Chapter 2

99 4 0
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*GYARA KAYAN KA...*
                    _{K'alubale gareku iyaye}_
                                        
                                  
                                          Gajeran labari


                           *NA*
UMAR FARUQ*D*

    BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

*PAGE 3&4*

Da gudu suka k'arasa cikin d'akin har suna karo da junan su sabo da jin sautin ihun ta. Durk'ushe take har lokacin a inda take tana wani irin kuka wanda ko sautin sa baya futa.
Turus suka ja suka tsaya gaba d'ayan su suna masu binta da kallo, lokaci d'aya kuma duk jikin su yayi mugun yin sanyi.
Ahankali mahaifin nata ya d'aga k'afar sa yana mai takawa ya fara matsawa kusa da inda take, jikin sa duk amace babu wani kuzari. Yayin da ita kuma mahaifiyar tata take tsaye har lokacin a'inda take ruwan hawaye na sauka daga cikin idanuwan ta zuwa kuncin ta.
Wuri ya samu ya durk'usa kusa da ita, tukun ya d'aga hannun sa ahankali jiki duk ba kuzari yana mai d'orasa akan kafad'ar ta, sannan ya d'ago fuskar ta. Dasauri ya kauda kai gefe sabo da yarce yaji wani irin k'unci da bak'in ciki sun caki xuciyar sa lokaci d'aya, sakamakon ganin yarce 'yar tasa tak'ara komawa.
Kallon su take yi daga shi har mahaifiyar tata da take tsaye agefe da idanun ta da suka rine daga fari zuwa kalar ja tsabar kukan da take. Gaba d'aya hallitar fuskar ta tasauya, leb'en ta ya bushe, idanun duk sunyo waje! Sai da tagama binsu da kallo tana jin ranta na k'ara ta farfasa da k'una, tukun ta kauda kai gefe, tana mai jan wata doguwar sheshekar kuka.
Tattaro jarumtar sa yayi tukun yak'ara dafa kafad'ar ta, sannan ya furta "shin har sai zuwa yaushe ne zaki dena wannan kukan khadija?, har sai zuwa yaushe ne zaki d'auki hak'uri da k'addara akan abun da yasame ki kibarwa Allah yabi miki hak'k'in ki?, khadija ina son ki sani ganin ki ayana yin nan da kike ciki ba k'aramun tada hankalin mu yake ba nida mahaifiyar ki, tabbas muma muna jin kalar yacce kikeji acikin ranki koma muce fiye da haka." Shiru yay yana mai sun kuyar da kansa k'asa yasa kafad'ar sa ya goge k'wallar dake shirin sakko masa daga cikin idanun sa, sannan ya d'ago yana mai d'orawa da cewar "tabbas ina jin k'unci da bak'in ciki acikin xuciya ta na abun da yasa meki 'yata, kuma ina jin inama ace inada hanyar da zanbi inbi miki hak'k'in ki da nabi dan... "Kai ko keda hanya Abba." Takatse masa maganr sa da fad'in haka tana mai kallon sa, sannan ta d'ora da cewar "akwai hanyoyi da yawa wa'yan da zaka iya bi kabi mun hak'k'ina har.... "Aa khadija, yi shiru basai kin k'arasa ba, domin ko nariga dana san abun da kike son ki fad'a, sai dai kuma ina son kisani wannan hanyar bamai yuwu ba ce, ba dan komai ba kuwa sai dan gudun tozar ta kanmu da fallasa sirrin mu ga mutanen duniya."  "Fallasa sirri kuma?, shin wai dama har akwai wani sirrin mu da yayi saura wanda duniya batasan dashi ba?, ai'ni ina ganin zuwa yanxu kuma babu wani sirrin mun da yake rufe banda wanda ya riga da gama ban kad'uwa."
Aa khadija kar ki fad'i haka, "cewar mahaifiyar tata" da sai lokacin ta iya tofa wani abun tunda ta tsaya awurin.
"Sun cuceni sun lalatamun rayuwa, sun mun babbar illa, amma wai ana cewa inyi hak'uri, koda yake bazan yi wani mamaki ba dan naji haka daga bakin ku, tunda dama kuna d'aya daga cikin mutanen da sukayi san... "Kina hauka ne khadija?, koko akan ki hakan tafara faruwa ne da har zaki nemu ki zauce?. Shin wai dama har akwai lokacin nan da zaixo wanda zaki iya bud'ar baki ki kallemu kina fad'a mana magan ganu munana amatsayin mu na iyayen ki?"
"Iyaye, iyaye, tabbas ku iyaye nane, amma sai dai.... Tayi shiru batare da tak'ara sa fad'ar abun da zata ceba tana mai juyar da kai gefe, jitake xuciyar ta na wani irin zab'al b'ala da k'una. Amma sai dai me? "Cewar mahaifiyar tata" da ranta ya fara b'aci. "Aa umman khadija, ke kanki kin san a irin halin da khadija take ciki yanxu dole sai muna mata uxuri, dan haka tashi muje kawai." Uban ya fad'a yana mai mik'ewa tsaye yayi gaba idanun sa cike fal da ruwan hawaye.
Juyawa itama tai ta futa tana mai goge fuskarta, yayin da ita kuma khadija tak'ara kife kai akan katifar ta tana mai sakin wani irin kuka mai sosa xuciya da ruhi, murzu kanta kawai take acikin katifah tana mai gwarasa da bango! Wani irin tuk'uk'in bak'in ciki da takaici ne suke tokare mata xuciya idan tana tuna abun da ya faru da ita, domin ko tariga data gama sanin tata ta k'are ita yanxu. Hakan yasa tun lokacin da abun nan yafaru da ita ta koma zaman d'aki arwala kawai ke sata futowa ko abinci bata iya ci, sannan kuma hatta mahaifan nata bata san ganin ko d'aya atsaye gaban ta, sabo da tana ganin kamar dama can sun san hakan zata faru da ita shiyasa basa kwab'ar ta akan abun da take, sannan kuma suka kasa kiyaye ta kamar yacce taga iyayen wasu daga cikin k'awayen ta na musu.

GYARA KAYAN KA... {Ƙalubale Gareku Iyaye}Where stories live. Discover now