20

450 49 0
                                    

Tana fara magana ya ɗago sabida yadda sanyar yar murta ta daki kunnuwansa.Tunda ta fara magana yake kallon ta yama kasa cewa komai har Umar yaja motar suka bar gurin.

  Da sauri ya dubi umar yace Please mu koma, kallon ban gane mu koma ba umar yai masa,sannan ya ce mu koma ina kuma.

  Please juya kar ta bar gun, mtss umar yai tsaki sannan ya ce, kana da matsala Faruk, mu koma muyi mata me?, kasani nasani ba So bane, and she's not your type ma.

  Tsaki Faruk yai shima Please mukoma wallahi inta tafi bazan taɓa yafe maka ba.

  Tsaki shima umar kawai yayi, sannanya juya akalar motar zuwa inda Ummu ke tsaye, sunyi sa'a wahalar mota da ake tasa bata samu adai daita sahu ba.

  Adai dai inda take suka parker motar Faruk ya buɗe ya futo.

   Kamar ɗazun gabanta faɗuwa yahau yi ganinsa, cikin muryarsa me jan hankalin ƴan mata ya mata sallama ciki ciki ta amsa.

  Baki samu mota ba ne? ya tambaya with concerned eh wallahi ta faɗa ataƙaice.

  Ok ko zaki shiga mu ajeki a inda zaki?, a'a kawai ta ce.

  Ok shima ya faɗa, ataƙai ce kamin yace ko zan iya sanin sunan.

  Ummu hani ta faɗa, tana kallon gefe da alamun ƙoƙarin tsaida mota take.

Ok ummu da alamu dai a nan unguwar kike ko, eh ta ce yayi kyau ko za'a min kwatance.

  Ba musu ta masa kwatance bai ce komai ba ya tsaida me adai dai ta sahu ya ce baki faɗan ina zaki ba, Rimi kawai ta ce.

  Shima Rumin ya ce da mai adai dai ta ɗin, yaron ya ce tom ku shiga.

  No ita kaɗai zaka kai, make sure you drop her off a inda zaka ta and ka dawo da ita gida.

  Shiga ko ya juyo yana kallon ummu, tama kasa masa musu kawai ta shiga inda ya ciro dubu ɗaya ya bawa me adai dai ta ɗin, sai alokacin ta ce la'ila wallahi basai ka biya ba.

  Kaga malan kuje ko me adai dai ta sahu yaja abarsa ba tare da yai musu ba.

   amota kuwa suna fara tafiya Umar ya ce,  Tsaya wai malam me kake nufi don't tell me wannan karanar yarinyar itama kokarin sata cikin list ɗin yaran da ka yaudara zakai, umar ya faɗa yana duban Faruk.

  Murmushi Faruk yai  ni na faɗa maka and point of correction kasan ni cikin su ba wadda na nema, su suka kawo kansu and am serious this time wallahi, sonta nake and to cut the story short mata ta nake son ta zama.

  Bushewa da dariya umar yai dafa bakai bane Allah dai ya tsare musu yarinya.

Haɗe rai kawai Faruk yai ya maida hankalinsa ga wayarsa.

 

   Kamar yadda Faruk ya faɗa mai adai daita sahun ya kaita ya kuma dawo ita dan shi kam riba ma ya samu abinsa.

    Agida tunda ta dawo take tunanin mutumin da ko sunansa Bama ta sani ba haka tai ta kirkiro aiki dan kar tunanin ya addabe ta.

  Tana hutawa ta hau gyara kayan miya dan kar dare yai mata su rasa markaɗe.

  Ganin har wurin shida su Aisha basu dawo daga Islamiyya bane yasa ta ce da Hajiya zata takai tabar mata muhd.

  Tana tafe tana saƙe saƙen kutumin ɗazu aranta ko me yasa ya tsaya mata arai oho ita ta rasa gano dalili.

  Sai dai ganin har ta dawo ba wanda ya dawo cikin su Aisha sai hankalinta ya kasa kwanciya ba shiri ta barma hajiya kayan miyan ta ɗora tai islamiyar.

  Tun daga bakin ƙofa hankalinta ya kwanta hango cewar taro ake na wa'azi sai yanzu ta tuna duk wata uku akan tara daliban amusu nasihoyi.

  Ganin ɗaliban musanman yan ajinsu duk sai taji babu daɗi ada habu abu mafi daɗi agareta irinta ganta cikin uniform ko na islamiya ko na boko gani 6
Ƴan ajinsu da suka fara karatu tare tun yarinta har yanzu sai taji tamkar tai kuka.

  Har ta juya zata koma taji Malam Mahmud cikin lasifiƙa ya ce Ummu hani shigo mana.

Jiki asanyaye ta shiga ta samu guri kusa da kursum ta zauna tana sairaron wa'azin da ake yayin da take rungume da Muhd dan ta tawo dashi inta barshi bazai bari Hajiya tai girkin ba.

  Tare suka jero da su Aisha da sauran ƴan ajinsu da suka saba tawowa tare lokacin tana makaranta mutun ɗaya ya ƙaru muhd, tama kasa hirar kawai tafiya take abubuwa da yawa take tunawa ayanzun.

Koda suka zo gurin da suke tsayawa suyita hira kan kowa yai gida kasa tsayawa tai dan ada in sun tsaya ba abinda suke tattaunawa sai shin me zasu karanta bayan secondry school sai gashi tasan yau in an tsaya bazai wu ce ai maganar me ake karantawa ba.

  Sai da safe kawai ta ce musu inda kursum ta bi bayanta sukai gida.

  Tunanin makaranta duk sai ya rage mats tunanin mutumin ɗazu duk da can ƙasan ranta shi ne fal.

Ji take tamkar tai kuka sai dai kukanta na nufin tashin hankalin mutane da yawa duk da tasan kuka rahama ne takuma san in tayi ne zataji sanyi aranta sai dai bata da gun zuwa ta laɓe ta koka.

  Haka tai ta yawo da damuwar ta wanda sai da ta gama komai kowa ya kwanta ya ɗauki alƙur'aninta ta hau karantawa ahankula hawayen ke bin kuma tunta jin kukan zai kwa ce mata ne yasa tai maza ta fita ta wanko fiskarta.

Gyarawa su Muhd lilliɓa tayi sannan ta koma ta kwanta ranta fal abubuwa.

*********

       Yau kusan kwana uku kenan da haɗuwar su, sai dai baizo ba har ta fidda rai da ganin sa tana zaune tana wankin kayan su Usaina, muhd na gefenta yana wasa da kayan da bata wanke ba yaro ya shigo gidan da sallama, wai ana sallama da Ummu hani.

   Shiru tai sai duk sai taji wani iri tunda take yau shine rana ta farko da aka aiko kiranta ko waye oho tama kasa motsawa ta cigaba da wankinta.

    Aisha dake dakin girki na kaɗa miya ta lego kaje kace tana zuwa.

   Sajida Aisha ta kwalawa kira, kizo ki amshi wankin nan yaya zata fita.

   Ummu Sarkin kunya sai kawai ta tsinci kanta da jin nauyin yan uwan nata.

  Hajiya dake gefe ta ce ke ummu kinfa bar mutun dasauri ta miƙe ta ɗaura zanin ta dan tsaf take gami da zarar mayafin ta tai waje.

  Muhammad da yasa kuka ne yasa ta dawo ta ɗaukeshi, Aisha zatai magana ta watsa mata harara tai waje kawai ɗauke da Muhd.

   Faruk ne sanye da shadda sky blue ya juya baya jikin motarsa yana lallatsa wayarsa, kamar yadda ya saba baima ga fitowarta ba bare yaji isowarta.

  Sallamar ta ce tasa ya juyo inda suka haɗa ido ya sakar mata murmushi.

  Ahankula ta gaidashi ya amsa cike da jin daɗi dan shikam bai saba budurwar sa ta gaidashi ba.

   Sun jima suna hira kai ka ce sun saba ya amshi muhd yaita masa wasa musanmam da ya kasance ummu akwai tsafta dan tsaf muhd yake yana ta kamshin humra.

Sai wurin awa guda da zuwansa sannan ya ce zai tafi sallama sukai har ta juya ya ce a'a ina kuma zaki ai bamu gama sallama ba.

Juyowa tai yayin da shi kuma ya juya da alamu abu zai ɗauko a mota.

  Kamar kuwa yadda ta zata sai gashi niƙi niƙi da ledoji kallon hannunsa a'a ko dai miƙa miki ciki zan dan nasan ba bani Muhammad din zakiyi in riƙe ki miƙa ba.

  Da alamun mamaki ta ce towo aikam dai ni bani amsar wannan kyauta nagode haɗe rai yai what me kike nufi.

  A'a ni ba abinda nake nufi kawai dai bazan amsa ba ka gaida gida ta juya tai ciki.

   Tsayawa yai kawai yana kallonta yarinyar farko da ya taɓama kyauta taƙi amsa.

  Yaro ya samu ya ce ya miƙa mata ciki inda shi kuma yaja motarsa yabar gun.

   Yanayin comment da Voting ɗin ku in ya burgeni shi zai sa in posting may be within this week insha Allah
  And don't forget to follow

Ummu HaniWhere stories live. Discover now