PAGE 41-45

1.1K 88 2
                                    

Abba yayi farinciki sosai da jin wannan batu na Alhaji Aliyu amma yana tunanin amsar da Raeesah zata bashi da kuma yanda reaction d'inta zai kasance saboda bayason b'acin ranta kuma abinda takeso shi yake so
Bai iso kaduna da wuri ba sai qarfe 11:00 na dare Raeesah har ta gaji da jiransa ta shiga d'aki ta fara abinda ta saba as usual wato tunanin jameel wanda bata saniba he exists or not, ita dai abinda ta sani shine wata rana zasu qara had'uwa taga kyayyawar fuskarsa da kuma murmushinsa abin birgewa, wani lokacin ma har biro da takarda take qauka ta fara rubuta kalamai masu d'ad'i wai idan ta had'u dashi face to face zata fad'a masa kalaman.
Tana cikin wannan tinanin ne taji sallamar abba ya bud'e k'ofa da gudu ta fita ta rungume abban nata tana mai sannu da zuwa tana farinciki da ganinsa maman hauwa ce ta fito daga d'aki itama tana mai sannu da zuwa, amsasu yayi sannan yace wa Raeesah ta tafi d'aki tayi bacci da safe zasu had'u! Toh tace ta nufi d'aki sannan ta kwanta taci gaba da sana,ar da ta saba . D'akinsa ya nufa ya shiga toilet ya watsa ruwa , kafin ya fito kuma Hadiza ta gama shirya masa abinci da drinks kala kala, Bayan ya fito ne ya huta ya ci abinci sannan ya fara baiwa hadiza labarin abokinsa da suka dad'e basu had'u ba sai yau a jirgi, a nan ne ya sanr da ita cewa zasu had'a yaransu aure Toh ya take gani? Gaskiya naji d'ad'i sosai amma bansaniba koh Raeesah zata yarda a iya sanina dai nasan bata da wani saurayi da suka tab'a tsayawa inji Hadiza, toh Allah dai ya tabbatar mana da Alkhairi Ameen inji Hadiza.
~~~~~~~~~~~
Raeesah fah abu ya girma a cikin zuciyar ta har ta fara zance ita kadai kamar mai hauka duk ta sauya ta rame kamar ba ita ba, Abbane zaune kan sofa Raeesah ta zo zata shiga d'akin Hadiza, kiranta yayi sannan tazo ta zauna kusa dashi
Raeesah you look different! What's wrong with you these days?
Abba nothing!
Mamana kar kiyi min qarya ba haka na sanki ba, amsawa tayi cikin natsuwa Abba da gaske nake babu komai ! Toh mamana babu komai shine duk kika rame kamar mara lafiya........
shigowar Hadiza ne ya dakatar da shi daga magana, yauwa gwara ka tambayeta wata qila  kai zata gayama ma abinda ke damunta domin ni taqi fad'a min
Juyowa abba yayi bangren Raeesah ki taimaka ki fad'a mana abinda ke damunki don Allah ba don halinmu ba... Amma sam Raeesah ta dage akan babu komai,
Kwana biyu shima abba ya shiga cikin tunanin irin halin da y'arsa zata shiga idan ya fito mata da maganar aure musamman ma auren wanda bata saniba, a haka dai ya yanke hukuncin sanar da ita koda ranta baya so saboda bayaso yaji kunya a wajen abokinsa Alhaji aliyu , Hadiza kuwa ranta fal yake tana farinciki da hakan .
A yanzu kam Tabbas Raeesah ta  yarda da soyayya kuma ta yarda cewa son jameel take amma wani lokaci da kanta take ganin haukanta, yaya za,ayi na fara son guy din da na gani a dream bayan shi bai sanniba? Kuma toh ina xan ganshi na fad'a masa abinda ke zuciyata kohda baya sona? Ina zan ganshi ?  Allah ka yayemin abinda ke damuna ! Adduar da takeyi kenan idan ta tuna da mai umbrella da ta sawa Suna Jameel .
A yau watan Abba d'aya da dawowa daga turai Alhaji Aliyu kuwa kullum yana faman kiran abba yana tambayarsa wacca shawara ya yanke gameda auren y'ay'ansu ..... amsardai guda d'ayace kullum ina kan shawara! Shine abinda abba yake fad'a masa domin baisan ta inda zai fara ba!
A yau Tuesday abba ya shirya sanar da Raeesah  abinda ke faruwa.... Hadiza ya aika ta kiramai Raeesah a d'akinta! Toh tace ta tashi ta nufi d'akin Raeesah suka fito tare...
Bayan sun xauna ne abba ya kalli Raeesah cikin tausayi yana magana kamar haka: mamana ki saurareni da kunnen basira ki kasance mai yimin biyayya kar ki zama mai taurin kunne a gareni , Abbba ban fahimce kaba inji Raeesah! Magana yacigaba dayi Toh kamar yanda kika sani haqqinmu ne mu iyaye nu zab'awa yaranmu abokan zama na gari,
Toh shi yasa naga tunda kin isa aure in aurar dake kema ki zama mutum kamar kowa domin raya sunnar annabi, kuma na samar miki wanda xaki aura yanzu so nake inji daga gareki.....

🦋🦋🦋🦋🦋🦋
Mudai munce Allah ya sanya Alkhairi 🤲🏻.

D'iyar fari 🧕🏼Where stories live. Discover now