*NA TAFKA KUSKURE..*!
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
*30**
"Mtsala ta farko da sakina tafara fuskanta shine na danta ADIL....wanda indai yana wasa afalo tashigo yanzu zai yanka ihu yatashi da gudu yabi safeena daki ko kichen inko tace zata daukeshi yadinga yanka ihu kenan kamar yaga dodo sai Safeena tazo ta daukeshi tana rarashi yana kuka yana fadin"Mami....Yana nuna sakina,sai Safeena tasabashi su koma daki kana zaiyi shuru.
Abun yana damun Sakina matuka domin koda take rashin kula Adil bawai batason shibane yaza'ayi mutum yahaifi da da cikinsa yace bayason shi wannan ma ai karyane,tana son danta kawai abubuwane suka mata yawa ciwon abu biyu tahade mata ga na kwatar miji gana d'a domin yanzu Safwan tsakanin shi da Sakina ido ko kula da yadda take rayuwarta bayayi saboda shi yanzu kwanciyar hankalinsa kwanciyar hankali Safeena da gudun jininsa.Hatta da su momma sai suyi sati basu sata a ido ba Hajiya mama ko aranar data shigo shashen ta iske Sakina zaune afalo dariya tahau tsintsurawa tana fadin agaida uwargida sarautar mata shiyasa bahaushe yace kada kayi wasa da damarka domin watarana matsayin daka ke adama rasashi kakeyi,babu shakka tasan da ita takeyi shiyaasa sum sum ta shige daki ranta na mata suya tana son tadawo Sakinarta tada ammh tarasa yazatayi.
Yau Tun safe Dr Safwan ya fice bayan yar rigiman sa Safeena tagama kukan Ita Umminta takeson gani tun yana lallashinta har yazo yana binta da ido domin kowani dakika kaunarta kara zurfi take aranshi,bawai bayason tafiyar nata bane A'a yadda Safeena tazama tallafinsu shida danshi yakeji kada suyi maraici,tana fushin yafice ya barta.
Sau wurin sha biyu tafito daga daknta Adil na biye da ita kamar jela yana mata gwarancinshi sanye take da wata atamfa milk and green riga da sikat kayan sun amsheta tayi daurin ture kaga tsiya ta daure gashinrta da band,tarasa mai zata dafa kawai sai ta soya musu doya tayi miyar kwai ta kammallah kenan taji ana sallama da sauri ta fito tana amsawa.
Wasu mata tagani guda biyu dayar tafi manyanta dayar kuma yarinyace dukkansu kallon banza suke binta dashi kamar sunga kashi Safeena taji gwiwarta ta sake tace cikin sanyi murya"Sannunku da zuwa...Ku....ke dallah rufema mutane baki"Anty laila kenan ta katseta tana binta dawani matsiyacin kallo Hajiya kari tace'yo kekuwa dole tamana sanabe mana anzo gidan daula anrabu da cin gabza"safeena taji wani abu ya tsayama amakogwaro kafin tace wani abu Adil ya fito daga daki dagudu da wayarta yana fadin"Mami....Mami...Abbu...Yana mikamata wayar alamar ana kira Amsa tayi tana shafa kanshi Dr ne ke kira shiyasa ta barshi.
Hajiya kari da laila suka hada ido suka futar lokaci daya"MAMI....."da mamaki afuskarsu kafin Laila tace"Hajiya kamar fa Adil ne fa yagirma hajiya kari tace"Shine Nima nayi mamakin girmansa rabona fa dashi tun haihuwarsa"Laila tace"Nima inaganin tun lokaci ammh naji yana cema watanan mami fa"Tafada tana kallon Safeena datake rumgume da Adil dake binsu da kallon rashin sani.
Hajiya kari tace'Ato sakarcin sakina ne baki sani ba"Tafada rai bace ai laila da hanzari ta ficikosa tana fadin"Bazai yuyuba kin asirce uba kuma ki asirce d"a ba.."Yako tsandara ihu iya karfinsa hajiya kari ta dunguremasa kai tace"Kinganin mun munafukin yaro kaci gidanku ni nan daka ganni kakankace ita kuma wannan yayar uwarka"Tafada tana nuna laila kana ta nuna Safeena dake daskare awurin hawaye sun taru a idanunta tace"Ita kuma wannan kishiyar uwarkace ga uwarka chan wacce tayi nakudarta"tafada tana figan hannunshi ta wuce dakin Sakina dashi laila ta marata baya shikuwa Adil kuka yake yana mika hannu yana ta kiran"Mami.....Mami...ita kuwa hajiya kari nakara jansa tana fadin"Ko zaka mutu sai kabar mamin don ubanka".
Safeena da kuka yakwacema tashige daki da sauri tana maida kuka gefen gado tazauna tana sharen hawaye aranta tana addu"an kada Allah yabasu ikon Rabata da Adil domin wlh bazata iya rayuwar gidannan ba yaron nan akusa da ita ba.
Sakina na kwance akan gado su laila suka shigo cikin mamaki ta mike tana kallonsu rike da adil dake ta kuka harda hawaye,cikin mamaki su hajiya ke kallon sakina tareda bin dakin da kallo laila tace"Sakina....Haka kika maida kanki ashe..?"Sakina ta tabe baki kafin tadiro daga kan gado sanye da breziya da under bako kaya tace"Eh....Haka Safwan ya maidani Anty"Tafada tana fashewa da kuka rumgumarta Anty laila tayi tana lallashinta hajiya kari ta damkafar da adil akasa tana fadin"Kama ma mutane baki wlh ko in mauje ka munafinki yaro"Sakina ta saki laila tana fadin"Hajiya kuma kungani ko wlh yaron nan in yaganni kamar yaga dodo"Tafada hawaye yana zubo mata hajiya kari tace"badole yamaidake dodo ba tunda kin zauna kin maida kanki sakarya mara wayo har ita waccan sillan kara wata abace dazaki zauna su ruguza miki rayuwa'Sakina ta tsananta kukanta tana fadin"Ya zanyi hajiya ya zanyi wlh narasa ma ni mai zanyi"Anty laila ta riko hannunta zuwa gefen gadon tazaunar da ita tana fadin"shine dalilin dakika bar kasuwancinki ya ruguje ayanzu haka shagonki na kano an rufesa coz bbu kaya why sakina zaki sakaci da rayuwarki ta tarwatse lokaci daya"Sakina ta share hawayenta tace"Ni bata shago nake ba ta yadda na zama bola agidan nan shi yafi damuna ku fadamun yazanyi"tafada hawaye na kwaranyomata Hajiya kari tace"Abunda zaki ki mike ga kanki kidawo sakinarki danki kuma da ake miki iko dashi ki karbi abunki domin ba uwar wani ya haifar miki ba wlh sakina in har baki mike kin kwaci yancinki agidan nan ba to na yarda ke ba nonon karimatu kika sha ba"Takareshe fada da bacin rai Sakina tace cikin kuka'zanyi hajiya zan nuna miki nidin yar karimace ta halas ma kuwa"Hajiya kari tace"ke kefa kici mutumci duk wanda yanemi yadakatar dake koda uwarsa cw"Laila tace"Ai sune munafukai baran wannan katafiriyar tsohuwar mai kalan yan duniya"Sakina tace"Ai itace ke juya safwan din inaji ko auren nan ita tayimai shi"Laila tace"Yar tasha ita lokacinta ubanwa yasa amata kishiya"Hajiya kari tace'ai karta aragama kowa harda ita tahada taci uban shegiya kota koma kauye inda aka fito tana wani ji da baki kamar fanteka🤣🤣gabadayansu dariya sukasa harda tafawa.
Koda suka waiga ba Adil ba dalinlinsa ashe suna chan suna mgana ya sulale yakoma gun Safeena wacce taci kuka ta koshi yana ko shigowa yatafi ya rumgumeta yana ajiyar zuciya alamar yasha kuka rumgumesa tayi tana dariyar farinciki.
gabda la'asar sukayi shirin tafiya bayan sun cika sakina da mugayan shawaransu wanda bazai bulle da ita ba saima karin jawoma kanta wata fitinar...kwamishina bayanan yaraka gwanna jigawa shiyasa sukasamu zuwa domin ido yasanya musu ko laila yace tadaina zuwa sai anyi wani abu kwakkwara tukun..
Sakina ta rakosu kenan suka ga hajiya mama zaune adan barandansu ta shimfida tabarma tana jin radio ta sai gasu sun fito sun yi tsam da suka ga hajiya mama ammh sai suka waske itakuwa hajiya mama harda cemusu bata gansu wurin biki ba adakile hajiya kari tace"Sunyi tafiyane shiyasa...Suka shige motarsu laila ke jan motar suka fice hajiya
mama tabisu da gwalo.*Anitha...*
commet
And
Share
Vote

CZYTASZ
NA TAFKA KUSKURE..!
AkcjaSafwan wai me ka maida ni ne...? na haihu kuma na koma ina maka Renon D"a...? baka isa ba wlh......