PAGE 66-70

1.1K 89 3
                                    

~~~~~~~~~~~
Da shigarsa wanka Raeesah ta shiga d'akin ta sanya turaren wuta mai qanshin gaske , bayan tasa ne ta nufi d'akin maman hauwa don amsa kiran da take mata , sallama tayi sannan ta zauna a bakin gado kusa da maman nata! Maman hauwa gani! Magana ta fara yi Raeesah ...naam tace! Wai Raeesah mai yasa kike so ki yi mana wasa da hankali? Menene yake faruwa? Ki fad'a min nifa mahaifiyar kice kar ki b'oye min komai Raeesah... ki fad'a min wai dama kunsan juna ne dake da wannan yaron jameel? Mamaki ne ya cika Raeesah .. amma maman hauwa mai yasa kika min wannan tambayar? A,a saboda naga da k'yar kika amince da zancen auren nan amma sai gashi daga zuwansa har kun fara hira kamr kun saba da juna !  Amsawa Raeesah tayi maman hauwa gani nayi idan ma ban ban saki fuskata ba dole ne fah sai anyi auren nan kuma na riga nayiwa Abba Alqawarin zan zama mata ta gari ga miji na , kuma bana so na sab'a umarnin Abba kawai shi yasa na saki fuska ta na kuma karb'i soyayyar sa Hmmm... maman hauwa tace , eh kuma hakane kina da gaskiya domin aure kam babu fashi Allah yayi muku albarka, Ameen Raeesah tace sannan ta fita.
K'arfe 8 da rabi Abba ya dawo, maman hauwa ce ta tareshi da labarin da yake son ji lallai kam abu yayi daidai Allah ya nuna mana auren nan, za,ayi auren da aka dad'e ba,ayi irinsa ba a kaduna Allah mun gode maka.
A b'angaren Raeesah kuwa kitchen ta shiga tana had'awa jameel coffee , sallama tayi ta shiga d'akinsa ta miqa masa coffee d'in , bayan ta miqa masane ta juya zata koma ya riqo gefen hijabin ta 😉ki zo ki zauna domin na dinga kallon ki hauwa ta! Dawowa tayi ta zauna Toh gani...  magana ta fara! yau gaba d'aya rayuwa ta ji nake kamr ina aljanna, daga zuwanka gidan nan naji gaba d'aya rayuwata ta koma sabuwa , haqiqa yau ne na farka daga baccin da nake yaune kuma mafarkina ya zamo gaskiya, nayi qoqarin yin bacci amma na kasa shiyasa na kowo maka coffee domin na qara sa ka a idanu na kafin safiya!
Idanun sa ya lumshe cike da shauqin soyayya yana mamkin yanda yarinya kamar Raeesah ta iya kalamu masu dad'i da kwantar da hankali, kusa da ita ya matso shima ya fara mata nasa kalaman yana nuna mata soyayya da qauna, bai barta ta koma d'aki ba sai 12am kafin ta koma d'aki ta kwanta a gajiye,
A b'angaren jameel kuwa kansa ya daga sama yana saqe saqe a zuciyar sa , a zahirin gaskiya jameel kyakyawa ne, dogon mutum ne mai d'an duhun fata, mutum ne mai son tara gashi , yanada fad'in kirji , kuma yasan ya kamata saidai baya son raini, shine babban abun da ya hana shi karba'ar soyayyar Class mate d'inshi Amira saboda baya d'auakr raini , sai gashi kuma lokaci guda yaji soyayyar Raeesah a zuciyar sa kamar da wasa .

~~~~~~~~~~
K'arfe 7 da rabi na safe Raeesah tayi kwalliya cikin wata koriyar riga mai daukar hankali, d'akin jameel ta nufa, tana shiga ta tarar dashi har ya shirya cikin manyan kaya yana shirin tafiya , good morning tace ... amsawa yayi cike da qauna morning my Hauwa.....  I'm ready, shagwab'a ta fara masa ... haba dan Allah ai dai ka jira 12 yayi kafin ka tafi koh !  qarasowa kusa da ita yayi sannan ya kama hannunta ya fara shafawa a hankali   Ki yi haquri I have no choice ... meeting d'ina 2 Oclock ne kuma ya kamata inje kafin 2 d'in I know you will miss me and I will miss you more... a haka yayi ta bata baki da zafafan kalamai masu dad'i har ta haqura.
Driver ta kira domin ya kai jemeel airport, sallama yayi da maman hauwa da kuma Abbanta sannan suka fito tare yayi mata sallama ya shiga mota

Zubeefly 🦋..... love you oll 😉🌸

D'iyar fari 🧕🏼Where stories live. Discover now