END

505 31 1
                                    

*NA TAFKA KUSKURE..*!

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*DEDICATED TO:My mommah Hajja Hadiza muhammed Ba"are*

_*Godiya gareku Masoyana wanda na sani da wanda bansani ba...Bahoot Bahoot Shukuriyyah*_

*END*

Bayan Tafiyarsu da wata biyu Safeena tayi rashin lpy Tahir yace yadubamasa ita illai ana dubata sai ga ciki har na tsawon two month murna gun Dr baida iyaka...To ahaka dai Rayuwar taita gungurawa cikin kwanciyar Hankali Safeena cikinta nakai wata biyar ta ciresu anono tacigaba da kula da kanta ga sch suna shekarar karshene.

Watansu Shida kuwa kana suka nufi gida koda suka zo sun tarar da Safeena da tulelen cikinta agaba yan biyu sun kara girma da wayau Abunsu sati biyu kawai Dr yayi yakoma yaso Tafiya da Safeena ammh Hajiya mama tace"Kaniyarka da cikin zata bika wata uwa duniya tama uban mene nifa bansa zalama in bazaka iya zama kai daya ba to kakoma da Sakinar"Ransa yabaci domin shi da Safeenar yaso komawa tunda kuma akace haka shine yayi komawarsa shikadai.

Sai Da Safeena tahaihu kana yadawo tasamu dan ta Namiji Ranar suna na zagayowa yasa ma yaron sunan kwamishina wato kabir...Hakika kwamishina yaji dadi matuka domin har hakan yakasa boyuwa aransa sai dayazo ya furta da baki da kuma aljihu to baisamu komawa sai da Safeena tayi arba"in dama kuma gashi sun sami hutu kawai sai ya tattarata suka Tafi akabar Sakina da yara.

Safwan da Safeena a Portugal sabuwar rayuwa suka bude ita dashi domin sun dade rabonsu da juna azahirin gaskiya yafi samun Natsuwa in yana tareda safeena sakina kawai arakane ammh shi Namiji ne dayakeson kwatantan Adalci shiyasa ko afuska ba wacce yataba Nunama sai dai a aikace in yana Tareda Safeena kullum cikin desire yake sakamakon Sakina wacce shi ko Sha'awar kasancewa da ita bayayi kawai yana daurewane don kar ta gane ammh sai da tagane to yazatayi tarigaya tasani yanzu qualityta da sauran mata ba daya kawai dai ana rakawa da ita ne.

Suna da wata biyar da tafiya suna ma shirin dawowane aka yomasu waya suzo hajiya mama ba lpy...Cikin tashin hankali yanemanmusu visa ammh bata samu ba sai a washegari da yammh suka taso cikin ikon Allah koda suka iso sun tadda gida cike tun a airport yake tama Tahir tambayan ya jikin hajiyar ammh amsa dayane"Hajiya ciwo yakare"Dagashi har Safeenar jikinsu yayi sanyi.

Da kwamushina yafara cin karo wanda yaxo da tawagarsa ga kuma yan safana yagani dasu kawu bala ana alwala ai jakar hannunsa ya saki yanajin wani jiri na kwasarsa Tahir neya rikesa kwamishina yadafasa yana Fadin"Sai hakuri wanda yafi sonta ya dauketa...Sai muyi fatan Allah yasa tana kyakyawan matsayi"Wasu hawayene masu zafi suka zubomasa safeena kuwa da gudu ta shiga gidan da Sakina tafara cin karo wacce ke gefe sanye da hijabi tana rumgume dasu little hajiya tana zubar kwallah sai momma dake kurya kanta aduke tana digan hawaye Adil ne yazo ya rumguneta yana Fadin"Mami...Hajiya ta tafi naga ansata awani abu"Sulalewa safeena tayi tana kuka iyami dake gefe takalleta itama kukan take tace"Yanzu kuke Tafi ina megidanki Hajiya ta rasu ammh abakinta har ta mutu tana sanya muku albarka"Tana fadar haka kawai dakin aka kara kecewa da kuka domin kan kowa yasan Hajiya ta mutane ce macece mai dattako da sanin yakamata macece wacce indai kazauna da ita wlh sai ka karu.....ALLAHU AKBAR KULLI NAFSIN ZA'IKATUL MAUT.

Dama koda suka iso an hadata badadewa aka isa da hajiya makwancinta na dindin wanda safwan ya durkushe gaban kabarin yana fitar da kwallah Tahir yakamasa suka shiga mota suka koma gida ko mgana bai iya ko gaisuwa aka mai saidai ya jinjina kai cikin gida suka yana yin sallama afalon da suke kuka yakara kecewa kai tsaye momma ya nufa yana zuwa gabanta ya durkusa yace cikin shakakiyar murya"Momma ya mukaji da hakuri..?

"Momma tadago idanunta jawur tace cikin kuka"Hakuri namune gabadaya Safwan Hajiya tatafi ta barmu tabarmu da kewa"Tafada tana fashewa da kuka Safwan ya runtse ido hawaye suka xubomai yace cikin muryan tsausayi"Momma mun sake yin rashi akaro na biyu...Mun rasa jigonmu hakika kekika haifeni ammh dukkan wahalata Hajiya tayisa ta kasance jigoce agareni wacce tazame min makwafin mahaifi wlh tallahi hajiya ce komai na itace ginshikina momma rawar data taka arayuwarmu mai yawa sai dai Muyi mata Fatan ubangiji ya amshi bakuntarta"Yafada yana zama dirshan ya tusa kansa atsakanin kafafunshi yana kuka gabadaya dakin jikin kowa yei sanyi kuka kawai akeyi Tahir dake tsaye shima sharar kwallah yake iyami ne tataso tazo tadagosa tana fadin'Kadaina kuka Safwan yanzu hajiya tafi bukatar addu'an mu akan kukanmu...Ta tafi ga ubangijinta ammh wlh tatafi dakai abakinta tana sa maka albarka da fatan gamawa da duniya lpy sannan ta horeka da kakwatanta adalci atsakanin matanka"Safwan ye wuf ya mike yana tangadi yafice kuka keneman kwacemasa safeena da Sakina suka bi mijinsu da kallon tsausayi domin wannan mutuwar shi aka mawa.

Has llegado al final de las partes publicadas.

⏰ Última actualización: Oct 14, 2020 ⏰

¡Añade esta historia a tu biblioteca para recibir notificaciones sobre nuevas partes!

NA TAFKA KUSKURE..!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora