Chapter 35

373 33 2
                                    

*NA TAFKA KUSKURE...!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*Dedicated to my momma Hajja khadija muhammd Ba'are*


*35*

  "Karisawa tayi cikin falo tasamu gefen hajiya ta zauna kallonta hajiya mama keyi ranta na bata kamar sakina ammh kuma tana karyatawa Sakina tadago ta kalli hajiya kan tace"Hajiya baki ganeni bako..?

.Hajiya mama tace"eh...Kiyi hakuri ban sheda ki ba yan"nan"Mirmishin takaichi Sakina tayi kan tace idanunta na tara kwallah"Sakina ce fa Hajiya"Ai da Hanzari tamike tana salati da karfi ta furta"Sakina...Nashiga uku ni Maryamu Sakina ciwo kikayi naga kin lalace haka"Fashewa da kuka tayi tana Fadin"wlh hajiya nagani kuma nagane koda kika samin tsama sona kike...Don girman Allah Hajiya ki yafemin'Hajiya ta karisa kusa da sakina tadagota tana fadin"Mekika min Sakina wlh bakimin komai ba duk abunda kikaga ina miki don ki gyaru ne...Allah yayafemana gabadaya"Rumgumeta Sakina tayi tana godiya cikin kuka momma dake tsaye tundazu ta kariso tana cewa"Tabbas baki mana komai Sakina har yanzu kallon ya'muke miki"Sakin Hajiya tayi kan ta isa gaban momma ta durkusa tana fadin"Momma...Ban chanchanta kiyi afuwa agareni ba ammh gani durkushe agabanki kiyi duba ga Allah ki gafartamin wlh na tuba nabi Allah baran kara ba nagane kune masoyana na gaskiya"Momma tadagota tana sharemata hawaye tace"Har Abada ban chanzaki ba sakina ki na nan amatsayin yata ta har abada...Karki damu daman baki man komai Allah yayafemana gabadayanmu"Rumgume momma tayi tana Fadin"Nagode momma Allah yakara girma.

Kan kujera suka karisa nan Sakina tabasu lbrinta tun bayan sakin da Safwan ya mata Hajiya mama tace"Allah sarki kabiru hakika ya jarabtu sai dai mu fatan Allah ya kara shiryar damu"Suka amsa Da Amin.

Adil ne ya shigo da gudu yadane cinyar hajiya mama yana Fadin"Hajiyata...Turesa tayi tana fadin"A'a Alhajine...Kai wai bana ce ka kiyayeni ba"Tura baki yayi yatashi ya isa ga momma ya haye cinyarta yace"Bani chonki...Momma nake cho"Yafada yana rumgumeta Hajiya mama tace"To sai me...Aikin banza chan da tsiyarka ni nan har akwai soyayyar data kai na marigayi Habule na nane wallahi bata"Tafada harda jaddadawa.

Sakina dake gefe tana kallonsu ta share hawaye tana kallon Adil dayakara girma da wayo ga yayi kiba abunshi alamun yana Samun kwanciyar Hankali abun takaichi wao ace danta na cikinta ma baisanta saboda wani sakarci nata...Hannu tasa ta share hawayen daya zubomata kada su hajiya su gani ammh ina sun riga sun ganta.

Sallamar Safwan shi ya dakatar da dramar dake tsakanin Hajiya da Adil Tafe yake shida Safeena dake sanye da doguwar riga baka ta sanya mayafi ya rufema cikin jikinta wanda yakusa rinjayarta saboda girmasa kanta na gefen kafadarshi shima ya zagayo hannnsa ta kugunta yana Sanye cikin bakar jallabiya tunda suka shigo Sakina tayi galala tana binsu da kallo ganin yadda suka chanza cikin lokaci kankani Dr Safwan yayi kiba ya murje yakara haske itama Safeenar,tunda suka shigo momma da Hajiya suka mike suna ma Safeena Sannu shiya taimaka mata ta zauna akasa yana mata Sannu Safwan yace"Momma...Wlh zan dawo muku da Adil damun yanmatana yake d kiriniya wai harda goyasa yakecewa ayi fa"Hajiya mama ta dunguremasa kai tace"kaga min mugu...Don ubanka da uban cikin da ubanka yamata zataji kokuwa da goyaka"😂kunya takama Safeena da momma shiko Safwan ko ajikinsa Tabe baki yayi zai fashe dakuka tace"Kaji gidanku wlh kanamin kuka zaneka zanyi ja'iri kawai"Kuka yasa yatafi da gudu gun momma yarumgumeta Safeena tace'Amana hakuri Hajiya kin manta yace zai Siya miki jirgi"Hajiya tace"Bani so Raggo kawai'dagowa yayi hawaye shabe shabe yace"Ba chan chiyanmiki jigi ba Daddy da mami na jan chiyama wa...Kuma baja ki hau ba"Yafada harda murguda mata baki dariya sukasa mishi gabadaya.

Safwan yadago yana dariya kawai caraf idanunsa suka sauka kan Sakina dake zaune gefe tana ZUBAR KWALLAH...Aziza idiris gombe...Bana gajiya da Novel dinnan walle....Kuramata ido yayi cikin mamaki da firgici kamar fa Sakina yake gani ganin inda yake kallo yasa suka bi gun da kallo Safeena takurama Sakina ido tana kallonta Aranta tana so tace Anty ammh wata zuciyar tana cewa ba ita bace"Sakina tayi saurin mikewa tana fadin"Momma..Zan tafi dama nazo gaishekune"Tafada tanayi hanyar waje...SAKINA..Dr Safwan ya furta da mamaki cak ta tsaya ranta na mata kuna Hajiya mama tace"kwarai...Tun dazu tazo neman gafararmu"Kai tsaye yace"kuma kuka yafemata"Juyowa tayi cikin kuka tace"Daman nasan ban chanchanci yafiyarku ba...Safwan"Tafada kuka yaci karfinta baya ya juyamata kawai ransa namasa kuna rarrafawa tayi ta isa zuwa gabansa tana fadin'Na san ban chanchanta ka kalleni ba Safwan ammh kadubi darajar Allah kadubeni da idon Rahama kayafemi ko naga daidai Rayuwata"shuru yamata Safeena ta mike dakyar ta isa kusa da Sakina ta durkusa tarike hannunta dagowa tayi tana kallonta ita kuma ta mata mirmishi kallonsa tayi tace"UNcle....Saurin jiyowa yayi yana kallonta kan yayi saurin cewa"Ke kina da hankali kuwa bakiga halin dakike ciki ba...Tashi tashi.."Kin tashi tayi saima cewa datayi'Kazama mai yafiya unku...Kaima sai Allah yadubeka da idon Rahama...Anty tayi kuskure kuma tagane kuskurenta Don Allah kabata dama baxata sake ba"Shuru yayi kan yace"ki tashi nace itama kallon idanunsa tayi tace"Bazan tashiba sai ka furta ka yafemata"kallonta shima yakeyi kan yayi ajiyar zuciya yace'Taji albarkacinki....na yafemata Allah ya yafemana gabadaya"Alhamdulillah...Haka cikakken musulmi yake"Hajiya mama ta furta.

Sakina tasa hannu tadago Safeena ta rike hannunta tana fadin"Bansan mezan cemiki ba Safeena...Ban sani ba'Tafada idanunta na kawo ruwa"Safeena ta damke hannunta tace"Basai kin ce komai ba Antyna wlh kin wuce haka agurina ammh alfarma nake nema agunki"Sakina tace"Ki fadi komiye safeena indai baifi karfina ba zan miki shi Safeena"kai tsaye Tafada tana kallon Dr Safwan"Ki dawo kizo mu zauna mu reni ya'yanmu tare kuma mu rumgumi mijinmu...Mu zauna har Abada"Kallon kallon aka hau tsakanin Dr Safwan da Sakina saurin sadda kai yayi yace"A'a.....Safeena tayi gaskiya ka maidata dakinta ku taru ku rufama juna asiri...Ku zauna lafiya da juna"Hajiya mama tace"shikenan kuwa...Allah yayi miki albarka Safeena Allah ya rabaki da cikin jikin ki lpy"gabadayansu suka amsa Da Amin.

Rumgumeta Sakina tayi tana kuka tana mata godiya safeena tadagota tana sharemata hawaye tace"Kidaina godemin Anty kin wuce komai agurina"Itama sai hawaye sharr Adil ne yaga suna hawaye duka biyun zuwa yayi ya rike ma Safeena hannu yana Fadin"Mami...wacece wannan.."yafada yana Nuna Sakina shafa kansa tayi kan tace"UMMINKANE...Itace mahaifiyarka"Kallonta yayi yace yana kallon Sakina"UMMI.....Yafada still yana kallonta sakina ta rumgumesa tana hawaye tace"Ni Umminkane ta haihu Ammh Mami mahaifiyarkace ta har abada"Tafada tana shafa kansa abun mamaki shima rumgumeta yayi yana sharemata hawaye.

_Allah sarki Uwa Uwa ce komai lalacewarta_


Komai ya daidaita cikin lokaci kankani Sakina nan ta wuni tana dawainiya da Safeena da Adil ita tataya momma Aikin girkin dare sai da suka kammallah kunsan Raba dare sukai suna hira kafin safeena ta barota cikin dakinta takoma gun Dr Sakina tayi kuka awannan daren na ganinta kwance kan gadon tabata tsinana komai ba sai lalacewa...Raba dare tayi da ibada da asuban fari tatashi kokan Su Safena su fito Sakina ta tsaftace gida ta hada musu break kwai ta soya musiu da ruwan tea suna karyawa DR yayi harama  abun mamaki har Adil na zarin shi zai bita lallabasa sukai suka shiga mota suka kaisa mkranta kana suka biya suka ijiye Safeena asch tana da test tai musu fatan dawowa lpy,suka kama hanya shida Sakina direba yana binsu abaya da motar data zo dashi,Shizai kaita saboda mganar Maida aurensu.

Hakika kwamishina  yayi murnan dawowar Safwan amtsayin sirikinsa a kashi na biyu...Hajiya kari saboda godiya harda kuka tarokesa gafara kuma tace ya rokan mata su Momma kan tazo...Anta dawainiya dashi an fahimci juna sosai cikin mutumci da girmama juna sai la'asar yayi shirin tafiya rako sa tayi gun motarsa kallonta yakeyi bako kiftawa Kauda ido tayi kan tace"Wannan...Kallon fa"mirmishi yayi yana Shiga mota yace"Mamaki nake wai Ke Sakina kabir kankia ce kika zama ustaziya"Dariya tace"Ka adana mamakinka sai Auren ya maidu tukunnah..."Tafada tana rufemasa murfin mota kallonta yayi yace"Sure....Gyada kanta tayi kawai dagamasa hannu tayi har yafice daga gidan.












commet
And
Share
Vote.

*Anitha...*

NA TAFKA KUSKURE..!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora