Shimfiɗa

3.9K 198 8
                                    

JINI YA TSAGA...... 👭

😘Um Nass 🎠
wattpad @UmNass

  Duniya ta cika da sanje-sanje masu yawa, gefe guda lokaci ya zama sakarai da kanzo ya gifta da gudu. Idan har akwai abin da ke da tasirantuwa awanan duniyar to bazai gaza ɗauke DARAJAR ALƘALAMI BA. Tabbas alƙalami yafi takobi tasiri acikin ababan da zasu zo su gifta.
  Labarin JINI YA TSAGA yana da tazara da yawa da sauran labaran da na saba zuwar muku da su.

STORY description:

Ba son ko wani uba bane samun balagurbi a cikin Ahalinsa, sai dai sau da dama ALLAH kan jarrabi bayinsa ta hanyoyi da dama.
   Duk da kasancewarsa babban Malami a garin hakan bai hana ya samu tawaya wajan gaza daƙusar da mutum ɗaya tilo a cikin Ahalin sa ba.
"Tabbas HAFSA zakka ce, daban take acikin yara na. Ni kuma itace tawa JARRABAWAR."
"DUK da ana cewa JINI YA TSAGA FATA TA CIZA, awanan karon haƙuri na ya gaza. Bazan iya zama da HAFSA ba! zuciya ta ba zata ci gaba da jurar muyagun habaicin ta ba!"
"NA san zaman ku da HAFSA ba mai ɗorewa bane HALIMA! Bazaki juri zama da ita ba. Ni na HAIFI HAFSA aciki na, na fiki sanin dafi da mugunyar halayyar ta."

sai kun shiga cikin labarin zakuga ruɗaɗɗan al'amarin da ke cikin sa, labari ne mai ban haushi da takaici.
labarin rikitacciyar yarinya mai halayyar ban haushi.

  SHIMFIƊA

Ƙofar gidan cike take da mutane, da yawa fuskokinsu ɗauke da alhini da jajjaɓin abin da yake faruwa, wanan ba shine karo na farko da suka saba taruwa awajan ba, haka ba shine karo na biyu da suka fara yi musu shari'a atsakanin su ba.

Daga tsakiyar wajan kuma wata matace tana kuka tana jan majina, hannunta ɗaya naɗe cikin bandeji wanda ya saƙalo har wuyan ta, wanan shike nuna karaya ta samu ahannun aka mata ɗori.
   "Halima kiyi haƙuri ki koma gidanki, kibar kuka da tarawa kanki mutane. Hafsat ƴar uwarki ce, ko babu komi JINI YA TSAGA FATA KUMA TA CIZA, ita ɗin dolenki ce, komi zata miki ɗole kiyi haƙuri ki zauna da ita."

Ɗagowa tayi ta kalli mai maganar idonta na ci gaba da ambaliya da fidda hawaye, muryarta har rawa take saboda zafin da zuciyarta keyi "Tabbas jini ya tsaga a tare dani da Hafsat wanda ya maida mu abu guda, amma hakan ba shi ke nuna cewa zan ci gaba da zama da itaba, Allah ya sani ban iya rigima ba, ku sheda ne akaina, zuciyata bazata ci gaba da jure jin miyagun maganganun da suke fitowa daga bakin Hafsat ba. Ƙanwata ce amma kuma ita ce matsala ta." ƙarasa maganar tayi tana ci gaba da kuka mai sauti.
'Ta riga data gama yankewa kanta hukunci, idan har Iyayensu basu shiga cikin wanan batunba, to babu makawa zata tafi tabar Hafsat agidan, zata kuma rarraba yaranta zuwa gidajan dangin su, ita kuma ta tafi wani garin, wata duniyar daban tayi rayuwa atare da su.'
_"Kawai kin dage ne Halima, amma ni na riga dana san zamanku waje ɗaya da Hafsat ba abune mai ɗorewa ba, ko kun zauna na daɗi ɗan lokaci kaɗan ne zata sauya akalar daɗin, Hafsat butsu ce haka kuma mishance mai ɓadda kamarta ta zahiri. Ni na haifeku ni nasan halin ko wacce acikin ku, ba zaki iya zama da ita ba."_

"Zan iya zama da ita Umma, zan zauna da Hafsat ba tare da hayaniya da hatsaniya ba, zakusha mamakin sauyuwar hali da ɗabi'ar da take da ita abaya. Wanan sabuwar Hafsa ce atare dani, wanda ta samu ban-banci mai yawa daga waccan da kuka sani, zan zauna da ita na sake aurar da ita akaro na uku in sha Allah, ke dai kisa ma zamanmu albarka kawai."

Kallonta tayi kafin ta girgiza kai da ciza laɓɓan ta "Kun zauna da Hafsa awancan lokacin cikin kariya da dafawar mijinki, amma kuma yanzu akwai ban-banci Halima, mijinki baya tare da ke, ƙasa ta lulluɓe ganin sa, baki da wani mataimaki sai Allah, sai kuma marayun yaran da ya barki da su. Kada ki gayyato wata matsala acikin rayuwarki, kada ki janyo Annoba cikin zuri'arki ku zauna ta tarwatsa miki kan ahalinki."

Kai ta fara girgizawa tana toshewa Umman nata baki "Hafsa ma ahalina ce Umma, ki daina aibata ta wajan kiranta Annoba, har yanzu akwai ƙuruciya atare da ita. Ki mana fatan alkhairi kawai Umma, kada ki fara wargaza zaman da ba'a kai ga farashi ba."

  "Yarinta? Yarinta fa kikace Halima atare da Hafsa, yarinyar data shekara talatin aduniya kike kirama yarinta, yarinyar da take da matashiyar budurwa ƴar shekara 15 aduniya kike kirama yarinta, Hafsan data yi aure shida arayuwarta kike alaƙanta mata suna da yarinya?"
  Kai Halima ta gyaɗa "Koma yaya ne Umma, ni awajena Yarinya ce, tunda har yanzu aƙasa na take, haka kuma amatsayin babba nake akanta Umma."
  Tashi tayi ta gyara lulluɓin mayafin ta "Ba zan musanta hakan ba, bazan kuma shiga cikin wata matsala dazata kunno tsakaninku ba, amma ina jin tausayinki Halima." tana gama faɗar haka ta fice ta barta, duk kiran da take mata bata tsaya ta saurare taba.

  Ido ta buɗe tana kai kallonta ga mutanen da suke kewaye da ita, hawaye na ƙara zuba akan idon ta "Umma tayi gaskiya, da gaske Hafsat Annoba ce, gashi ta raba tsakanina da makusanta na."

Kallonta ta kai ga inda Hafsa take, tana marairecewa agaban mutane, sai matsar hawaye take "Dan Allah Adda Halima kiyi haƙuri ki yafeni ki dawo mu zauna tare, kin san bazan iya rayuwa kina fushi dani ba." ƙasa takai tana riƙe ƙafarta, idan ta faki idon mutane kuma sai ta mintsini ƙagar ta aika mata da gwalo da dariya, amma da an kalleta sai ta koma kalar tausayi da hawayen ƙarya.

"Haba! Wata irin zuciya gareki Halima? Kinaga yanda take baki haƙuri kina aika mata da magana marar daɗi, ai naka naka ne komi zai maka, balle kuma ya roƙeka akan kayi haƙuri. Ku wuce mu tafi ku ƙyaleta."
Gaba ɗaya mutanen wajan suka fashe suka barta da yawa suna mita akan halinta na rashin haƙuri, kai da ɗan uwanka ace ka gaza haƙuri da shi har kana tara masa mutane.
Sai da mutanen suka baje gaba ɗaya sanan Hafsa ta miƙe tana karkaɗe jikin ta "Kibar ƙoƙarin bayyanar da gaskiyar da take ɓoye, saboda mutane suna yadda da abin dake zahiri ne Adda Halima. Koda bakya so ni na zama dolenki haka idan kikace zaki fiddani ta ƙarfi tofa nima ina da gado agidan nan, saboda yaranki yarana ne." tana gama faɗar haka ta shige cikin gidan tana rausaya jiki da karkaɗa mata ɗuwawu.

"Ya Allah." Halima ta faɗa hawaye na zuba akan idonta.......

JINI YA TSAGAWhere stories live. Discover now