*🅰MRAH NAKE SO!♥*_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*7⃣0⃣
Wattpad: PrincessAmrah
***
Sai da ta sha ruwa sannan Alhaji Marwan ya ce da ita ta tashi su tafi, cewa gobe za su sake dawowa su ɗauki Maryama da Annur ɗin, sai su gana da Dr. Hamdan a gidansa.
Har gaban motarsu Maryama ta raka su, sannan ta dawo dafe da kanta, har yanzu al'ajabi bai kau daga zuciyarta ba. Tunanin yadda rayuwar Annur ta dawo a gidan su Momy kawai take, da kuma yadda aka yi aka ce wai Annur ɗin ya mutu a lokacin da aka haife sa. Ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta ce da Annur ya tashi su nufi sallah, saboda tuni aka kira magrib ɗin. Tashi ya yi suka tafi jiki babu ƙwari, shi kanshi kallo guda za ka masa ka tabbatar cewa ba ya cikin walwalarsa.
*
A hankali ta leƙa fuskar Hanan, ta tabbatar da ta yi barci sannan ta ɗaga pillow ɗinta ta jawo diary ɗin Sans. Buɗewa ta fara yi, anan ta ga head line na Bama da kuma exact day na ranar da ƴan ta'adda suka fara kawo musu hari. Tun daga harbin da ya ji an ma Abbunsu, izuwa fitarsu daga gida, suka zauna a kango, har tafiyarshi zuwa siyar da wayarsa bai bari ba. Duk abin da ya faru a wannan ranar har komawarsa Maiduguri da motarsu da ta lalace a hanya, dawowarsu bayan ya siyo musu, harbin ƙafarsa da aka yi abinci duk ya rubuta.
Ta dafe kanta cikin mamaki. Tunani ta fara yi kodai ba na Uncle Noor ɗinsu ba ne? Sai dai kuma hotonsa da ta gani a next page ya tabbatar mata da cewa nasa ne. Amma kuma a ina ya samu suna Salman (Sans)? Tambayar da ta gaggauta yi wa kanta kenan. Ba ta kai ga samun amsarta ba ta buɗo shafin gaba. Nan kuma duk abin da ya faru washe gari ne a rubuce. Mutanen da suka zo suka tsotse man motarsa suka tafi da shi Maiduguri, kai shi asibiti da suka yi, zaman da ya yi a can har ranar da aka sallame shi.
A wannan gaɓar hawaye sosai Janan ke yi, mamaki bai gushe daga saman fuskarta ba. Ta sake buɗo wani shafin, sai ta ga hoton Sans ɗin wanda yake a cikin yanayi na damuwa. Daga ƙasa an rubuta
"Tun daga lokacin da na zama gurgu na tsani kaina, na tsani komai nawa. Kamar yadda fuskata babu annuri a wannan hoton, to haka na kasance tun sadda aka naƙasa min ƙafa."
Ta matse ƙwallarta, haɗe da buɗo next page. A nan kuma tafiyarsa ce daga Maiduguri har zuwa Katsina. Ƙalubalen da ya fuskanta a tafiyar, da kuma bawan Allah'n da ya haɗu da shi a mota wanda har ya saya masa abinci. Isowarsa tasha da fizge masa kuɗin da aka yi sadda yake kan keken guragunsa.
A shafin gaba kuma haɗuwarsa da Farouk Sardauna ne. Silar haɗuwar tasu da kuma taimaka masa da ya yi ya kai shi gidan gonarsu. Ta sake buɗo wani shafin, sai ta ga hoton Bobby wanda ya saki kyakkyawan murmushi a ciki, daga ƙasa an rubuta,
"He always smiles. He helped me, and never forget him in my mind. Ina fatar ranar da Allah zai kawo min hanyar da zan rama taimakon da ya yi min, ko da kwatankwacin wanda ya min ɗin ne."
Ta buɗo wani shafin. Date da time ne duka a rubuce na ranar da ya fara shan kayan maye. Ya rubuta,
"Ba na so, amma damuwa da ta yi min yawa ta sa na fara. Na kuma ji daɗin hakan, saboda ban ƙara shiga cikin damuwar rashin dangina ba tun daga sadda na zama drug abuser."

ESTÁS LEYENDO
AMRAH NAKE SO! (Completed✅)
Romance"Sickler gare ta, kuma ku kuka ja mata." Ta yi shiru daga nan, dafe da goshinta, tana jin yadda kanta ke sara mata. "A kullum dad'a wayar wa mutane kawuna ake game da awon genotype, amma wasu sun kasa ganewa, sun kasa sanin darajarsa."