PAGE 11-15

1.7K 131 3
                                    

This page dedicated to mah little fly🦋 only if you know 🤪

~~~~~~~~~~~~~
Raeesah dai ta taso cikin jin dad'i da kulawa daga wajen uwa harma uba sai dai Husseini mahaifinta yafi sonta da shagwab'ata kasancewar ita kadai suka haifa kuma sunan mahaifiyarsa gareta
Sai dai wasu lokutan Hadiza batason yadda shi Husseinin yake b'ata Raeesah
Gashi yanzu bata jin maganar kowa kuma bata sauraron kowa sai rashin kunya da kuma wauta irin ta y'ay'an fari😉
Ahalin yanzu Raeesah ta kai kimanin shekaru 19 amma har yanzu batasan mai takeyi ba kuma batasan inda ta dosa ba domin ita daukar kanta take amatsayin qaramar yarinya saboda yanda babanta yake shagwab'ata kuma a kullum yake gayamata ita kyakyawace
Wannan shi ya sa take qara yiwa mutane wulaqanci da rashin mutunci da kuma nuna cewa ita ba ajinsu bace da rashi kunya da kuma sakarci irin nata na y'ar fari
Batajin storon kowa, haka a islamiyya ma takeyiwa malamai rashin kunya hatta ma d'alibai bata barsu ba duk wanda ya gayamata mutuwar uwarshi sai ta gayamasa na ubanshi (hausa proverb)😉
Gashi yanzu da taga ta kammala secondary school dinta koh islamiyyar ma bata zuwa
Amma ba da son mahaifiyar ta Hadiza ba domin tafison y'ar tata da ta samu ilimin addini kodan gaba da kuma lahira
Sai dai yanda rai yakeso ba haka yake samuba
Inji Hadiza
~~~~~~~~~~~
qarfe takwas na safe 8:00
Hadiza ce ke magana kamar haka: abban Raeesah ya kamata ka san abin da zakayi akan yarinyar nan domin koh islamiyya fah bata zuwa kuma gashi yanzu ta gama secondary school Toh mai zai hana ta ci gaba da karatu? Idan kuma ba haka ba toh gaskiya ayi mata aure tunda ta isa aure shekara goma sha Tara!  Koh kuma a sakata a catering school ? Saboda Raeesah babu abin da ta iya ..
Hadiza ita kad'ai taketa maganar ta shi kuwa abban Raeesah yana ta kai laumar dankali ko kulata baiyi ba domin duk abin da take fada basu gamsar da shi ba ita kadai take ta surkullen ta 😂.....
Sai da ta fuskanci ba ta ita yake ba sannan tace wai abban Raeesah ba da kai nake ba?
Toh maman hauwa mai zance?
Au me zakace?
Shikenan tunda baka da abin da zakace mstwww.. ta ja tsaki sannan ta juya ta b'ata rai
Saida yaga alamun ranta ya b'aci matuqa kafin yace: maman Hauwa kiramin mamana
Sannan ta saki rai ta tashi ta nufi inda d'akin Raeesah
Kai tsaye ta shiga ta ga ashe koh tashi batayiba gashi yanzu 8:29
Yanzu da haka yarinyar nan koh sallah batayiba!  inji Hadiza
Dagewa tayi ta kai mata duka a baya tana fad'in tashi dan ubanki wani daren za,a qara miki?
Bargo Raeesah taja tana fadin :  haba maman hauwa yanzu fah aka kira sallah ki bari na d'an kwanta ....
Inji ubanki toh 8:29 yanzu wallahi koh ki tashi koh in watsa miki ruwan sanyi
A firgice ta tashi saboda taji an ambaci ruwan sanyi 😅 sanan maman hauwa tace idan kin gama abbanki yana jiranki a  dining
Toh tace sannan ta fad'a  toilet da kayan bacci tayi wanka sannan ta d'auro alwala tazo ta bud'e wardrobe dinta ta dauko wata baqar riga doguwa tayi sallah sannan ta shafa mai ta hau shafa hoda  sannan ta sanya red lipgloss kafin ta fito .
Shigowar ta falon ne ya katse musu hirar da sukeyi
Zama tayi kusa da abban nata sanna tace abba ina kwana ya amsa da lafiya mamana kin tashi lafiya tace lafiya
Maman Hauwa ina kwana itama ta amsa da lafiya Raeesah ya bacci ya chatting?
Ran Husseini ne ya b'aci dayaji wannan sannan yace a,a maman Hauwa banason irin wannan tambayar da kikeyiwa yarinyar nan bai kamata ba . Toh dole in tambayeta ya chatting saboda wannan yarinyar idan ta fara chatting tun 8:00pm sai takai har 2:00am batayi bacci ba saboda Maita 🤔 inji Hadiza
Magana ya fara da cewa mamana na kiraki ki ne domin inji ta,ra,ayin ki wai shi makaranta kikeso kici gaba kokuwa aure kikeso? Kokuma kinaso a saka ki a catering school? Wanne kikeso daga ciki ?
Cikin muryar kuka ta fara magana abba aure kuma? Toh ni na isa aurene? Kumama ai idanma auren ne toh wa zan aura ? Ta qarasa maganar tana kuka .
Toh Toh... mamana dan Allah ki daina kukan nan banason gani ki daina! Shikenan yanzu idan kin karya zamu je a kaiki catering school inda zaki koyi girki da kuma abubuwa da dam ai kina so koh?
Eh! Abba d'an dama dama wannan..
~~~~~~~
Hmmmm inji maman Hauwa ana ganin abu anan , oh oh naga ta kaina ni dije 🤦🏻‍♀️.

Is your girl zubbefly 🦋
Can you vote and comment?
Pls do let me know that you are enjoying the story 🥰👍🏼

D'iyar fari 🧕🏼Where stories live. Discover now