Shafi na 18

713 137 21
                                    



*Wato ba abin takaici irin ka rubuta chapter ka neme ta ka rasa, na rubuta har zuwa 22, 18,19 da 20 sun ɓace, na kuma manta me na rubuta, sai da na kuma zaman rubutu, the worse part of it littafin ya fara ban haushi, sabida banson rubuta same chapter sau biyu.*

Ummu hani na zaune ita da Kursum suna hira, lokaci lokaci Bala nasa musu baki, wanda yazo cin abinci kasan cewar sun saba da kursum yasa yake ɗan saka bakin.

Suna nan zaune Umman Bashir suka shigo, Bala kasan cewar yasan su yai saurin gaida su, yayin da ita Kuma ummu hani kamar da umma tai da Bashir yasa ta saki fuska so sai, tana faɗin Umma sannu da zuwa ku shiga.

Ke Dakata ba zama muka zo yi ba, bari ma dakata gidan uban waye kika Sanni?, duk Umman Bashir ke faɗe cikin fishi.

Kema dai yaya da wani abu kike ba dole tasan ki ba tunda tana morar ɗanki umman Bushira ta faɗa.

Murmushi Ummu hani ta kuma yi, tamkar bata ji ko fahinci ba mutunci ne ya kawo su ba, ta kuma cewa dan Allah ku shiga ta faɗa tana ƙoƙarin shiga ciki.

Ke dakata baki ji na ce miki ba zama mukazo yi ba, ku baku da gurin da zan shiga in zauna, nazo in miki tsakani da ɗa na ne, ki fita sabgarsa.

Anman Umma.... Ke bansan bariki, ki sauraren dan daɗin bakinki da kini bibin ki duk nasan irinsa bazaimin tasiri ba. Umma ta dakatar da ita.

Sum sum Bala ya tashi ya fi ce, kai tsaye shago ya wuce Bashir na zaune yaba tilawa Bala ya zayyana masa komai da hanzari ya miƙe yai waje.

inda ita kuma kursum haushi ya rufeta ta miƙe.

Haba bayin Allah tayaya zaku zo ku rufe baiwar Allah da masifa, ita ba ita ce ta ke jawo Bashir ba, inta ita ne ma kar yazo, shi ya kawo kansa kamata yai kuje can shi ku masa, ku ce karya kuma zuwa kursum ta faɗa azafa fe dan ita ba gwanar haƙuri ba ce.

Kai!, ke ni zakima rashin kunya, me kike nufi wato ban isa da yaro na ba kome?, umman Bashir ta faɗa a zuciye.

kinga yaya aike kika kyale ta kamata yai ki wanke yarinya da mari inta kawo miki raini wallahi, kinsan yara irin waɗannan ba tarbiya suke da ita ba.

Wa?, ta mare ni, tab! da wallahi bata kuma ba, sannan ai ba rashin kunya nai mata ba gaskiya na faɗa, maganar rashin tarbiya kuma kowa yasan waye mara tarbiya a unguwar nan, Kursum ta faɗa yayin da ummu hani ta daka mata tsawa, kai kace ba sa'ar ta ba ce.

Kursum ummu ta faɗa cikin fishi, me yasa baki da kunya ne, ki shiga gida ba gunki suka zoba ummu hani ta faɗa murya a kausashe.

Sim sim kursum ta shige ba tare da ta kuma cewa komai ba, yayin da ummu ta jiyo ga su Umma tana basu haƙuri.

Umma dan Allah kuyi haƙuri, indai yaya Bashir ne zan yi ƙoƙari ya dena zuwa, kuma indai ni ce nima zan fita sabgarsa.

Ke munafika kina wani sin sin da kai na munafurci, nasani yadda waccan take jin tashen Balaga haka kike ji, to nadai faɗa miki dan wallahi zuwa na, na gaba bazai miki daɗi ba, ki fita sabgar sa dan ni ban shirya surukuta da mai zaman kanta ba...

Haba umma mene haka, ina ni ne kike son in daina zuwa, to mene kuma zaki zo ki dinga ci mata mutunci, ni nake kawo kaina ba ita take jawo ni ba Bashir da ya shigo ya faɗa.

A fusace Umma ta juya eyye sannu isasshe wato da gasken ne baka dena zuwa ba, yanzu uban me kazo yi.

Hannunta ya riƙe muje, fizgewa tai ba inda zani inaso ka sani itama ta sani ni uwarka dana haife ka nama katanga da yarinyar nan, da mutan gidan nan in wallahi na kuma jin ko da abayan idona ka zo ko ka shiga sabgar ta ban yafe ba fuuu ta fita.

Juyawa yai ya kalli inda tayi, ya juyo ya kalli ummu hani, yace Ummu dan Allah kiyi haƙuri bansan....

Hannu ummu ta ɗaga masa karka damu ka tafi, kar fushin mahaifiya ya hauka karka damu uwa tafi komai kana ji tace karka kuma shiga sabgar mu tai ciki da gudu.

Baƙin cikin ummu hani ɗaya kiranta me zaman kanta da umma tai, wato haka ake musu kallo, ita ba kanta take ji ba, yanzu in mutane suka farawa ƙannenta kallon masu zaman kansu ya zata rayu.

Allah ka gani ba yanda zamu yi ne, bawai zaman mu kaɗai muka zaɓa ba.

Dafata Kursum tai mene kike kuka haba ummu, koda son Bashir kike ba wai mutunci kuke ba yaci abinda mahaifiyarsa ta mki kiji farat ɗaya ya fitar miki arai, ki taso ki koma gun sana'ar ki, u are strong, u can endure it, karki bari abu kaɗan yasa ki bar hanyar da zaki nemawa ƙannenki rayuwa mai kyau.

Share hawayenta tayi, tunawa da tai ko mene akwai wasu a ƙarkashinta, miƙewa tayi ta fito, su Aisha duk sunyi carko carko suna kuka .

Murmushi ummu tai, ku kuma mene haka jibeku dan Allah ta faɗa tana murmushi ta amshi muhd sukai soro....



Bana ganin comment ɗin ku da voting ɗinku fa kodai labarin be yi bane a fasa.

Tun inayin rubutun inason rubutawa har na fara ƙosawa inaga ajeshi zanyi kawai sai inna samu faraga na dunga rubutawa tunda ba masu karantawa.

Share and follow pls

Ummu HaniWo Geschichten leben. Entdecke jetzt