Shafi na sha shida

782 71 1
                                    

Kamar Ɗazu girgiza kai kawai Ayatullah yayi yabar Ɗakin.

  Murmushi ya yi bayan ya fita gami da Ɗan bugun goshn sa yabar asibitin, Gida ya wu ce dan yasan yanzu gidan Ya Fatima sunyi bacci.

   Ya yi sa'a Dady ya kwanta ya Parker mota yai Ɗakin sa.

  Kamar Ɗazun kasa Bacci yai, tashi yayi ya ɗauki computer ɗinsa ya hau online, duk a ƙokarinsa na kore tunanin matar mutane, tsoron sa Ɗaya kar ya samu alhakin tunanin matar wani, wanda ya rasa me yasa ya ke tunanin ta, me yasa da ya tuna bugun zuciysrsa ke ƙaruwa.

    Ita kuwa Ummu hani tsaki kawai ta yi, inba wulaƙanci ba kawai cikin Daren nan kai ba jami'in asibiti ba ka banko Ɗakin mutane.

  Hirar su suka ci gaba da Zainab inda ta kwantar da Muhd.

********

Bashir ne zaune yana cin tuwo, Ummansu ta fito daga Madafa ta kalle shi ta girgiza kai, kamin ta ce kai yanzu dan Allah bakajin kunya ace kullum ƙaton ka dakai sai dai ka shigo gida abaka ɗimame.

  Murmushi ya yi kamin ya ce karki Damu Umma, insha Allah na kusa huta wannan gorin, kedai ki cigaba da mun Addu'a very soon zan nemo matar aure.

  Kaji ka baka shirya auren bane, anman inba haka ba ko Bushira da take masifar sonka ai da ka duba.

  Da sauri ya miƙe ya wanke hannu,  ni na fita ya ce yai waje.

  Girgiza kai Umma tayi ita kam zata so taga ranar da Bashir zai yadda ya kalli Bushira a matsayin mace.

   Daga gida Shagonsa ya wu ce ya ɗebi kayan da yasan Su Ummu zasu buƙata yai asibiti.

   Ga mamakin sa an sallame su ta haɗa kayan su Muhd ,shi kawai take jira tana ganinsa ta saki fuska gami da gaida shi cike da jin daɗi ya amsa.

  Shi ya ɗauki Usaina dan har lokacin jikinta bai kwari ba, yayin da yake riƙe da sauran kayan da yazo dasu inda sajida ta goya Muhd ummu Hani ta riƙe kayansu da Hasana.

  Duk wani cike cike da cikon da ake buƙata Bashir ne ya yi, dan Ummu hani kaf kuɗin ta ya ƙare Hajiya ce ma kwanaki ta bada itama abinda ba'a rasa ba.

   Har ƙofar gida mai adai adaita ya kai su, Bashir ya miƙawa Ummu hani kayan da yazo dashi ta ce ina wallahi Ya Bashir mun gode bazan karɓa ba wanda kayi ma ya isa.

   Yai yai ta amsa taƙi, ya ce tom shikenan alamar yaji haushi, itakam Ummu haƙuri kawai ta bashi tai cikin gida, taƙi amsa ne sabida tasan ba wani ƙarfin jari ne dashi ba, ɗawainiyar da yayi da su tayi yawa in ta nuna zata dinga amsar kuɗinsa da cutarwa.

   Cinikin Su ummu ya tsaya sabida babu kuɗin kayan miya fulawa da mai, shinkafar ma wataran gaya sukeci dan itama Hajiya ta ƙarar da kuɗinta.

  Rayuwa ba daɗi sai dai aƙalla ummu takanji sa'ida aranta inta tuna komai tsanani yana da sauƙi.

   Bashir bai san me yasa Har yanzu Ummu bata dawo da Abincin ba, yana son ya tambaya baya son taga yana musu shisshigi, yayi tsanmanin ko so take jikin yaran yai kyau sosai sai dai kuma yanzu gashi ƴan biyu har yawonsu suke, bata dawo dashi ba.

   Yaukam yai ƙundunbala Bayan ya shiga sun gaisa da Hajiya, sun fito shida Ummu hani ya ɗan kalleta kinsan kuwa nayi missing abincin ki, yau she za'a dawo mana dashi ne.

  Murmushi tayi kamin ta ce Bari kawai Yaya kuɗi sukai tsiya, shine Hajiya ta ce in bari a musu Fansho sai ta bani.

  Shiru kawai ya yi ta dube shi ganin yayi shiru lafiya dai.

  Yanzu Ummu daman baki ɗauken komai ba, dan dai kuɗin kayan miya da fulawa bakya tambaya ta.

  Murmushi ta yi bawai, ban ɗaukeka komai bane, banason in ɗorama damuwar da ba taka ba, sannan naga kaima da kanka kai hidima a kwanciyar mu a asibiti shi yasa.

  To naji in kin ɗauken mahinmanci yanzu nawa kuke buƙata, eh to kamar dubu ɗaya da ɗari biyar, anma kusa fanshon ai karka damu.

  Ban tanmayeki ko ankusa ko ba'a kusa ba muje ki amsa.

  Anma.. kinga malama biyoni ya katseta yayin da yai gaba.

  Murmushi kawai tayi ta bi bayansa.

  A ƙofar shagon ta tsaya ya auna mata fulawa da siga ya lissafo kuɗi dubu biyu ya bata.

  Zare ido tai, kai ai sunyi yawa kinga in bakyaso ki zubar amsa tai tana murmushi, shikenan na amsa amma gaskiya Ba shi ne, yanzu ka ɗauko littafin Ba shin ka ka rubuta a gabana in gani.

  Girgiza kai yayi ummu hani akwai pride, shi yasa take kuma burge shi, duk da tana buƙatar taimako but still tana yin iya yinta dan mutunta kanta.

    **********

Abun duniya ya ishi Ayatullah ko yaya ya ke ɓe shi kaɗai tunanin matar mutanen da be san me yasa ya ke yi ba, sai ya mamayeshi, fuskarta muryarta sune suke masa yawo a ka.

  Ada ya tsara wata ɗaya zai yi a Nigeria, ba shiri ya samu ya kammala shirye shiryensa ya koma Makaranta dan gani yake watakil in yama bar ƙasar zuciyarsa zata dena kawo masa unreasonable abubuwa.

      Babu yadda gida basu yi ba ya zauna yaƙi, ya nuna wani abu ne ya taso masa mai mahimmanci dole haka suka haƙura suka ƙyale shi sukai masa rakiya koma.

      ********

Cinikin ummu Hani ya kankama kusan kamar da kullum cikin ɗauwai niya take na ƙanne dana abincin siyarwar ta.

Tun kwana biyar da dawo da cinikin ta haɗa kuɗin Bashir ta kaima sa dakyar ya amsa anmafa tasha mita.

Umman Bushira ce wadda ta kasance ƙanwa ga Umman Bashir ta shigo gidan su Bashir da alamu hankalinta ba'a kwance yake ba yadda yanayinta ya nuna.

  Lafiya dai Bushira me ya faru haka, naganki duk a hargitse.

  Ai bari kawai Yaya matsalar ba tawa ba ce ni kaɗai ada na so in shiru naga dai da cutuwa gwanda aima tufkar hanci.

Towo Lafiya me ya faru umma ta tambaya tana maida hankalinta ga Umman Bushira.

  Eh Daman wannan yaron Bashir ne naga yana ƙoƙarin jawowa kansa jangwan.

  Ware ido Umma tai me yayi na shiga uku ni Hasiya.

Kwantar da hankalin ki bai jawo ba tukun cewa nai yana ƙoƙarin jawowa kansa.

   Ƙishin ƙishin najin yana soyayya da wata yarinya ko ince uwar mata, ashekaru ƙarama ce, anman ta maida kanta uwar mata tunda har shayarwa take.

  Towo bazawara ce ko kuwa shegene da ita inji umma.

  Ba ɗaya ƙanin ta ne kinsan bama shayarwar ce abin ji ba, a'a duk wanda zai aure ta na tabbata nauyi ya ɗorawa kansa, tunda ƙannenta shida a ƙarƙashin ta suke banda wata tsohuwa.

  Towo 🤣 umma tasa dariya, kema dai Baraba da shiriri ta kike, ina Bashir zai je ya ɗaukowa kansa Wannan wahalar, bacin da yasan kansa ma dakyar yake iya riƙeshi.

  Allah yaya ni nagani da idona yadda yake musu wahala inda zakije shagon nasa sai kinga ya faɗa.

  Wai ke tsaya wasa kike ko kuwa, umma ta nutsu.

  Wallahi yaya ba wasa nake ba na ce miki ni ganau ce.

  Ina da sake, zaizo ya samen, dolema ya canja, mace gudama ya aka iya bare ga garke.

    Yawwa gwanda dai ayima tifkar hanci wallahi in ba haka ba kuma kin haifawa wasu ne, tunda nasan ayanzu haka moran da sukai masa baki masa ba.

  Inafa nayi masa ni kullun ina tausayinsa ashe shi yaje ya ƙare a gun wata to da sake.....

  

Ummu HaniWhere stories live. Discover now