*🅰MRAH NAKE SO!♥*_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*7⃣4⃣
Wattpad: PrincessAmrah
***
A bisa stool ta zauna tana shafa mai. Ji ta yi ya ɗora fuskarsa bisa kafaɗarta, ya tsura mata idanuwa ta cikin mudubi. Kallon sa ta yi ita ma ta cikin mudubin haɗe da ɓata fuska cike da shagwaɓa. Ya janye fuskar tasa.
"Daure min fuska ma za ki yi ko?"
"Ehh mana."
Ta saki kakkausan murmushi.
Bai sake faɗin komai ba ya ji wayarsa na ƙara. Ya koma ya ɗauko ta daga bakin gado sannan ya yi recieving.
"I'll be on my way now, Dady. Na tsaya karyawa ne."
Ya juyo ya kalli Maryama.
"Dady ne. Wai in hanzarta. Ashe ma a jirgi za mu tafi, kuma ƙarfe goma jirgin zai tashi. Ki ga ikon Allah, jiya-jiyan nan ashe Uncle Marwan ya je ya binciko kuma aka yi sa'a akwai jirgin da zai tashi zuwa Maiduguri ɗin yau."
Maryama ta miƙe tsaye.
"To kuma ko karyawa fa ba ka yi ba a hakan za ka tafi?"
"To ya zan yi Baby? Pass 9 fa. Ni kaɗai ake jira har Uncle Marwan ma ya kai Yamairah, dayake tare za mu tafi da ita."
"Ina zuwa to."
Ta nufi ɗakinta.
Cakes irin na leda ɗin nan ta ɗebo masa guda huɗu. Sai ta ɗauki lemo ta saka a ledar ta miƙa masa.
"Ban yarda ka zauna da yunwa ba. Ga shi ka samu ka ci please. Sai yaushe za ku dawo?"
Ya ce,
"Ina tsammanin in dai mun samu yadda muke so to gobe ma mu juyo. Sai idan abun ya yi tsayi ne sai jibi, wanda ma ba mu fatar hakan."
"To yanzu Yaya ya za a yi? Mugunta ma ba ta bari ka faɗa min yadda zan yi ba?"
Ya mata hararar wasa.
"Ashe ma dai mugunta."
"Ehh mana."
Ya taɓe baki.
"Yadda zan yi da ke a me wai?"
"Ka san fa ba zan iya kwana a gidan nan ni kaɗai ba. Ko in tafi gidanmu kawai?"
Cikin shagwaɓa ta yi maganar.
Ya jawo ta ya haɗa fuskokinsu wuri guda, har hancinansu na gogar na juna.

YOU ARE READING
AMRAH NAKE SO! (Completed✅)
Romance"Sickler gare ta, kuma ku kuka ja mata." Ta yi shiru daga nan, dafe da goshinta, tana jin yadda kanta ke sara mata. "A kullum dad'a wayar wa mutane kawuna ake game da awon genotype, amma wasu sun kasa ganewa, sun kasa sanin darajarsa."