Chapter 7

59 3 0
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*GYARA KAYAN KA...*
                    _{K'alubale gareku iyaye}_
                                        
                                  
                                          Gajeran labari


                           *NA*
UMAR FARUQ*D*

    BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

_*SPECIAL GIFT TO UMMU ASLAM.*_

_HAK'IK'A INA JIN DAD'IN YARCE KIKE YIN COMMENT AKAN BOOK D'IN NAN BA KAD'AN BA, RABBI YA BIYA MIKI BUK'ATUN KI NA KHAERI YA KUMA SHIRYA MIKI ZURI'AH. GABA D:AYA WANANN PAGE D'IN KYAUTA CE GAREKI KIYI YARCE KIKE SO DASHI NAKI NE KE KAD'AI._

*PAGE 13&14*

....10:30pm, sanye take da dogon hijabi wanda tsayin sa zai kai har guiwar ta, tana tsaye gaban wani shagon charge da yake cike da matasa tako ina, wasu na hirar duniya yayin da wasu suke labarin k'wallo, wasu kuma na labarin 'yan mata.
Fad'i take "dan Allah sani ka mik'o mun wayata bana son rainin hankali fah."  "Haba yarin ya ai wallahi idan baki bani kud'ina ba yau bazan baki wayar nan ba kema."  "Mlm kar karai namun hankali fah, duka duka nawane kud'in naka da har zaka kama yiwa mutane zancen banxa."  "Eh anji koma nawa ne d'in sai azaro abani abuna har dai kina son kwana da wayar ki kusa dake kema." Mtsweee! Taja d'an gajeran tsaki, tukun ta juya bayan ta inda wasu samari ke zaune su hud'u suna cin gyad'a mai gishiri tare da hira. "Habu dan Allah d'an taso kaji mana, wai yau ni sani ke shirin rainawa hankali." Ta fad'a tana nuna d'aya daga cikin matasan da ke zaune. Na zaune atsakiyar ne ya mik'e yana mai fad'in "yane 'yan mata wai me ke faru wane?, yadai guy d'in nan yake miki haka ne wai?" Mtwssss! Ta d'anja tsaki tana mai fad'in "kai dai bari kawai, ai wllh wataran sai nayiwa yaron nan tsirara awurin nan har dai bai dena raina mun hankali ba."  Hhhhhh! Wanda ta kira da habu ya kwashe da dariya yana mai fad'in "kice akwai kallo ranar", ya fad'a yana mai k'ara sowa inda take, sannan yace "nawa ne kud'in naka malm?" 
     "D'ari ne na kwana biyar, sai abani abun idan har ana son ayi amfani da waya." Hannu habu yasa a aljihu tukun ya zaro naira d'ari biyu yana mai mik'a masa tare da fad'in "dallacan karb'i tsiyar ka ka bamu wayar mu mlm." Mtwseee! Sani mai chagi yaja tsaki, tukun yace mlm kafuta daga harkata kuma baza abayar da wayar ba tunda ba kai kakawo taba."  "Kai fah sanin nan mugun d'an raini wayo ne, to naratse da Allah sai ka kawo ta." Ta fad'a tana wartar d'ari biyun ahannun habun tukun ta mik'awa sani mai charge tana fad'in "ga tsiyar ka nan mlm." Karb'a yay yagama juyata, sannan ya zaro wayar ya mik'o mata tare da changen ta. Hannu tasa ta karb'a tana mai jan tsaki, tukun ta zaro kud'i acikin hijabin ta tana mai mik'a masa tare da fad'in "gashi wannan kabawa mama nutri milk mai sanyi, da kuma irin biscuite di'n da kaba ta jiya nina manta sunan sa ma." Karb'a yay ya d'ebo abubuwan da tace ya sama ta abak'ar leda tukun ya mik'o mata tare da changen ta.
D'auka tai tukun ta shammace sa ta k'wala masa jarkar milk d'in aka, sannan ta ruga da gudu tabar wurin. Zaki xo ne gobe yarin ya wllh sai na rama, "cewar sani mai charge yana dariya."
Can daga nesa taje ta tsaya tukun habu ya k'araso inda take suka ware atsaye suna hira yarce kasan ba dare ba.

Kun san me, wllh waccen yarin yar ba k'aramin had'uwa tayi ba, kuma insha Allahu nan ba da dad'ewa ba sai na d'an d'ane ta. "Cewar wani saurayi" da suke zaune akan wani benci daga gefen wurin mai chargen su ukku suna shaye shaye. "Ai wllh guy nima kullum yarin yar nan tazo wurin nan sai naji yana yina na sauyawa."
"Ku dai kawai ku bari guys zamu san abun yine, tun da dai ita bata da lokacin futowa ta tsaya sai dare ai duk abun zaixo mana da sauk'i ma." D'aya daga cikin su ya fad'a sannan suka kwashe da dariya.Yayin da can b'arin su khadija kuma suke tsaye ita da habu suna ta hira tare da k'yalk'yala dariya har sai da shad'aya na dare tayi tukun sukayi sallama ta huce gida bayan ya rakata hanya.

Tana shiga tasawa gidan sakata tukun tak'a rasa d'akin mahaifiyar tata tana mai mik'a mata ledar ai ken ta tare da fad'in "gashi nan mama." Karb'a tayi tukun tace "wai ina kika tsaya ne kika barni tun d'azu ina jiran ki anan."  "Wllh mama sani me charge ne ya hanani waya ta shiyasa."  "To akan me ya hanaki wayar ki kuma?" "Wai dan ban biyasa kud'in rannan ba, amma ai ya kawo ta ma habu ne ya bada kud'in."  "To ai shikenan sai ki huce kije ki kwanta sai da safe kuma." Juyawa khadija tai tatafi d'akin ta ta kwanta.

Haka koda yaushe take kasan cewa kullum rana ta Allah khadija na hanyar waje, sannan kuma ranaku d'ai d'ai ne suke zuwa su huce batare da an aike ta bayan k'arfe tara na dare ba, kuma aduk lokacin da za'ayi aiken mahaifin ta na cikin gidan amma bazai je ba sai dai su aiketa, sau tari wani lokacin ma shine ke aiken ta kanti tasiyo musu kayan shayi.

Tun daga ranar da khadija tai kai dare awurin sani mai chage wa'yan nan matasan masu shaye shaye dake wurin suka fara shirya yarce zasu same ta cikin sauk'i su biyawa kansu buk'ata. Hakan yasa tun washe garin ranar suka fara dakon ta tare da fatan Allah yasa idan ta futo takai har shad'aya kafin ta koma. Sai dai kuma har kawo yau kwana biyu da waccen futo war tata bata k'ara kaiwa goma bama awajen.

Kwance take akan katifar ta ta lullub'e jikin ta da rabin bargo sabo da yana yin sanyi da ake ciki. Chart take awayar ta tana ta sakin murmushi da alama dai ba k'aramun dad'in hirarar take jiba.
  "Khadija!!" Ta jiyo sautin muryar mahaifiyar ta tana kwad'a mata kira. "Na'am mama gani nan." Ta fad'a tana mai mik'ewa tsaye tajan yo hijab d'in ta da tsayin sa zai kai har gwiwar ta ta d'orasa akan 'yar fingilar rigar baccin dake jikin ta. Futa tai tak'ara sa har d'akin da iyayen nata suke bakin ta d'auke da sallama. Amsa mata sukayi tukun ta d'aga labulen ta shiga. Zaune suke agefen gado mahaifin nata na danna sistem d'in sa, yayin da ita kuma mahaifiyar tata take danna tata wayar sunayi suna hira. Gani mama, "cewar khadija" tana mai tsayawa agefe. "Yawwa khadija kije fallow ki duba kan kujera ta zakiga jakata akai, sai ki bud'e ki zari kud'i kije wurin sani kisiyo mun nutri milk duk yau nakasa cin abinci wllh."
     "Tom" ta fad'a tukun ta juya tatafi. "Idan kin dawo sai ki rife k'ofar gidan kinji ko." Ta jiyo sautin muryar mahaifin ta yana fad'in haka. "Tom" ta fad'a tana mai zuwa ta d'auki kud'in sannan ta futa.

Tsit garin yake bako alamar mutane agaba d'aya layin nasu, kowa ya shiga gida sabo da sanyi da ake kwad'awa. Hakanan kawai ta tsinci kanta da jin tsoro tare da fad'uwar gaba, sabo da yarce taga garin yayi bak'ik'k'irin gashi ba kowa akan layin nasu. Sauri sauri gudu gudu ta farayi har tasha kwanar inda sani mai chage yake. Hasken da ta hanga awurin tare da 'yan tsirarun jama'a ne ya sata sakin ajiyar zuciya ta ciga ba da tafiyar ta ahankali. Tana zuwa ta fad'awa sani abun da zai bata ya had'o duka yabata harda changen d'ayan batteryn ta. Har ta juya ta tafi sai taji murayar wani daga cikin matasan dake zaune awurin yana fad'in "au yau abun 'yar shariya ce kenan khadija?, kinzo ba magana kuma shine zaki tafi bako magana KO?" Hakan yasa ta juyowa ta dawo inda suke tana mai fad'in "wllh ba haka bane ba, ban lura da ku bane kuma gashi yau ana matsanan cin sanyi shiyasa nake son hucewa gida."  "Kuji wai wannan yarin yar ce sanyi yake hanawa tsayuwa, ke dai kawai kice yau bakiyi niyyar kulamu ba sabo da kinga habu baya wurin ko?"
     "Yawwa kai dan Allah inama habun yake, ni yau duka ban gansa bafah?"  "Habu na gida yau baiyi zaman wurin nan ba, ko akira miki shine?"  "Aa barshi kawai ya huta, inya so gobe ma had'u idan Allah ya kaimu."
Daga wannan zancen da suka fara mai makon khadija ta musu sallama tatafi gida sai tak'i saima tsayuwa data gyara suka fara hira suna dariya, ba ita tayi musu sallama tatafi ba har sai da k'arfe goma da rabi tayi.
Tunda ta dun faro kwanar layin su taji gaban ta na wani irin fad'uwa, zuciyar ta na bugawa da mahaukacin k'arfi, wanda tarasa dalilin daya sa ta jin hakan. Juyawa tai ta kalli gaban ta sannan ta kalli bayan ta, ganin ba alamun wani mutum dake tawowa alayin ne yasa ta k'arajin wani irin tsoro ya lullub'e ta, hakan yasa ta fara sauri sauri har tana d'an had'awa da gudu gudu, sai dai kuma tana zuwa tsakiyar layin nasu taga wani irin farin haske ya kashe mata idanuwa! Hakan yasa ta mutuk'ar firgita ta juya baya da sauri da niyyar komawa. Nan d'in ma ko taku d'aya bata k'arayi ba aka k'ara dalle ta tanan b'arin ma, take awurin jikin ta yafara rawa hankalin ta yayi bala'in tashi, hannu ta d'ora aka tana mai furta "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un", tukun ta bud'e baki ta daddage tana shirin sakin ihu, amma sai taji ansa hannu an matse bakin nata tayar ce ko magana ba zata iya yiba balle kuma ihu!........✍



COMMENTS, SHARE AND VOTE PLS
                  
             08038135929
   
        Umar dayyan ✍

GYARA KAYAN KA... {Ƙalubale Gareku Iyaye}Where stories live. Discover now