55 Mafarkin Annur

2.1K 258 11
                                    


*🅰MRAH NAKE SO!♥*

_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_

Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)

              Na Amrah A Mashi
               (Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

                            5⃣5⃣

Wattpad: PrincessAmrah

***

Kallonta ya yi cikin idanuwa, yana nazartar yanayin nata. Cikin sanyin murya ya furta,

"Ki yi haƙuri Fiddou, ko kaɗan ban yi hakan da nuhin ɓata ranki ba. Soyayya ce ta ja, ita ce sila Fiddou. Don Allah ki duba lamarin nan, ki min kwatankwacin koda rabin ƙaunar da nake miki ce."

Shessheƙar kuka take, tana mai ƙoƙarta ɗauko rinannun idanuwanta ta kalle shi.

Dusasshigar muryarta da kuka ya gama disasharwa ta buɗe, ta ce,

"Na amince zan aure ka Mahmouda. Na yarda, na kuma tabbatar cewa kai masoyina ne na gaske. Amma ina so ka san wani abu, cewa soyayyar Modu na nan ta yi zaman daram a cikin zuciyata. Ba zan taɓa iya hidda ƙauna tai daga raina ba. Ya riga ya bi jini da jikina. Idan ka amince za ka iya a hakan to, idan kuma ba za ka iya ba ka tahi, zan iya ci gaba da rayuwata a haka ba tare da na auri kowa ba."

Cike da mamaki ya ɗago fuskarsa ya kalli Fiddou. Shin da gaske ne kalaman da yake ji daga bakinta? Da gaske ta amince za ta aure shi? Kamar a mafarki yake jin lamarin. Abin da bai tsammani ji ba kenan, saboda tun sadda ya zo wurinta take ta faman kuka, ta gagara furta komai.

"Na gode ƙwarai da damar da kika ba ni ta aurenki Fiddou. Na miki alƙawarin zan kyautata miki, zan kula da ke, zan ba ki dukkanin gata da ya kamata ɗiya mace ta samu."

Ba ta furta komai ba, sai dai kuma har yanzu ba ta daina kukan ba. Kanta sunkuye a ƙasa tana wasa da ƴan yatsunta.

"In dai har kin shirya, to ina ga ba ma za a ɓata lokaci ba a yi auren ba. So nake na cika burin da mahaifiyata ta tafi da shi a ranta, ba tare da ta ga tabbatuwarsa ba. Abin da nake so da ke yanzu, don Allah de ki daina kukan nan, kar a je wata cutar ta kama ki. Bari in tashi in wuce, gobe da yamma zan dawo, ki faɗa wa Yaya Labib ɗin."

Miƙewa ta yi bayan shi ɗin ma ya miƙe. Ta masa sallama sannan ya fita daga gidan, tana mai bin sa da kallo har ya fice.

Ba wai son shi take ba, har ga Allah ba ta da wanda take so sama da Modu. Amma ya za ta yi? Ba ta da zaɓin da ya wuce ta amince da soyayyar Mahmouda, saboda aikin banza take, Dakon Son mahaukaci, da yanzu haka ya gama mantawa da ita ma.

***

Su suka biya mishi kuɗin motar da kansu, sai da suka tabbatar motar ta tashi, sannan suka bar tashar, cike da tausayinsa.

Tafiya daga Maiduguri zuwa Katsina ba wasa ba ce. Sosai suka sha zaman mota, wanda har sai da suka yi branching a Abuja suka kwana, saboda ta can suka bi. Dukkanin hanyoyin da za su bi a sauƙaƙen babu kwanciyar hankali, dole sai mai tsayi.

AMRAH NAKE SO! (Completed✅)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang