Chapter 12

47 6 0
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*GYARA KAYAN KA...*
                    _{K'alubale gareku iyaye}_
                                        
                                  
                                          Gajeran labari


                           *NA*
UMAR FARUQ*D*

                     
                  _Wattpad@umarfaruqD_

    BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

*PAGE 23&24*

Dasauri yayan kahirat ya sun kuce ta yana mai yin cikin asibitin da ita da gudu, biyo bayan sa suma sukayi in ban da kuka babu abun da umman khairat keyi. Sosai likitocin suka yi bala'in tausayawa khairat tare da yin tsinuwa ga wanda ya aikata mata hakan.
Arikice baban khairat ya shigo cikin asibitin hawaye na malala daga cikin idanun sa, k'ara sawa yay inda ya hangi matan nasa tsaye yana mai ce musu "ina khairat d'in." Umman indo ce ta iya basa amsa tana mai fad'in "suna ciki ita da likitocin suna mata aiki." Yayin da ita kuma umman kairat d'in keta wani irin kuka mai sosai zuciya. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un." Ya fad'a yana mai komawa gefe ya zauna rik'e da kansa sabo da yarce yaji yana sara masa. Wani irin haushin umman khairat yake ji bana wasa ba, ko kad'an baiji tausayin ta ba na kukan da yaga tana yi saima wata tsanar ta da yaji ta wanxu acikin zuciyar sa, domin ko gani yake koma mene itace sanadi, tunda data na tsare ta ta hanata yawo da duk hakan bata kasan ce da ita ba." Suna nan tsugunne awurin har bayan shud'ewar awa guda tukun likitan da kewa khairat aikin ya futo daga cikin d'akin idanun sa sunyi jajir. Dasauri suka yi kansa suna masu tambayar sa "ya jikin nata doctor, ba dai ta mutuba ko?"  "Jiki alhmdllh", ya fad'a tukun ya d'ora da cewar "ina mahaifin ta yake?"  "Ganin nan doctor", baban khairat ya fad'a. "Biyoni muje office to." Ya fad'a yana mai yin gaba.

****
Da gudu suka k'arasa cikin asibitin hankalin su gaba d'aya amugun tashe. Tunda ga harabar asibitin lubna tafara k'wallawa likitocin kira awani haukace. Lokaci d'aya duk tabi ta zauce ta futa daga hayyacin ta. Nurses ne suka zo da gadon marasa lafiya suka d'ora yaran akai, tukun aka turasu zuwa ciki. Sosai hankalin likitocin yayi bala'in tashi sabo da ganin yarce akayiwa yaran rashin imani. Cikin kid'ima likitan ya futo daga cikin d'akin da aka shigar da yaran yana mai yowa inda yaga su lubna. "Ina mahaifin nasu yake?, maza maza kabi yoni office yanxu." Ya fad'a yana kallon makwabcin su lubna tukun yayi gaba dasauri. Binsa yayi abaya suma su luban da fati suka bisa abaya suna ta faman kuka abun gwanin ban tausayi.
Gumi likitan ya sharce daga goshin sa, sannan ya turowa alhaji bala makwabcin su lubna wata farar takadda gaban sa yana mai fad'in "ga wannan ina son yanxu yanxu kasa ka hannu ajiki, sannan kuma kaje ka biya kud'a d'en nan sabo da sai anyiwa yaran aiki." Wani irin kuka lubna ta fashe dashi tana mai fad'in "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wayyo Allah na shiga ukku nalalace ni lubna!" Yayin da fatima ma ke wani irin kuka mai tsuma zuciya da ruhi.
Jiki amace ya mik'a hannu ya d'auki takar dar yayi singning, sannan ya sake mik'awa likitan. Karb'a yayi tukun ya mik'o masa ta kud'in yana mai fad'in "gawan nan ka gaggauta zuwa kane mo kud'in abiya kafin nan da awa biyu." D'auka yayi yana mai juyawa ya futa, binsa su lubna suka saka yi abaya. Yayin da shikuma likitan ya buga uban ta gumi da hannu bibiyu yana tinanin kome ne ne yasa akayiwa yaran nan haka.

*****
Zaune yake akan kujera ya zubawa likitan idanu yana sauraran bayanan da yake masa. "Alhmdllh mun mata duk abun da ya kamata kuma muna saran farfa d'owar ta akowane lokaci yanxu. Sai dai kuma azahirin gaskiya ba k'aramar illah aka yiwa yarin yar ba. Domin ko ayarce binciken mu ya nuna tayi matuk'ar firgita tayar ce har k'wak'wal warta take bara zanar dena aiki."  "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yanxu meye ne abunyi doctor?"  "Agaskiya babu wani abun yi yanxu, domin ko mun riga da mun gama yima ta duk wanda ya kamata muyi, sai dai kawai muzu bawa sarautar Allah ido zuwa lokacin da zata far fad'o, inyaso sai muga awane yana yi zata tashi, yanxu dai kawai addu'a zakuyi mata Allah ya tada kafa d'un ta." Gigiza kansa yayi wasu irin hawaye na silalowa daga cikin idanu wansa zuwa kun cinsa. "Sai kuma abu na k'arshe shine ina mai baku sahwarar tsawai ta bin cike tayar ce za'a gano wanda yayi mata wannan aika aikar, kar ku kuskura kuce zaku rufe maganar iya yaku sabo da wai gudun kar jama'a susa ni, domin ko yin hakan zai zamto kamar kun bawa wanda ya aika ta wannan d'an yen aiki damar ciga ba dayi akan wasu yaran, akwai wata riga da aka kawo yarin yar aciki wacce yaron hurin ka yace mana da ita suma suka ganta akai, ina ganin ita kanta zata tai maka wurin bin ciko wanda yayi wannan ta'asar, hakan yasa na ajiye ta acikin d'akin idan kana buk'a tar ta sai muje in baka. Sannan kuma abun da ban fad'a muku ba shine na kira 'yan sanda tun lokacin da naga yarin yar kuma sunyi duk abun da ya kama ta, sannan sun ce zasu dawo da anjima idan kazo." 
         "Godiya nake doctor, kuma insha Allah zan tsaya kai da k'afa wurin bin ciken tsinan nen da ya aika tawa wannan yarin yar haka. Ya fad'a yana mai mik'ewa ya futa daga office d'in.

GYARA KAYAN KA... {Ƙalubale Gareku Iyaye}Where stories live. Discover now