🍇🍇🍇💖Arguments

227 44 62
                                    

💞SAKI
DAYA
NE💞

WRITTEN AND STORY
                    BY
NERNAH MARYAM
(MARTEY BEE)

🍇🍇💝2⃣9⃣

This page is for u my biggest fan Fateemah Lawal Usman(Meemee) , love u load dear stay blessed 💖💞,

***********************************
A hankali Nadeen ta fito daga cikin motan a jere suka tako zuwa main door in part in mom, haka kawai Nadeen ta ji gaban ta na faduwa a hankali ta lumshe idanun ta tare da karanto addu'ar 'Hasbiyallahu wa ni'imal wakil',

Suna gab da shiga tace baby yes my love yace yana me kallon ta, babe tsoro nake ji pls don't leave me ka ji, pls relax mana ba ga ni ba mu shiga pls kin san maamee tace bata son muyi dare, don haka ki nutsu kin ji, da kai kawai ta amsa masa sannan ya bude kofar suka shigo da sallama fuskan Nadeen a kasa,

Mamaki sosai yayi ganin Haj Zuwairah da shegiyar diyar ta Meedah zaune a parlour ga mom da Hibba ma, rashi ya baci amman ya danne don har ga Allah be san dalilin zuwan na su ba and haka kawai ya ji ba zuwan Alkhari ba ne,

Mom na zaune ta daura daya kan taya Meedah na kwance a jikin ta, tabo ta haj Zuwairah tayi tare da nuna mata su Asaad da ido, 

Ai ko sai gani nai mom ta washe baki tare da mikewa, ahh maraba daughter yau ke ce a gidan na mu, nai fushi ai wato baki taba ce masa za ki zo ba ko ta kareshe tare da rungumai Nadeen, tana murmushi,

Wani wawan ajiyar heart Asaad ya sauke tare da jin wata sanyi a ransa da irin tarban da mom tai wa rabin ran tasa,

Ko da yake ba laifin ki bane na sa ne since shine be kawo min ke ba, mu je ki zauna nan ta ja ta, son matsa mana ni kam, murmushi Asaad yayi yace wato mom tun kan ma ta shigo har kin fara nuna babanci koh, eh na ji bamu guri ba musu kuwa ga ya matsa suka shiga cikin parlour,

Durgusawa Nadeen tayi tare da gaishe da mom aa daughter tashi don Allah ki zauna, smile tayi tace aa mom nan ma yayi, aa nikam tashi dai ba komai ai ni nace ki zauna, saida ta gaida haj Zuwairah sannan ta dan zauna tana wasa da zoben ta kanta a kasa,

Ganin ta zauna ya sanya mom cewa to son a bamu guri ko, smile yayi yace mom in zauna mana, aa fita zaka yi itama ta fada tana smiling, kallon Nadeen yayi don mata sallama ya ko yi sa'a suka hada ido, so da ido ya mata alamun zan tafi, da sauri ta zaro eyes tare da mishi kallon pls don't go and leave me here shima maida mata yayi tare da murmuring relax every thing well be okey da haka ya sa kai zai fita har ya kai kofa ya ji mom na cewa Hibba tashi maza ki dauko wa Antyn ku ruwa da lemo,  murmushi yayi yace thanks mom Allah na gode ma da ya sanya mom ta karbi zabina da man na sani don bata ganta bane ya sanya take fadin haka amman yanzu i can see ta na kaunar Nadeen da haka ya sanya kai ya fita,

Mikewa Hibba tayi tare da rike kwankwaso ta iso gaban Nadeen hannu ta sanya tare da dago face inta, sai ta shege da daria,

Mom like damn serious wannan aban kike kira da Anty na haba wlhy kin cuce ni, daria mom ta sanya tare da tafa hannu tace ni fa na dau wata mace me amsa sunan ta zan gani inda aka dame mu da batun Maryam kullum amman sai na ga Aljanu,

Da sauri Nadeen ta dago tare da kallon mom cike da dinbim mamaki, uhmm haj Rukayya ke nan ke baki yi mamakin yanda aka yi son ke ta rawar kafa ba ashe gamo yayi da diyar Aljanu, haj Zuwairah tace,

Ke dan ubanki dago munafukar mumunan fuskan ki nan ki kalle ni, ni nice uwar Asaad kuma ban son ki ban kaunar ki kwata kwata baki mun ba ke in sanar da ke na tsane ki kuma nai wa dana mata don haka tun wuri ki fita harkan sa ko wallahi in ci ubanki ke Nadeen kike ko wa, kwata kwata baki yi daidai da yaro na ba, in ce don kudin sa kike son sa to zan baki adadin ko million nawa kike bukata, in zaki bar rayuwar dana mayya,

SAKI DAYA NEEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora