*NA TAFKA KUSKURE..!*
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞*DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
*34*
"Kunya tareda Nauyi sun hana Sakeena zuwa tabawa Safwan hakuri duk da Hajiya kari ta Matsamata taje tagwada sa'arta azahirin gaskiya dukkansu sunyi nadama kuma suna ta tuba ga Allah hajiya karima tanemi gafaran yan"uwanta kuma sun yafemata ammh sunce basu da hurumin dazasu roki Kwamishina yamaidata dakinta sai dai ta cigaba da addu'a Allah yasa tsakaninsu akwai Sauran Zama
wuni yana shudewa kwana yana shudewa ahaka har watanni suka shude awannan lokaci Safeena cikinta nada wata takwas aduniya tayi kiba cikin kuma yayi girma sosai kamar dan wata tara gashi tana karatunta cikin nasara da jin dadi tareda taimakon mijinta kuma gwarzonta Dr Safwan Sale Safana wanda duk abunda bata gane ba inta koma gida yana kara koyamata,Shi da kantshi yakemata awo ammh shikanshi girman cikinta na bashi tsoro duk da yamata scan kuma yaga komai lpy.
Su hajiya mama da momma kuwa rayuwa sabuwa domin yanzu basu dawani mtsala sukam damar Sakinace damuwarsu kuma yanzu batanan shiyasa yanzu bakajin Hajiya mama na kwakwazonta na fama sai dai in yan abun sun motsa kunsan mai hali bayasa Halinsa.
KANKIA
awannan watannin in ku ka ga yadda su Sakina suka koma sai kun zubar musu da kwallah saboda yadda suka rame suka kammajame sakina fuska tayi baki ta kuma cika da kuraje ga kan nan yayi duku duku kamar na mahaukaciya kumbuna sun yi baki sunyi datti hajiya kari kuwa kamar tsohuwa takoma saboda wahala.
Yau tunsafe Sakina taje layin bowol ammh sai wurin takwas tasamu zuba ruwanta tadauko daya akanta daya yana hannunta tana tafiya zata gida taji ana mata hon abaya kaucewa tayi domim bata zata da ita ake ba sai da motar tazo daf da ita kana ta tsaya cikin mamaki take bin jeep din da kallo kafin taga anbude murfin mota anfito wazata gani...Daddy ta furta cikin mamaki ya amsa da "Na'am sakina kece kika koma haka "yafada idaninsa sunkawo ruwa zatayi mgana kenan wata farar mata ta bude mota ta fito sanye cikin leshi da mayafinta bawata babba bace bata wuce sa'ar Anty salma ba.
Ta nufe sakina cikin tsausayawa tana fadin"Innalillahi...Sweety badai dota Sakina bace wannan..?"Kwamishina yagyda mata ta yi saurin saukemata ruwan ta rumgumeta tana fadin"Baka kyauta ba Sweet hrt kowa yana kuskure ko Allah muna masa laifi yayafemana ko"baicemata komai ba sai ma cema direba yayi su karisa.
Sakina sai kallan matan take datake rike da hannunta har cikin gida ai sakina sai ta shiga kwalama Hajiya kari kira tana fitowa Daidai kwamishina yana shigowa ai sai tayi cak tana kallonsa shima ita yake kallo yana nuna ta da mamaki hawaye ya zuraroma Hajiya kari sai ta koma daki da gudu tana kuka...dakin matan tabita tana rike da sakina.
Hajiya kari dake durkushe tana kuka tadafa tadago tana kallonta murmishi ta sakarmata kafin tace"Don Allah kibar kukan nan hakanan ko Allah muna masa laifi yayafema na balle mu mutane"Hajiya kari tace cikin kuka wacece ke!...MATATA CE....dana aura bayan Rabuwarmu...atare sakina da hajiya kari suka kara kallonta itakuma tana musu mirmishi.Dady Yafadi haka bayan ya sawo kanshi dakin yakarasa shigowa yana fadin"Bayan na koreku kwana biyu kawai na kara nabar kasar sai da nayi wata uku baninan karkuyi mamaki duk halin dakuke ciki inada lbr...Dagacham saudayi na wuce achan na hadu da Mariyatul kibdiyya wacce asalinta yar gombe ce tayi aure mijinta ya rasu ammh bata taba haihuwa ba mahaifinta shine wazirin masarautar gombe munyi aure wata hudu da suka wuce daman nafadamata yayana hudu shine da bata ganki ba ta tambayeni nikuma na fadamata komai wlh tallahi tunda na fadamata ta kasa sukuni akan lalle Saina yafemuku kuma saina zo mun dauko ku.....mu koma gida.
Sakina tafada cikin rawan murya"mu Dady...Kayafemana mu koma gida harda Hajiya"Dady yace"kwarai ma Sakina tare zamu koma domin tun jiya da asuba na sanya aka maida aurenmu....Da mahaifiyarku nasan ko ahaka na barku kun fahimci rayuwar danike gayamuku"Sakina ta guce da kuka kan zube gaban daddy tana kara basa hakuri dagota yayi ya sharemata hawaye yace"ba'a san raina na muku haka ba wlh sai dan ku gyaru kuma ku gane yadda Rayuwa tasa gaba,sakina tace"Ba komai daddy hakika kaci ka uba nagari...Wlh ko ahaka nagane daddy nagane mutum ba komai bane.
gurin Mariya taje ta durkusa tana fadin"mungode Anty hakika bamu da bakin gode miki Allah ya saka miki Aljannah"kamota tayi ta rumgumeta tana fadin",babu komai yata...Karki damu inaji kamar nina haifeki Sakina.Mirmishi sukama juna lokaci daya kan taja hannunta suka fice.
Hajiya kari takasa dagowa ta kalli kwamishina saboda kunya shine yayi gyaran murya yace"Basai kin ce komai ba karima Allah yayafemana gabadaya.."Tadago idanunta jawur tace"Ban chanchanci yafiyarka ba kabiru wlh ban chanchanci yafiyarka ba sam"takareshe fada da kuka takawa yayi ya isa gareta yadagota yana sharemata hawaye yace"ko alama karima duk nasan kin min abubuwa masu yawa ammh tunda kingane kuranki wlh har ga raina na yafemiki kuma nasa anmaida auranmu..da zuciya daya sai dai bansani ba ko zaki iya zama da kishiya"da sauri Hajiya kari tace"wane ni daja da abunda Allah ya halarta...Ai samun abokiyar zama irin mariya sai an tona...Ngd sosai Allah yakara girma.Mirmishi ya sakarmata yana kara gogemata hawaye.
nan suka wuni har su yayyen hajiyan suka dawo sukayi mgana da kwamishina yasaukemusu kayan abincin dayazo dashi sukuwa su sakina yace kada su dau komai aikuwa murna gurinsu ba'a mgana dazasu tafi suka roki gafarar kowa suma mutan gidan suna neman tasu ankara musu fada kan sundai ga rayuwa inzasu natsu yarage nasu,gidansu kwamishina suka biya suma chan din albarka sukaita sanyawa musu har suka tafi.
Amota mariya babu ruwanta sai jan Hajiya take da hira ita da Sakina su kuwa sunkasa sakin jikinsu da ita itakuwa ko ajinkinta sai jansu take ajiki.
Suna komawa takai Sakina har daki ta hadamata ruwan wanka tadauko mata wata doguwar riga ta ijiyemata hakama tama Hajiya kari wacce kunya ya hanata mgana bayan shiganta wankane hawaye ya zuraromata wai yau itada take iko da gidanta sai gashi yau watace ke iko dashi...Ba shakkah duk wanda bai godema Allah da Ni'imar sa ba zai godema wuyarsa.
Ita tai ta dawainiya dasu suna godemata kayanta ta daukoma hajiya kari kafin gobe aje asiyama su nasu kayan.
Allahu akbar Sakina da Hajiya dasuka sa hakarkarunsiu akan katifa suka furta domin ko amafarki basu taba tsammanin zasu dawo rayuwarsu ta baya ba..Koda gari ya waye hakanne yafaru a dining suka ci abinci tun basu sakin jikinsu har dai suka fara sakewa da ita.
Kwanan su biyu dawowa komai yafara zama normal tuni an musi sabbi dinkuna abunsu hajiya kari tazama wata so cool da ita kamar ba itaba itakuwa Sakina Anty na iya bakin kokarinta na ganin ta saki jinkinta,washegari sai ga Laila tazo gidan tana ba su Sakina hakuri na rashin zuwanta kankia Sakina ta mata dariya kawai tace"Anty laila kenam bbu komai Rayuwar kenan...Sai kuma naji ance ya mujaheed yayi aure"tace"eh...Wlh wata biyu dasuka wuce"Sakina tace"to meyasa kika yarda"tazaro ido tace"so kike in tada hankali nima ya sake ni ko"Sakina ta kalleta hawaye ya ciko idanunta tace"oh..Ammh ni kikace in tada hankalina ashe kinsan Safwan zai iya sakina in namai abunda kikace kenan ko"Shuru Laila ta mata mikewa Sakina tayi tace"basai kinyi mgana ba nagane komai domin ni yanzu ashafin rayuwa ba abunda bangani ba"da sauri Laila tasha gabanta tana fadin"kiyi hakuri yar'uwata nima nasan sam ban kyautaba amtsayina na yayarki....Ki yafemin don Allah"Kallonta sakina tayi kan tace'shikenan bbu komai...Harda haihuwar dakikasa na dakatar duk na yafemiki duk da ke kinata haihuwa kamar naga ga wani karuwar nan mun samu"tana gama fadar haka ta fice tana sharan kwallah,hajiya kari dake gefe tace'Mumaka sa sakina ta tafka kuskure mune sila wlh"Anty laila tace"Allah ya yafemana....Ammh tadade tana saka mganar sakina tasan mgana ta saka mata.
Asatin Anty salma tazo ita da Ummi daman tana hannunta tuni tayi murna matuka kuma ta kara musu fada sosai lalle ta yarda duniya tahora hajiya koda yarda tayi sanyi Anty mariya tana ta fadin"Yaya kaza,yaya kaza...Hajiya na amsawa da kulawa...Zamansu gwanin sha'awa kamar ba kishiyoyi ba,Anty kwananta biyu takoma ammh kafin takoma sai da tace ta shirya taje har gida ta ba Dr hakuri ko ya maidata dakinta tabbas tayi na'am da shawararta shiyasa washegari nayi ta shirya cikin dogon hijabinta har kasa Anty mariya ta aramata motarta tamusu sallama ta fice suna mata fatan sa'a.
Cikin sanyi jiki ta dumfari gidansu Safwan lokacin da Habu mai gadi ya budemata get bai ganeta ba sai da ta paka motar ta fito tana gaisheshi take tambayansa ko Safwan yana gida,ya amsa mata da "eh...Yana nan hajiya mirmishi ta mai kawai tace"Sakina sunana ba hajiya ba"Ai sake baki yayi yana kallonta kan yace"Au...Sak...Oh hajiya barka da zuwa"wucewa kawai tayi ta barsa sake da baki har yana kara lekata.
Shashen su momma ta nufa ta shiga da sallamarta wanda Hajiya mama ke zaune afalon ta amsa tana fadin"Maraba shigo......
Commet
And
Share.
Vote*Shakira..*

YOU ARE READING
NA TAFKA KUSKURE..!
ActionSafwan wai me ka maida ni ne...? na haihu kuma na koma ina maka Renon D"a...? baka isa ba wlh......