26

620 62 24
                                    

Bayan tafiyar iyayen Faruk kawunnan Ummu hani suka rabe kuɗin a tsakanin su, yayin da Kawu Musa ya ce gobe zai je ya samu ita ummu ɗin, haka suka watse kowa cike da farin ciki.

Shiko Faruk tun bayan tafiyar su Abbansa ya kasa zaune ya kasa tsaye, jira yake kawai su dawo yaji ya sukayi dan tun jiya yake roƙon Abbansa ya yadda aɗaura auren, yace ina shi ai an dena haka.

Aiki suna dawowa tunma kan su firfito, yai gun motar da hanzari Kawu ƙarami ya nufa dan yasan shine kawai zai iya faɗa masa me akayi.

Shima kawun murmushi yai kafin yace wato yaran yanzu ba kunya, to an ɗaura shikenan.

Ɗan tsalle Faruk yayi gami da rungume kawun, nagode sosai kafin ya sake shi ya kamo hannun Dad ɗinsa Dady nagode.

Kwace hannunsa Dad yayi kaga ni nagaji, me makon ka taren da ruwa, sai ka wani taren da surutu duk suka sa Dariya.

Cikin gida Faruk ya yi da Hanzari yana kiran Mum where are you.

Fitowa ta yi lafiya dai ake min wannan kira haka sai kace anban ajiya.

Dariya yasa gami da rungume ta, albishirin kallon sa ta yi goro, Finally kinyi sirika ya faɗa yana dariya.

Ɗan dukansa ta yi na wasa, wato kai Faruk baka da kunya ko.

Ɗan tsuke fuska yayi kai mum dan Allah shikenan bazan murna ba, dariya suka sa baki ɗaya.

Ɗakin sa Faruk ya yi inda ya kira Ummu hani, tana zaune tana yiwa Usaina Wanka inda Sadija ke shafawa Hasana mai, kukan wayar Ummu hanin yasa Sajida sakin Hasana tai sauri ta miƙo mata wayar bayan ta amsa mata kiran.

Hajiya ce ta taso jeki ki amsa wayar kawo in ɗauraye ta Hajiyar ta faɗa.

Murmushi Ummu tayi, ta ce to kafin tayi ɗaki bayan ta ce Assalamu alaikum.

Shima amsawa yayi kan ya ce wani abu ta gaidashi.

Amsawa yayi kafin yace albishirin ki, goro ta ce.

Anfa ɗaura kin zama matata.

Dariya tasa, wallahi Faruk ka cika wasa sai kace ɗaurin auren film, ummu ta Faɗa da alamu bata yadda da batun sa ba.

Lallai yarinyar nan wato gani sarkin Makarya ta ko.

No Ba haka bane ayi haƙuri kaji angon Ummu hani.

Murmunshin jin daɗi yayi, kafin ya ce to yanzu yaushe zaki tare.

Ita har yanzu bata ɗauki batun nasa gaske ba, biye masa kawai tayi tace yo ni ai duk abinda mujina ya ce shi zanyi koma yanzu sai a tare ɗin.

Daɗi ne ya kuma cika Faruk ya ce karfa daga baya kice bakisan zance ba,..... Haka sukai ta hirar su cike da Farin ciki da ƙaunar juna.

********

Shi ko Alhaji Sulaiman daga gidan nemawa Ɗan Aminin nasa aure, gida ya wuce kusan tun yarinta suke da Alhajin su Faruk wannan yasa kusan komai suke tare komai kuma ɗaya zaiyi sai ɗaya ya sani.

Wannan yasa duk da cewar Alhaji Sulaiman ɗin ɗiyarsa da yake mutuwar so bata da lafiya, bai fasa zuwa neman auren ba.

Direban sa na parker motar ya fito yayi Ɓangaren ɗiyar tasa.

Kamar ɗazu tana kwance yadda ya barta, ƙarasawa yayi ya riƙo hannunta Fatina ya jikin.

A hankula ta ce Dad ka dawo?, eh ya ce ta kuma cewa Dad ya kuka yi da su.

Ɗan kallon ta yayi kafin ya ce, an dai ɗaura jibi zasu kai lefe asa ranar biki.

Wani baƙin ciki ne ya daki zuciyar Fatima, wai an ɗaura auren Faruk da Wata daban ba ita Fatima ba, shiru kawai tayi kafin ta ce Dad kaje ka huta kaina na ciwo banson magana.

Sai da ya kama mata kan tukunna ya fice.

Yana fita ta hau kiran wayar Faruk kusan bugu uku kafin ya ɗaga.

Malama kin fa damen lafiya?, da abinda ya amsa wayar kenan.

Eh ai dole kace na dameka, bugowa nai in maka murna kafin in bugo inma jaje, dan wallahi ina tabbatar maka wannan yarinyar baka isa ka aureta ba, ina faɗa maka bama ita ba babu wata mace da ta isa in raba namiji da ita, Fatima ta faɗa a hasale.

Sai da ka gama cutata sannan kazo kace wata can zaka aura....kan ta ƙarasa yama kashe wayar tako rushe da kuka.

******************

Washe gari kawun Ummu hani yazo tana zaune tana Fanke, Allah ya taimake ta babu mutane dan fitowarta kenan da sassafe ya zo.

Kuɗi ya miƙa mata, ungo nan yace bayan sun gaisa sai da gabanta ya faɗi ta amsa jiki na rawa.

Dubu hamsin ne kuɗin sadakin ki, jiya sunzo an ɗaura muku aure, sai kiyi tunanin lokacin da kike ganin ya dace zamu faɗa musu matsayin lokacin biki ya faɗa bayan ya miƙe, ni zan wuce.

Kasa magana tayi wato da gaske an ɗaura ɗin, har ya fita ya juyo yawwa sun kawo da kuɗin kayan zance Nagani inaso, mun ajiye su agunmu zamu cika mu miki abinda ba'a rasa ba.

To shikenan kawu nagode kawai ta ce, bayan ta juye kaskon farko na fanken da ta kwashe da bata san ko na nawa bane ta bashi, ya amshe ya yi waje.

Tama rasa me ke damunta, duk da cewar kamata yayi tayi farin ciki sai duk take jin akasin haka.

Duk da batasan yadda ake ba anma tasan kawunnan ta basu kyauta mata ba, ai da sai ko sati ne su nema su yi bincike kan Faruk ɗin.

Wata zuciyar ce ta ce mata karki damu Allah na tare dake insha Allah bazai haɗa ki da mugun mutun ba, sai alokacin ta ɗanji sanyi aranta tuna Allah datayi.

Sai bayan ta tashi sannan ta shiga cikin gida ta bawa Hajiya kuɗin ta faɗa mata yadda sukai da kawu.

Ita kanta Hajiya bataji daɗin abinda kawunnan sukai ba, sai dai ɗiya tasu ce ba yadda ta iya.

********

Kamar yadda suka Faɗa kuwa iyayen Faruk kwana uku tsakani aka kawo lefe, lefe ɗan ubansu, kai zaka rantse da Allah cewar ɗiyar me kuɗi zai aura yadda ya zage ya mata kaya iya kaya.

Su kansu dangin ummu hani mamaki iya makaki sukai, yayin da iyaye mata ke ta fatan inama da ace Tata diyar aka kawowa.....

Muje zuwa, Wasa farin girki, Yanzu aka fara labarin, don't forget to follow.

Ummu HaniWhere stories live. Discover now