75 KARSHE

4.2K 274 147
                                    

*🅰MRAH NAKE SO!♥*

_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_

Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)

              Na Amrah A Mashi
               (Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

                            7⃣5⃣

END

Wattpad: PrincessAmrah

***

Sadda suka dira cikin gida a lokacin har magrib ta kusa. Maryama da su Hanan dama sun zo sun gyaggyara gidan sannan suka musu girki. Islam ma ta zo sun yi tare da ita.

A falo suka zazzauna duka ana miyar da magana. Maryama kuma suna serving ɗinsu abinci. Bayan sun gama jido kayan duka suka zauna. Ta ɗan saci kallon Annur ta ga ita yake kallo, sai ta sakar masa murmushi haɗe da ɗauke kanta. Muryar Sans ta ji ya ce mata,

"Maryama sai kika ji wani al'alamarin ubangiji ko. Ashe Farouk Sardauna jinin su Momy ne. Ɗansu ne na cikinsu."

Annur ya ce,

"Ta san shi ne?"

"Sosan sosai ma kuwa. Mallam ai da shi za ta aura sai Allah bai nufa ba. Da yanzu shi ne ba kai ba."

Ya ƙarisa maganar cikin zolaya. Bugu Annur ya kai masa. Uncle Marwan ya ce,

"Salman ka cika tsokanar faɗa na kula."

Duka aka yi dariya har da Dady da Momy. Sai dai su kam ta ciki na ciki, suna jimamin rashin gudan jininsu.

Bayan an kira magrib duk suka mimmiƙe. Uncle Marwan ya ce da Yamaira ta tashi su tafi. Maryama ta cicciɓar mata Yesmeen da ke barci. Ta ce,

"Ummina da alama ta ji daɗin barcin nan. Tunda kuka shigo take abu ɗaya."

Yamaira ta ce,

"Ai haka take da barci Yesmeen. Ba ta ko gajiya. School dai za a saka ta idan an koma hutu duk kowa ma ya huta."

Bankwana ta ma Momy. Momy ta mata nasiha kan ta ƙara riƙe zumunci, yanzu ba kamar da ba ne. Idan da kawai a matsayin matar alhaji Marwan take to yanzu ba haka ba ne, ta shigo sahun ƴaƴan gidan. Ta ma Momy godiya sosai sannan suka tafi.

Bayan Maryama ta dawo har za ta zarce ɗakin su Hanan sai Momy ta kira ta ta dawo. A ƙasa ta zauna kanta sunkuye tana wasa da yatsun hannunta.

"Maryama..."

Ta ji Momy ta kira sunanta. Da jin haka sai ta tabbatar da cewa magana ce za su yi mai muhimmanci. Ta miƙa dukkanin hankalinta ga Momy.

"Maryama a haƙiƙa bani da kalmar da zan yi amfani da ita wurin jinjina miki. Jiya lokacin da Alhaji Marwan yake ba mu labarin gwagwarmayar da kika sha na yi matuƙar mamaki. Ban taɓa tsammanin kyawawan halayen naki har sun kai haka ba. Ashe ƙaramar yarinya kamar ki za ta iya siyar da farin-cikin ta domin nema wa wani bawan Allah lafiya? Na yi mamaki sosai.

AMRAH NAKE SO! (Completed✅)Where stories live. Discover now