Chapter 9

60 3 0
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*GYARA KAYAN KA...*
                    _{K'alubale gareku iyaye}_
                                        
                                  
                                          Gajeran labari

                           *NA*
UMAR FARUQ*D*

    BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

*PAGE 17&18*

.... Da wani irin gudu ta k'arasa inda khadija take kwance tana mai janyota jikin ta tare da sakin wani irin gigitaccen kuka, hakan ne yasa su habu da mahaifin nata shigowa aguje ciki suma. K'am! Su kayi tsaye awuri d'aya xuciyo yin su na bugawa da wani mahaukacin k'arfi, durk'ushewa awurin mahaifin nata yayi yana mai sakin wani azababben kuka kamar ba namiji ba. Yayin da habu kuma ya juya baya jikin sa na wani irin rawa ransa namasa d'aci da k'una. Wani irin tausayin khadija yaji na ratsa kwane lungu da sak'o na jikin sa, ji yake inama Allah zai had'asa da wanda yay mata haka, tabbas ko da shine zai zama ajalin sa. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Allahuma ajirni fi musibati." Mahaifin khadija ya fad'a cikin matsanan cin kuka yana mai jin tsanar kansa da ya kasan ce mai tura 'yar sa aiken dare mai makon shiyaje da kansa, yayin da ita kuma mahaifiyar tata take wani irin kuka mai ratsa zuciya numfashin ta na futa afizge. Dak'yar ta iya tattaro jarumta tana mai cire hijabin jikin ta tasa kawa khadija ajiki, tukun tasa hannu tab'an b'are mata gam d'in da aka lik'e mata baki dashi. K'ara sowa mahaifin nata yayi zuwa wurin yana mai birkito ta jikin sa, sannan yasa hannu ya kwance hanuwan ta da aka d'aure. Sai alokacin tukun wani irin kuka ya kufcewa khadija wanda ko sautin sa baya futa. "Nashiga ukku ni binta na lalace, shikenan sun maida mun 'ya abar kwatan ce acikin unguwa, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un waye ne yamiki haka khadija?" Ciccib'ar ta mahaifin nata yayi yay gaba, suma mahaifiyar tata da habu suka bisa abaya. Basu tsaya ako ina ba sai ak'ofar gidan su. Mutafi asibiti abban khadija ba gida ya kamata ashiga da itaba. "Cewar maman khadija" ranta na k'una. "Ashe dama haka iyayen da ake yiwa 'ya'yan su fyad'e suke ji, Allah ya isa bamu yafe ba, ubangiji kabi mana hak'k'in mu." Ta fad'a wasu irin zafafan hawaye naciga ba da sauka a fuskar ta. Dan Allah maman khadija kiyi shiru, wannan kukan duk ba mai yi bane saima mutane kawai da zai kawo mana wurin nan idan kika cigaba. "Cewar baban khadija" yana mai jin zuciyar sa kamar ta futo. Tukun daga baya ya kalli habu, sannan yace "habu aina kake ganin zamu samu mai napep yanxu?"
Girgiza kai habu yayi tukun ya d'auke k'wallar dake sakkowa daga cikin idanun sa, sannan yace "akwai aminu na nan baya koshi sai akira." Tom shikenan kira mana shi habu. "Cewar mahaifin khadija" yana mai komawa jikin bango ya jin gina.
Zuwa yay ya kirasa suka tawo tare, tukun aka saka khadija aciki suka tafi asibitin har habu da yazauna agefen mai adai dai tar shima. Sosai likitocin da suka duba khadija sukayi bala'in tausaya mata tare da alawadan wada da yayi mata haka. Ana gama yimata aikin da za'ama ta iyayen nata suka nemi sallama wai dan kar zaman su asibitin yasa kowa ya fahimci abun da ke faruwa cikin unguwa. Batare da wani b'ata lokaci ba aka rubuta musu sallma sannan aka fad'awa mahaifiyar tata duk yarce zatayi ta kula ita, kasan cewar dama asibitin kud'i ne tukun suka tawo gida. Sai da har sukaxo k'ofar gida tukun habu ya musu sallama ransa duk ba dad'i. Godiya sosai tare dashi albarka iyayen khadija sukayi masa sannan ya juya ya tafi gida cike da tausayin khadija azuciyar sa.

Tun daga wannan lokacin duniya ta juyewa khadija daga dad'i zuwa kishiyar sa, gaba d'aya ta canxa ta koma bata da abun yi sai kuka da zaman wuri d'aya, bata tab'a tina nin haka 'yan matan da ake yiwa fyad'e suke shiga k'unci ba sai da abun yazo kanta. Gaba d'aya ta dena kula iyayen ta ta dena yiwa kowa magana acikin gidan, domin ko gani take sunfi kowa laifi tunda sune suke aiken ta da dare, hakan yasa take jin haushin su, sannan ko magana suka mata bata amsawa, ta fad'awa iyayen nata ko suwaye suka mata haka, amma sai haka suka ce tayi hakuri tabarwa Allah ya mata sakayya kawai, sabo da wai gudun fallasuwar sirrin su, sai dai ita kuma ko kad'an hakan bai mata ba, sannan kuma bata tinanin zata iya hak'urin, domin ko acewar ta har dai ba ad'auki mataki akan suba Allah kad'ai yasan iyakar yaran da zasu cutar, ita kuma ayanxu ko mak'iyar ta bazata so irin hakan ta faru da ita ba.
Tun awashe garin ranar da abun ya faru aka fara zancen acikin unguwa, ba dama mahaifin khadija ya futa waje sai kaga har nunasa ake ana bada labari, wanda gaba d'aya suka rasa ta inda maganar ta futa har jama'a sukaji, hakan ne yasa gaba d'aya khadija ta dena zuwa ko ina gudun kar ta futa agoran ta mata sai yau da habu yaxo.
Ta b'angaren habu ma daren da abun nan ya faru gaba d'aya kasa rintsawa yay, da zarar ya rumtse ido ba abun da yake gani sai yana yin da yabaro khadija aciki. Sosai yake matuk'ar jin tausayin ta na ratsa ko ina na jikin sa, babu abun da yafi tayar masa da hankali sai irin yarce yaji mutane na zancen acikin layi, hakan ne yasa tausayin ta k'ara ninkuwa acikin zuciyar sa har ya fara tinanin yarce zaiyi yasata farin ciki. Lokaci d'aya yaji yana muradin auren ta ga wata irin soyayyar ta da ta cafki xuciyar sa.

GYARA KAYAN KA... {Ƙalubale Gareku Iyaye}Where stories live. Discover now