Chapter 4

69 4 0
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*GYARA KAYAN KA...*
                    _{K'alubale gareku iyaye}_
                                        
                                  
                                          Gajeran labari


                           *NA*
UMAR FARUQ*D*

                                Fllow me on Wattpad@umarfaruqD

    BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

*PAGE 7&8*

Yaran suna zuwa bakin masallacin babban ya tura su yana mai fad'in "kuyi gaba ku shiga nima yanxu zan tawo." Shigewa sukai ciki sai da har ya tabbar sun shiga tukun ya juya baya da gudu ya koma wurin da yaga yara suna wasa akan yashi yaje ya jona su.
Anan cikin massalacin ma kuwa ana kawai sujjada d'ayan yaron mai bin babban yatashi yalallab'a ya fuce, shiwai dan kar yayan yagan sa ya fad'awa maman tasu idan suka koma shiyasa yay haka. Yana futa shima yayi d'ayar hanyar yaje ya had'e da yara suka fara wasan banza. Yayin da shikuma d'an karamin nasu yay ta bin sallah yana mai yin duk yacce yaga anayi.
Sai da har liman yazauna zaman tahiya wato yana shirin sallama tukun yaran suka dawo suka zauna batare da wani yaga wani cikin su duka biyun ba. Ana idar da sallah babban ya kama hannun k'annen nasa ya jasu suka tafi gida

****
Washe gari bayan safiya tayi habu yayi wanka ya gama shirin sa tukun yashiga cikin gida dan yayi break fast.
Azaune ya samu mahaifiyar tasa akan kujera bakin kiching tana nata karin.
K'ara sawa yay har inda take tukun yasamu wuri daga gefen inda take ya durk'usa yana mai fad'in "umma ina kwana antashi lafiya."  "Lpy k'alau habu fatan kaima katashi lpy?" "Lpy k'alau wllh umma." "To masha Allah yanxu sai katashi kashiga kiching ka d'auko abun break d'in ka kasha ko."
"Eh umma amma kafin nan dama akwai wata 'yar magana ce dana keson muyi dake."  "Magana kuma, to bisimillah ina jinka." Uhm! Uhm! "da..ma umma ina son in fad'a miki ne ki...sanarwa baba na sa..mu matar...da..za..n aura." Ya fad'i maganar ararrabe kamar mai jin tsoron fad'a. "Masha Allah, kai Alhmdllh amma naji dad'in wannan zance naka habu, Allah yasan ya alkhairi ya kuma kaimu lokacin."  "Ameeen" ya fad'a acikin ransa tukun yayi shiru ba tare da ya k'ara cewa komai ba.
"To amma ita yarin yar 'yar wace unguwa ce, sannan kuma suwaye mahaifan ta?" Damm! Yaji gaban sa yayi wata muguwar fad'uwa sabo da yarce tambayar umman tasa tazo masa abazata! Sosa kansa yay gumi nafara karyo masa, lokaci d'aya jikin sa yad'an fara mazari, tukun ya sun kuyar dakan sa k'asa yana mai sosa k'eya, sannan ya fara d'aga labban sa d'akyar yana mai furta "ai kin ma santa umma." Tukun yayi shiru ba tare da yak'ara cewa komai ba. "Na santa kuma, a'ina take ne to?" "Uhm!... Nace dama.. Da..ma khadija ce 'yar gidan mlm.. Is.ma'il na bayan layin nan..na.... "Kha me? Wace khadijar kake nufi habu?, ince dai ba kana nufin wannan yarin yar data gama tamba d'ewa ba atskar layi cikin dare ba ko?" Mahaifiyar tasa ta fad'a azafafe tana kallon sa! Yayin da shikuma jikin sa yafara rawa k'irjin sa na dukan tara tara, hankalin sa idan yayi dubu sai da duka ya tashi sabo da jin abun da mahaifiyar tasa ta fad'a. "Tambayar ka fah nake kamun shiru kana kyarmar munafurci." Ta fad'a da k'arfi tana tsare sa da idanuwa.
Bakin sa na rawa jikin sa na kyarma gumi na yanko masa tako ina ya furta "itace umma" awani fizge! Sannan yay sauri ya d'ora da fad'in "amma wllh umma duk yarce kike tina nin khadija ba haka take ba kad'd'ara ce kawai ta afka ma.... "Ka dallacan rufemun baki shasha shan banza mara hankali, ashe kai dama kai wawane ban sani ba sai yanxu, ashe duk kallon dana ke maka na mai hankali ba haka kake ba, in banda kai lusari ne me zakayi da yarin yar da aka riga aka lalata tun atiti, yarin yar da kowa da kowa yasan abun da ya faru da ita acikin unguwa, wato sai da 'yar tasu tariga tagama lalacewa tukun zasu ce zasu baka auren ta tsabar sun mai daka lusari ko, kai kuma da yake wawane shine har kakwaso jiki katawo kake fad'a mun ko?, to wllh tallahi ko bayan raina ban yadda ka auri wannan yarin yar ba, kai bari na fad'a maka ma koda wasa idan kayi kuskuren barin mahaifin ka yaji wannan batun sai nayi mugun sab'a maka, dan bazan tab'a bari a auro mun mugun iri acikin gida ba hakan nan kawai mummu nan tabo yazo yabi jiko kina abanza!"
Sosai hankalin habu yayi bala'in tashi sabo da yarce yaji mahaifiyar tasa na fad'i, lokaci d'aya yabi ya ki d'ime ya rud'e jikin sa yadin ga rawa, hankalin sa yayi k'ololuwar tashi, ko kad'an bai tab'a tinanin haka san khadija yayi nisa acikin zuciyar saba sai yanxu da yaji yana shirin rasa ta. Dasauri ya durk'usa yana mai zuba k'afafun sa akasa tare da had'e hannuwa sa wuri d'aya, sannan ya fara furta "dan girman Allah da annabi kar kiyi mun haka umma, na rok'ek'i kar kiyi sana din rugujewar rayuwa ta ke da kanki, wllh tallahi umma ina san khadija so mai tsanani, ina mata san dani kaina ban san iyakar adadin saba, na rok'eki umma kiyi hak'uri kijan ye wanann kud'irin naki, domin ko ita kanta yarin yar bada san ranta abun ya faru ba khaddara ce ta afka mata, kuma har kawo yau d'in na.... "Kamun shiru shasha shan banza wanda baisan ciwon kansa ba, to bari kaji in fad'a maka ba rugujewar rayuwa ba ko mutuwa zakayi akan baka auri yarin yar nan ba sai dai ka mutu, amma ni dai bazan tab'a bari ka auri yarin yar data gama zama bazawara ba tun agidan su, dan haka ka tashi kab'ace mun daga nan kar ka kuskura na k'ara jin ko da kwatan kwacin wannan zancen acikin gidan nan!"
Sosai habu ya k'ara kid'i mewa har baisan lokacin da ya mik'e dasauri ba yana mai kama hanyar waje ya fuce.
Tana ganin wucewar sa ta buga wani mahaukacin tsaki tana mai fad'in "zancen banza zancen hofi, wato da can baka tashi san yarin yar ba sai yanxu data ke da mummunan tambari ajikin ta kenan, salan kawai mugun tabo yazo yadin ga bin irina ko, to wllh hakan ma bazai tab'a yiwu ba kuwa."

GYARA KAYAN KA... {Ƙalubale Gareku Iyaye}Where stories live. Discover now