🍇🍇🍇💖Feeling uneasy to reveal him self to her

312 36 28
                                    

💞 SAKI
DAYA
NE💞

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEY BEE)

🎶
I don't want hear say*, you dey with another man, the way your body rotate, I no go like am, if I see u with another man, coz Nobody Nobody... 🎶
Nobody song by
Joeboy ft Mr Eazi.

🍇🍇💝1⃣8⃣

This page goes to u my kawar fada😝 my Nurse Fanty, although u are my kawar fada but I love u babe💖💓💝,

**********************************
2 YEARA LATER

Wai aka ce rayuwa ke nan, in kana da rai gudu take daga kwanaki zuwa satika zuwa watanni zuwa shekaru, wannan duk iko ne da yi na Allah,

Alamura da dama sun faru sun shude cikin shekarun nan, amman za mu iya cewa na Alkhairai ne duk suke faruwa wa Nadeen, don cikin iko da yardar Allah ta kammala Law school inta ta kuma kammala NYSC inta, yanzu Barrister me zaman kanta take,sai fara aiki kawai ya rage,

Bangaran lamarin ta da Asaad koh sai godiar Allah don koh yanzu wata irin soyayya me karfi da zafi ne ta shiga tsakanin su, inda duk su biyun ke jin basu iya rayuwa ba tare da juna ba,

And har yanzu be fito ya sanar da ita anihin koh waye shi ba, gudu da tsoron rasa ta da yake yi, soyayya me tsafta da zallar kauna suke a junan su, kusan kullum in ta sanar da shi ita fa tana son su hadu, ya ringa kawo Excuses ke nan, ya sanar da ita surprising inta yake son yi, but he make her promise him that koh yaya ta same shi bara ta guje shi ba, ba tare da wani tunani ba Nadeen ta amince don soyayya ta rufe mata ido,

Ita kanta har mamakin irin son da take masa take yi lokaci daya ta fada cikin soyayyar sa da ta mata mugun kamu, don kullum bata da magana cikin su Elhaam sai na Muhammad inta, su Elhaam har sunyi mamakin har sun gaji sun daina don ganin inda kawar ta su ta iba son da zafi, gefe daya kuma Elhaam na jiye mata tsoron kar ta zo wataran ta ganshi ba yanda tayi zata ba a samu matsala, don irin wannan blind love in na da babban ila, Deenerh kuma tsoron randa asirin ta zai tonu take yi don sarai tasan inda Nadeen ta tsani sojoji, and tana tausayawa yayan ta randa ta gane shi ta rabu da shi, bata san ya zai kare ba, don ta lura ba karamin so yakewa Nadeen in ba, wannan ke nan,


Zaune take gaban maamee kaya ne a gaban su, tun dazu kusan rabin hour ke nan suna zaune, ita da maamee kuma ba zaman komai suke yi ba illa na taya ta zaban kayan da zata sanya zuwa partyn da zasu yi anjima ita da kawayen ta wanda suka kammala NYSC tare,

Nadeen Allah na gaji since kin zaunar da ni nan kuma kin kasa zaban kayan da zaki sanya, tun dazu sai na zaba kice be miki ba, kawai ni zan tafi ki zabi abunki da kanki,

Turo baki Nadeen in tayi kafin tace kai Loml, in baki taya ni zaban kayan ba, gun wa xani, ga kakanki da baban ki, ke ga ma son duk zasu iya ai, but amman maamee duk zabin su bare kai naki ba, sweet talker ba a banza zaki zama Bars ashe ba mutum sai dadin bakin tsiya, but seriously Allah wannan karan shine last zaban da zan miki in dai har be miki ba saidai ki zaba da kanki kin yarda don nima ina da abun yi, okey sweetheart na yarda,

Nan maamee ta shiga duba sauran kayan don ganin wanda ya dace yar nata ta saka, can koh idon ta ya saukan kan sabon gown in da ta siyo mata a Dubai last 6 month,

Seriously daman baby baki taba sa kayan nan ba, kika sanya na baki and kin san tsadan sa kawai kin zo kin aje baki da niyar sawa koh,

My God Nadeen ta fada a ranta ita kam ba tama gama mantawa da gown in da maameen ta siyo mata ba,

Toh Allah shi zaki sanya yau, tuno yanda suka yi kan wannan ne zaban karshe, and har yanzu ita fa bata ga abunda ya mata ta sanya ba, ya sanya ta murmushi tare da fadin good choice maamee na, ai saboda irin haka ya sanya ban ma taba sanya sa ba,

SAKI DAYA NEEHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin