Chapter 10

76 5 0
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*GYARA KAYAN KA...*
                    _{K'alubale gareku iyaye}_
                                        
                                  
                                          Gajeran labari


                           *NA*
UMAR FARUQ*D*

                     
                  _Wattpad@umarfaruqD_

    BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

*PAGE 19&20*

Yinin yau gaba d'aya habu kasa aiwata da komai yayi, sai faman zirya kawai yake tayi daga cikin gida zuwa waje, lokaci d'aya yabi ya zabge ya rame sosai kai kace bashi da lafiya ne. So yake ya k'ara yiwa mahaifiyar tasa bayani akan khadija ko zata amince, amma sai dai yana tsoron tin karar ta. Ta fannin itama mahaifiyar tasa tana lura da duk yana yin da yake ciki, amma sai dai tad'au karwa kanta alwashin komai zaiyi sai dai yayi amma ba zata tab'a bari ya auri yarin yar nan ba. Yayin da itama k'anwar tasa take lura da komai, sannan ta d'auki alwashin sanarwa mahaifin su ab'oye ba tare da kowa yasani ba, gudun kar d'an uwan nata yakamu da wani ciwon sabo da yarce taga duk ya canza acikin yini d'aya.

****
Tun lokacin da khairat ta shigo gida bata k'ara gigin ko k'ara takawa k'ofar gida ba sabo da tana tsoron kar ta futa halima ta kamata ta daka har kawo yanxu misalin k'arfe biyar na yamma. Zaune take jikin mahaifiyar tata tana ta faman zuba shagwab'a tare da tumur mushe ta.
K'arfe shida dai dai na yamma sukayi bak'i agidan nasu, k'atuwar ta barma aka d'auko aka shimfid'a musu atsakar gidan gaba d'aya suka zauna akai har matan gidan. Aiko Take awurin hira ta b'alle, yayin da khairat kuma ta hana umman ta sakat tana ta fama 'yan koke koke tare da diddira k'afa fuwa. Kallon ta tayi tana mai fad'in "wai dan Allah me yake damun ki duk kika bi kika isheni da koke koke?" Banza khairat d'in tayi bata ce komai ba sai kukan ta data cigaba dayi ma. Hakan ne yasa umman tata tasa hannu ta janyo jakar ta, tukun ta bud'e ta tana mai zaro nera goma tare da fad'in "anshi kije kisiyo alewa kinji." Karb'a khairat d'in tayi tukun tamik'e tana mai zurawa aguje tayi waje. Yayin da ita kuma uwar tata ta gyara zama suka ciga da kwasar hira.
Da gudu khairat ta k'arasa kanti, sai dai tana zuwa tayi tsaye turus atsaye sabo da ganin kantin da tai arufe, da alama dai ya tafi masallaci ne kasan cewar anfara shiga sallah.  Hakan da khairat tagani ne yasa ta tale baki ta fara kuka tare da komawa jikin bishiyar wurin ta jin gina. Tana nan tsaye awurin ta hangi tanimu ya bud'e shagon sa ya shiga. Hakan ne yasa ta yin dariya tana mai fad'in "yawwa baya naje tanimu abani ayawa." Tukun ta zura aguje tana mai yin shagon nasa.

****
"Al'amin, sufyan, habib, wai me kuke yine da har yanxu baku huce masallaci ba bayan kuna jin har ankusa sallamewa?"  "Yanxu zamu tafi arwala muke yine." Babban ya fad'a da k'arfi yarce uwar tasu zataji kasan cewar tana daga cikin d'aki ne.
"To wai aunty mai zai hana kawai su zauna suyi sallar tasu acikin gida mana, tun da dai naji har anfara sallamewa ma fah."  "Wai dan Allah fatima meyasa kike yimun hakane?, ke ace arayuwa kwata kwata bakya son ad'ora yara akan turbar dai dai."  "Aa aunty wllh ko kad'an ba haka nake nufi ba, kawai dai naga suna zuwa da rana ne, sannan kuma zamanin ne yanxu ya canza gaba d'aya duniyar talalace, mutanen banxa sun yawai ta acikin ta shiyasa."  "Lallaine yarin ya, aikuwa da zaki tai maki kanki ma da kinyi shiru kin dena wahalar da bakin ki akan wannana batun, dan nidai bazan iya dena turasu masallaci ba tare da aiken dare idan buk'atar aiken ta taso."  "Tom ai shikenan aunty Allah ya tsare ya kiyaye kuma."  "Yawwa koke fah yarin ya, ashe dama can kin iya wannan adu'oin kika tsaya kina ta b'ata bakin ki tun acan baya." Uhmmm! Ita dai fatima tace ba tare data k'ara furta komai ba.

GYARA KAYAN KA... {Ƙalubale Gareku Iyaye}Where stories live. Discover now