*NA TAFKA KUSKURE..*
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_*Intelligent Writer's Asso.*
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are
I so much luvs u my momma*😍_*Wannan littafin ba Sabon Novel bane Tsohon Novel dina ne na Dawo dashi,saboda zan sake gyarashi,na fadadashi domin masoyana wadanda basu karanta ba Dama wadanda suka karanta...Ina godiya sosai domin kuna nuna min One love💝kuna ma kan kunamin*_
*1 january 2019*
*Chapter 1*
⭐Da gudu wata mota 320 kirar toyota,ta shiga cikin wani private hospital mai suna *S&S SAFANA SPECIALIST HOSPITAL*
Cikin Hanzari matar tabude motar tafito tayi cikin asibitin da gudu tana fadin"ku taimakamin kada y'ata ta mutu ku taimaka min.." Nurses suka biyota aguje da gadon daukan marasa lafiya,wata matashiyar budurwa ce aka fito da ita daga cikin motan tareda wata dattijuwan mata,tsirtsetsen cikin keta wutsul wutsul alamar yana gab da Fitowa Ihu take zabgawa iya karfinta tareda wasu maganganu marasa ma'ana Da Hanzari suka gungurata sai labour room,Hajiya karima takalli Momma tace"To ai sai kira d'anki shafaffe da mai ya taho ya girbi abunda ya shuka" tafada dawani irin izgilanci,Momma tayi murmishi irin nata kan tace"Ayyah Hajiya zai zo ba"a gabanki namai waya ba kan mufito,insha yanxu zai zo kila wani abun ne ya tsaidashi"Tafada tana duban Hajiyar yamutsa fuska tayi zatayi magana kenan Kamshin turaren azzaro visit yafara musu maraba ko ba'a fada musu ba sunsan mamallakin kamshin.
Momma takara fadada fara'arta daidai lokacin da suka kariso maza biyu ne cikin shigar suit Black and ash,rigar likitancine saye acikin su,Daya daga cikinsu ya Karisa yana Fadin"Momma Har kun iso?
Cikin fara"a tace"mun iso Babana kashiga sun shiga da ita ciki"mtswssss tsakin daya katsesu kenan suka juya atare suna kallon Hajiya kari datake zabgamusu Harara,tace cikin kallon raini"Kaga mallam ba mgana zaka tsaya yi ba yata nakeson nasan Halin data ke cike,tundazu anshiga da ita bawani labari"Tsam dukkansu sukayi da rai kafin momma tayi karfin halin zame Hannunta tana Fadin"Babana Hanzarta kashiga ga Halin da *SAKINATU* take ciki.
cikin takaici da bakin ciki ya juyo wow!! abunda na Furta kenan dogon bufullatani mai cikar zati da kamala,yanada tsawon da dan kibam murjewa,dogon Hanci ya mallaka tareda madaidaitan dan bakinsa pick kamar yana shafa janbaki idanunsa,bakin gashin kansa yakwanta ye luf dashi,zagayayyen sajensa yakaramasa kwarjini Fari ne tas mai jaja din nan abun burgewa goshinsa dauke da tabon salla wanda yake kara masa kima a idon mutane,wani siririn gilashine mai karama Fuskarsa kyau sanye a idanunsa,kallo daya zakamai ka fahimci tsayayyan Namiji ne mai cikar zati da Haiba
*DR SAFWAN SALE SAFANA* kenan likitan daya kware gurin kula daduk abunda yashafi mata wato gynea Doctor wanda ke tare dashi *DR TAHIR* ne Abokine kuma Amini garesa kuma abokin aikinsa dasuke aiki akarkashin asibitin shi Dr safwan din.
Sai da ya isa kusa da ita yadan ramkwafa yace cikin dakakkiyar murya"Barka da zuwa Haji......."
"wai shi na tambayeka"ta katseshi "yata nake bukatar jin Halin datake ciki anshiga da ita tundazu naji shuru'"
takareshe fada tana wani jijjiga kamar wata yar daba,yadade tsugunne kafin yamike cikin sanyin jiki,ya Nufi kofar labour room din yasa Hannu a handle din kenan Wata murya cikin karaji da azaba yaji tana fadin
"Allah ya isa tsakani na dakai safwan,kayi min ciki kabarni da wahala,kacemin Haihuwa babu wuya...Gashi....Gashi kabarni da wahala kai babu abunda kasani sai ci🙈kamar tuwo wlh bazan sake yadda dakai ba" cikin bakin ciki da Nadama yasaki Hannun kofar ya juya ya Fara Tafiya duk suka bishi da kallo Hajiya kari tace cikin daga murya"Kai safwan ina zaka ko bakajin ihun da sakina takeyi ne....".Ina ko waiwayowa baiyiba saima kara sauri dayayi har yabace daga gurin.
Cikin Takaici Hajiya kari tadaga Hannu sama tana Fadin"wayyo ni karima nashga uku"kan ta isa kusa Da momma tana Fadin"ke wata irin uwace kinaganin wulakancin da d'anki yayi ma y'ata ammh kin gagara mai magana,saboda yagama cin moriyar ganga ya dirkamata ciki ko"?
Takareshe Fada Tana zaremata ido,Momma tayi mirimishi daya zaman mata jiki kam tayi magana Dr Tahir yarigata dacewa"Am....Hajiya kiyi Hakuri i promise u sakina Zata Haihu lafy"yana gama fadar haka ya bude Kofar Labour Room din ya Shiga.
Dakyar Dr safwan ya karisa office dinshi cikin kunan rai,toilet yafada yasakarma kansa shower ko kayan jikinsa bai cireba Haka ruwan keta kwararamai yafi minti talati ahaka so yake yarage radadin dake addabansa,Haka ya Fito ruwa na diga ta ko'ina ajikinsa kan kujrerar dake office din yafada yana maida Numfashi.
Har abada baisan yaushe zai zama mutum a idanun sakina da mahaifiyarta ba,baisan yaushe sakina da Mahaifiyarta zasu daina cimai mutumci ba shida mahaifiyarsa ba,baisan sai yaushene zata darajasa ta kallesa amtsayin miji ba bai sani ba,bai sani ba,yafada da karfi idanuwansa sun canza launi.
Yafi minti Hudu acikin wannan yanayin kafin ya sake Bude idanuwansa,gabadaya Zuciyarsa ta gama cika da wani kunci kansa na sarawa lokaci daya jijiyoyin kansa suka Dago,kansa ya Dafe lokaci daya yana Share Ruwan Dake Diga daga saman kansa,kafin ya sake komawa ya jingina da jikin kujeran yana maida Numfashi a jere kamar wanda yayi gudun tsere.
Runte idanunsa yayi yana ajiyar zuciya Lokaci daya yana Saukar Da Numfashi Daga ganin yadda yake yi zaka fahimci yanayin Dayake ciki na bacin rai da dacin Zuciya,idanuwansa ya bude yana bin Kofar shigowa da kallo lokaci Daya Abubuwan da suka Faru abaya suka fara dawowamai daki daki kamar alokacin Abun ke Faruwa tamkar yana kallo cikin magijin talabijin.
Commets,share,like and vote....
*Anitha..*

YOU ARE READING
NA TAFKA KUSKURE..!
ActionSafwan wai me ka maida ni ne...? na haihu kuma na koma ina maka Renon D"a...? baka isa ba wlh......