Chapter 3

89 5 0
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*GYARA KAYAN KA...*
                    _{K'alubale gareku iyaye}_
                                        
                                  
                                          Gajeran labari

                           *NA*
UMAR FARUQ*D*

    BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

*PAGE 5&6*

.... "Habu kaine, me kuma kakeyi anan ne kaxo kayi durk'ushe?" Yajero masa tambayoyi yana kallon sa.
"Dama naxo na duba jikin khadija ne baba, dan Allah ka taimaka kace mata inan ina jiran ta." Wani irin farin ciki mahaifin khadija ya samu kansa aciki, sabo da jin har zuwa wannan lokacin akwai wa'yan da basa gudun khadija. Girgiza kai yayi yana mai jin jina hankalin yaron, tukun yace "jirani anan bara nashiga na futo."
Bewani jima aciki ba ya futo yana mai fad'in "tashi muje daga ciki." Sai da ya kaisa har cikin d'akin tukun ya juyo ya futo. Har zuwa lokacin tana nan adurk'ushe a'inda take kanta cikin guiwoyin ta, in banda suya da rad'ad'i ba abun da zuciyar ta ke mata. Wuri ya samu nesa da ita ya zauna, sannan ya furta 'barka da warhaka khadija." Shiru tai ba tare da tayi koda motsin kirki ba balle har yasa ran zata d'ago kanta ta. Hakan da ya gani ne yasa sa girgiza kai yana mai jin xuciyar sa na zafi da rad'ad'i, tausayin ta na k'ara bin ko wane lungu da sak'o na sassan jikinsa yana dulmuyewa. "Khadija ba zaki d'ago mugai sa ba, nine fah habun ki." Ya fad'a cikin sanyin murya sabo da yarce zuciyar sa tayi rauni na ganin halin da take ciki har yanxu.
Sai lokacin tukun ta d'ago kanta tana mai watsa jajayen idanuwan ta cikin nasa, tukun ta d'auke su dasauri daga kansa tana mai juyar da kai gefe. Dasauri shima ya rumtse idanuwan sa yana mai jin wani irin abu mai zafi na cakar xuciyar sa, sabo da yarce yaga kaman nin khadija sun sauya! Sauka yay daga kan kujerar da yake yana mai d'an matsawa kusa da inda take, tukun ya durk'usa akan guiwoyin sa, sannan ya furta "haba khadija, me yasa baza kiyi hak'uri ki d'auki hakan amatsayin kad'd'ara ki dena kuka ba?, shin har sai zuwa wani lokaci ne zaki bar zubda hawaye?, tabbas nasan ancutar dake cuta ba k'arama ba, kuma har kawo yau ina addu'ar Allah ya wargaza rayuwar duk tsinan ne da yayi miki haka." Ya fad'a yana mai juyar dakai gefe, tukun ya furzar da wata zazzafar iska daga bakin sa yana mai rumtse idanuwan sa da k'arfi, sannan ya bud'e su yana mai cigaba da fad'in, "ganin ki cikin wannan yana yin ba k'ara mun tayar mun da hankali yake ba khadija, tunda ga ranar da abun nan yafaru har kawo yau ban k'ara yin wani bacci mai dad'i ba, sabo da tina nin halin da kike ciki khadija, dan haka ina rok'on ki dan Allah badan niba kitai maka ki dena kukan nan haka ko zuciyo yin rayuka da yawa sasamu salama." Ya fad'a yana mai fesar da wata zazzafar iska daga bakin sa, idanun sa sun kad'a sunyi ja alamun yana cikin wani hali shima.
Sai lokacin tukun ta juyo da kanta b'arin da yake, sannan ta kallesa tana mai furta, "bana tina nin zan iya daina kuka har dai ba rayuwa ta bace tayan ke aduniya, bana tinanin dena kuka balle har na kwatan ta yin hakan, sabo da shine kad'ai abun da zanyi naji sauk'i acikin raina. Sun cuceni sun mai dani abar k'yama da nuni acikin al'umma, sun mun babban tabo wanda nake da tabbacin bazai tab'a goguwa ba daga nan har kisfewar k'asa, taya ya zan fara shirin dena kuka nida ban san inda mako mata take ba, taya ya kake ganin hawaye zasu bar futa daga cikin idanun da k'waro yayi mazauni aciki, taya ya kake ganin ruhi da zuciyar wanda ake k'yama zasu samu salama, bayan babu mai mar marin koda had'a hanya dashi, taya ya kak.... "Dakata khadija, meyasa kike fad'ar haka?, meyasa kike irin wannan furucin ne?, meyasa zaki ce ana k'yamarki sabo da kad'd'ara ta afka miki?. Dan Allah dan annanbi ina son daga yanxu kar kik'ara furta hakan agaba na, domin ko jin hakan na k'ara dulmiyar da ruhina cikin k'unci ne." Ya fad'a asanyaye, tukun ya tsaya yana mai sauke numfashi, sannan ya k'ara d'ago kansa cikin sanyin murya da karayar zuciya, yana mai d'ora k'wayar idanun sa akan fuskar ta, k'irjin sa na bugawa da k'arfi. Dak'yar ya iya d'aga lab'b'an sa da yake jin sun masa wani irin nauyi yana mai furta kalmar "khadijah!!" Tukun yayi shiru yana mai jiran amsar ta. Bud'e idanuwan ta tayi daga rufen da suke tana mai d'agowa ta kallesa, sabo da jin yana yin daya kira sunan nata wanda taji ya bambam ta dayar ce ya saba kiran ta ada. Kallon ta yayi ido cikin ido, tukun ya furta "shin zaki iya aurena khadija kuwa?"
Wani irin dum taji sautin dirar furucin nasa acikin kunnen ta, idanuwa ta k'ara bud'ewa jikin ta narawa bakin ta na furta kalmar "me nake shirin jine yanxu haka?, me yasa zaka mun haka habu?, me yasa zakake mun irin furucin da kasan bazai tab'a yiwu ba, ko ko kaman ta ni d'in wace ce yanx....  "Dakata khadija, duk naji abun da kika fad'a kuma nasa abun da kike gudu da tinani, sai dai kuma ina son kisani ni abubabar ba irin sauran mutanen da kike zato bane, dan Allah dan annabi khadija kar kice bakya sona, kar kice bazaki iya aure naba, domin ko idan har kika furta haka bansan wana irin hali zan shiga ba, khadija ban tab'a sanin ina sonki ba sai acikin kwana kin nan da kika shiga wannan halin, ada duk na zata kawai shak'uwa ce da abota tsakanina dake, amma kuma sai yanxu naga ne duk ba hakan bane, dan Allah na rok'ek'i kar kice bakya yina khadija, domin ko furta hakan gareni ba k'ara mun garari zai sani ba!" Ya fad'a yana mai had'e hannuwan sa wuri d'aya jikin sa na kyarma yarce kasan wanda aka saka acikin ruwan sanyi! Yayin da ita kuma khadija duk tabi ta rud'e gaba d'aya, in banda zubar hawaye ba abun da idanun ta keyi, ji take inama ace hakan mai yiwuwa ce, da tana da tabbacin yin farin ciki fiye da nasa, amma kuma sai dai ta ruga data san ayanxu babu wanda zai iya auren ta, koda ansamu ma tasan babu wanda iyayen sa zasu bari har dai sunji labarin abunda ya faru da ita. Zazzafan numfashi ta sauke, idanun ta na ambaliyar ruwan hawaye, tukun ta furta "ina ma ace hakan mai yuwuwa ce, tabbas da na kasan ce cikin farin ciki nima, amma sai dai kuka na riga dana san kawai kana fad'a ne habu dan hankalina ya kwanta, domin ko sanin kan kane kaima baza abarka ka aureni ba." Ta k'arashe maganar tana mai toshe bakin ta da hijan d'in dake jikin ta sabo da kukan da yaci k'arfin ta!  "Aa khadija, dan girman Allah ki dena kukan nan, wllh ganin ki cikin halin nan bak'aramun tayar mun da hankali yake ba, sannan kuma ina mai tabbatar miki da har dai kika ga auren mu baiyi ba sai dai wani iko na rabbi samawati, amma ta hurina bana tina nin akwai wata matsala, domin ko na riga da nashirya d'aukar ko wane irin k'alubale ne akan wannan abun, kuma nashirya yin yak'i da duk wanda yayi k'ok'arin dakatar dani daga auren ki tunda Allah bai haramta ba, dan haka ina son kiyi shiru ki dena kukan nan haka, domin ko nasan kad'd'ara ce ta afka miki kuma bata huce kan kowa ba." Girgiza masa kai tayi tana mai fad'in "a'a habu, dan Allah kawai kayi hak'uri kar ka saka kan ka cikin damuwa ta dalili na, kawai kabarni ayacce nake ni da Allah ya d'orawa wa, amma kar ka d'auki nauyin abun da ba zaka iya saukewa ba."
"Bana son jin irin wannan furucin daga bakin ki khadija, domin ko jikina na bani zanyi nasara, kuma kema ina son daga yanxu kisa aranki nid'in nan habu ina gab da zama mijin ki nan kusa bada jimawa ba, domin ko ashirye nake da fuskan tar ko wane irin k'alubale ne akan ki." Ya fad'a yana furzar da zazzafar iska daga bakin sa, yayin da ita kuma take ta binsa da idanu har lokacin hawaye na kwaran ya daga cikin su.  Matsawa ya k'arayi kusa da ita tayar ce har suna jin saukar numfashin junan su, tukun ya furta me yasa ba zaki dena kukan nan ba khadija?, me yasa baza kibar xuciya ta da ruhina su samu salama ba koda nayi ni d'aya ne khadija?, Yanxu nake son tafiya, amma sai dai kuma bana son hucewa nabar ki ahaka, dan Allah na rok'ek'i da kitsai da kukan nan haka nan khadija."  "Bazan iya ba habu, bazan iyaba, domin ko ina jin xuciya da raina na zafi akoda yaushe."  "Me yasa kike cewa ba zaki iyaba khadija?, me yasa kike fad'in haka ne?, ina son ki kwatanta yin hakan zaki iya."  "Bazan iyaba habu, bazan iya ba har sai lokacin dana tabbatar dana ga bayan tsinanun da suka mai dani abar nuni acikin al'umma."
"Kikwan tar da hankalin ki khadija, har dai wannan ne na miki alk'warin tsayawa kai da k'afa har sai naga bayan su sannan zan barsu."

Haka dai habu ya samu yay ta lallashin khadija har sai da tayi shiru sannan ya tafi, duk da dai tayi ne kawai dan hankalin sa ya kwanta, domin ko abun da yazo mata dashi yau ba k'aramun jefata yayi acikin wani tinanin ba.

*****
Tunda khairat tashiga gida bata k'ara gigin futowa ba, sabo da tana tsoron kar ta futo wannan yarin yar ta kama ta ta daka har yanxu da magariba ta gaba to.
Zaune suke iyayen nasu mata atsakar gida suna ta hira mai aiki na aikin ta, yayin da khirat kuma ke mak'ale jikin ummanta tana ta zuba mata shagwab'a.
Ka khairat rigima, wai me take sone da duk tabi tacika wa mutane kunne da gwaran ci yau ba yawo? "Cewar d'aya daga cikin abokanan zaman umman khairat d'in, da yake su ukku ne ahurin mijin nasu. "Ke ma dai kya fad'a wllh, aini nafi tina nin tsokana tayo ne d'azu data futa shiyasa duk tabi ta hanani sukuni yau." Umman khairat ta fad'a tana dariya. "To ai yanju ma jan tashi infuta, wai dama wace nayin ya ce dan nashe mata ya baja shine ta maleni." Gaba d'ayan su su ukkun suka kwashe da dariya sabo da jin abun da khairat ta fad'a, sannan d'aya daga cikin matan uban nata tace "Allah ya k'ara, maganin mai jan tsokanar tsiya." Kafa ta fara murzawa tana mai fad'in "wayyo ayyana umma cinga umman indo tana shokana ta ko." 
"To yi hak'uri kar kiyi kuka barni da umman ido nima sai na mata duka anan gidan yau."  "Yehhhh ummata to dake ta aga bana ingani cinji."  "Aa kibari sai anxo kwanciya bacci tukun zan zane ta, yanxu dai tashi ki shiga d'aki akwai nera goma akan mudubi sai ki d'auka kije kisiyo alewa kisha ko."  "Yeehhh ummata", ta fad'a tana mai mik'ewa daga jikin nata taje ta d'auki kud'in, sannan tayi waje aguje sai wurin mai kanti, yarce kasan ba dare bane ya gaba to.
Tana zuwa ta taddasa yana rufe k'ofa zai tafi masallacin magariba, kasan cewar ankira sallah dama.
Hakan yasa ta tsayawa tayi turus tana kallon sa, tukun ta zun b'uro baki tana shirin fara kuka. Har ya rufe zai tafi sai kuma ya lura da ita, hakan ne yasa sa cewa "a'a khairat 'yan mata lafiya dai ake shirin kuka, ko ko wani abun za'a siya ne?"  "Eh ayawa jan shiya, amma cine kake lufe k'ofa."  "Tom khairat kar kiyi kuka har dai alewa ce yanxu zan bud'e na baki." Ya fad'a yana dariya sabo da yarce 'yar take burgesa, tukun ya bud'e k'ofar ya d'auko ya bata ita kuma ta basa kud'in sa.
Kallon ta yayi tukun yace "maza maza yanxu ki huce gida kar ki tsaya ako ina kinga dai dare yayi ko." "Tom", ta fad'a tana mai zurawa aguje tayi gaba. Girgiza kai mai kantin yayi yana fad'in "wasu iyayen basu da tinani wllh, ace kamar wannan yarin yar 'yar k'arama haka ita ake bari na kaiwa har irin wannan lokacin awaje." Tsaki yad'an ja tukun ya rufe k'ofar sa ya tafi masallaci.

Khairat tana rugawa mai makon tatafi gida sai tak'i, sai ma lab'ewa da tayi akan kwana jikin katan gar wani gida tana lek'e, dan taga hucewar mai kanti masallaci sannan ta futo. Aiko tana gani ya huce ta futo tana ta dariya tare da cewa "shice nan na masha wayo", hhhhh! Hhhhh!! Tukun ta zura aguje tayi hanyar gidan su k'awar ta. Acan d'in ma tana zuwa ba tare da ta jima ba maman k'awar tata ta koro ta gida sabo da dare da taga yayi. Amma khairat na futowa sai tatafi bakin mai suyar awarar layin taje ta zauna tana rok'on matasan wurin da suke siya, sannan tana wasa da k'asa.
Atakai ce dai khairat bata tashi komawa gida ba sai da aka kusa isha, shima ganin baban su ya kusa dawo wane yasa umman ta tasa d'aya daga cikin yaran gidan yaje ya koro ta sabo da kar ya dawo ya bal bale ta ayar ce take cewa.

*****
Aunty nidai na rok'ek'i ki dena wani tura yaran nan masallacin dare,
ki dubi yarce gari yayi duhu fah isha ce ake yi bama magari ba ba."
"Ke wai dan Allah meyasa ke dai bakyason ad'ora yara ahanya ne?" "Aa wllh aunty wane irin bana son ad'ora yara ahanya, nifah ina nufin kawai sud'in ga zuwa na azahar da la'asar, amma dai na magariba da isaha da kuma aiken dare duk ki dena musa, sabo da wllh yanxu zamanin ba d'aya yake ba dana da."  "Ke dallacan yimun shiru, yaran da ba mata ba zaki tsaya kina isata da magan ganu marasa ma'ana akan su, ai sai ki jira idan naki sunxo saiki hanasu sallahr ma gaba d'aya, shima aiken kina yi da kanki har da ranar, ku tashi ku huce kuma kukayi zaune kuna kallon mu, wato kunji abun da take cewa har kun fara d'aukar hud'u barta ko, ai kuwa wllh baku isaba yara." Ta fad'a tana buga k'wafa, yayin da su kuma yaran suka tashi suka huce masallacin isha, duka duka babban cikin nasu ma shine me shekara takwas da haihuwa.
"Ke kuma malama ki dena mun haka gaban yara, kin gani dai yanxu har sun fara d'aukar banzar hud'u bar ki, tunda dai da da ankira sallah su da kansu suke mik'ewa suta basai nayi magana ba."
"To aunty Allah ya baki hak'uri ni banyi dan in b'ata miki ba, kuma ni ai agani na duk yaran dai nima nawa ne, sannan kuma ai *GYARA KAYAN KA* ba shike nufin sauke muraba ba 'yar uwa".......✍

#SHARE
#COMMENTS
#VOTE ND FOLLOW PLSS

                   WhatsApp nmbr
08038135929

           Umar faruq

GYARA KAYAN KA... {Ƙalubale Gareku Iyaye}Where stories live. Discover now