini, da nufin in samu masu siyan wayata, ko zan sama musu wani abu su saka ma cikkunansu. Baba ga ni a nan, mota ta tsaya mana, mun rasa mafita. Ba dole na yi kuka ba?"

YOU ARE READING
AMRAH NAKE SO! (Completed✅)
Romance"Sickler gare ta, kuma ku kuka ja mata." Ta yi shiru daga nan, dafe da goshinta, tana jin yadda kanta ke sara mata. "A kullum dad'a wayar wa mutane kawuna ake game da awon genotype, amma wasu sun kasa ganewa, sun kasa sanin darajarsa."