PAGE 6-10

2.3K 172 3
                                    

Alhaji Abubakar Dan kwambo sunan sa, a garin lagos yake harkar kasuwancin sa amma shi haifafen kano ne, bai damu da karatu ba hakan ya sa ya fara kasuwanci domin ya tsirq da kansa da iyalensa yana da mata Guda biyu hajara da hauwa  kuma Allah ya albarkace shi da yara guda uku hassan da hussaini  ta bangaren hauwa sai Aminu ta bangaren hajara
Yaso ya d'ora yaran nasa a harkar kasuwancin sa amma sam Husseini yace shi makaranta zaiyi domin yanzu ilimi shine a gaba yacewa baban nasu Alhaji Abubakar. shi kuma hassan ya yarda da kasuwancin tareda dan autan su Aminu.
        Wannan ahali sun taso cikin farinciki da tausayin na qasa da kuma girmama na gaba sannan matan Alhaji Abubakar basusan menene kishi ba kansu a hade yake  kuma suna bawa junansu girma sannan ga taimakon juna .
    A cikin lokaci qanqani hassan da aminu suka fara gane komai da baban su yake nuna musu ta b'angaren kasuwancin sa,
  Shi kuwa Hussein yayi nisa a karatunsa gashi ma next year zaiyi graduating , ya kasance mutum ne mai fasaha ga koqari da kuma kwazo kuma ya taso yana son mahaifiyarsa hauwa da kuma kishiyar ta hajara.
     ~ ~ ~  ~ ~
A halin da ake ciki yanzu Alhaji Abubakar ya miqa dukkannin kasuwancin sa ga y'ay'ansa Hassan da Aminu domin ganin tsufa yazo masa bazai iya Ci gaba da juya dukiyar sa ba amma amfannin haihuwar kenan tunda yana da masu kula da dukiyar tasa.
Shi kuwa Husseini a yanzu ya zama graduate harma a yafara neman aiki kuma ciki ikon Allah ya samu aiki a kaduna Toh annan ne ya hadu da Hadiza Muhammad ya fara soyayya da ita . Saidai yana zuwa kano lokaci zuwa lokaci yana duba iyayen nasa da kuma y'an uwansa
    Saidai hankalin mahaifinsa a tashe yake don ganin tsufa yazo masa gashi kuma babu wanda yayi aure daga cikin y'ay'an sa abin dake qona masa rai kenan idan ya tuna
  ~~~~~~~~~~~~
A lokacin da Husseini yaje ganin iyayensa ne babansu yayi musu magana akan kowa ya nemi mata ya aura domin yafiso yaga aurensu kafin ya bar duniya inji mahaifinsu Alhaji Abubakar
Toh fa babu wani b'ata lokaci aka aika kaduna domin neman auren Hadiza sannan hassan da aminu kowa ya nemi matar aure kuma an basu
Farin ciki ne ya cika Alhaji da godiya ga ubangiji Daya sa zaiga auren y'ay'ansa Hassan Husseini da Aminu, cikin qanqanin lokaci aka daura auren su aka kuma kaiwa kowa matarsa wanda dama shi Husseini a kaduna yake da zama saboda aiki . Hankali Alhaji ya kwanta saidai kash ya tsufa sosai ko fita baya iya yi saboda ciwon qafa dayake damunsa
~~~~~~~~~~~
Shekaru biyu kenan da auren y'a'y''an Alhaji Allah ya albarkace su da haihuwar y'ay'a hassan matarsa ta haifi y'an biyu basma da basman Aminu matarsa ta haifi  namiji mai suna Ibrahim khaleel, Husseini ne dai haryanzu Hadiza matarsa bata haihuba amma tana nan da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe!
A yau Monday 8th August Allah ya sauki Hadiza ta haifi y'arta mace kyakyawa ga idanuwa ga kuma hanci duk da mutane suna cewa kamannin babantane amma dai Babyn tana da kyau.
  Tirqashi...... a wannan safiya da Hadiza ta haihu ne hassan ya kira Husseini domin sanar mai da rasuwar mahaifinsu. INNALILLHI WA INNAILAIHIRAJIUN .... abin da yayi ta maimai tawa kenan yana mai zubar da kwalla yana cewa Allah ya gafarta maka mahaifina yasa ka huta. Gaban Hadiza ya fadi wacce ke riqe da jaririyarta tana fadin mai ya faru? , nan ne ya shaida mata cewar babane ya rasu kuma ya kamata ya tafi kano a yau domin janaizar babansa.
   Abu dai biyi dadi ba duk da ita mutuwa dolece ga mai rai Toh babu yanda za,ayi . Husseini yayi wa jaririyar hud'uba da sunan mahaifiyar sa Hauwa , sai hadiza ta fad'a cewar za,a dinga cewa yarinya Raeesah .
   

Wannan shine asalin Raeesah D'iyar fari
Is your girl Zubaidahn Gaddafi
Show me some love by voting and comments also 😘 love you oll 💗

D'iyar fari 🧕🏼Место, где живут истории. Откройте их для себя