21

379 35 0
                                    

Tana shiga Umar ya shigo niƙi niƙi da kaya wai gashi, da hanzari ta ce maza mayar masa ai ya tafi umar ya ce.

  Karɓa kawai tayi ta miƙa ɗaki gami da dawowa dan ci gaba da wankinta.

  Kairiya da ta shigo ne yass ummu ta watsa mata hara malama baki iya sallama ba.

  Nafayi sallama yaya ji ne bakiyi ba, eh ai bazan ji ba tunda na kurmance.

  Komawa Khairiyya tayi batare da ta ce komai ba tayo sallama, Assalamu alaikum, gabaki ɗaya suka amsa sannan ta dubi yayar tasu Yaya na dawo kamin ummu ta ce wani abu ta ce da hajiya Hajiya na dawo.

  Ummu ce ta ce ina kika tsaya, wallahi yaya yanzu aka tashe mu, cewa nai ki rantse eyye.

Wuri wuri Khairiyya tai da ido dan tasan halin ummu duk da cewar yayar su ce sai dai suna shashkar ta tamkar yadda ɗa ke shakkar mahaofiyar sa.

Tambayar ki nake kinyi shiru ummu ta kuma faɗe.

  Wallahi yaya ba ƙarya nake ba yanzu aka tashi girgiza  kai kawai ummu tai har ta cigaba da wankin inda Khairiyya tai ɗaki ta ce Khairiyya.

  Da hanzari khaiy ta juyo ta ce kin tabbata yanzu aka taso, cikin sauri ta ce wallahi yaya ba karya nake ba.

  Aishikenan anman dai kullun ina faɗa muku kuji tsoron Allah ku rike maraicinku ki je ki cire kayan kizo ki tayani wankin nan.

*******

Tun zuwan Faruk bai kuma zuwa ba yau kwana wajen huɗu kenan duk ummu ta damu ita kanta har mamakin yadda ta damu dashi bacin ba wani sabo sukai ba .

  Tana mamakin yadda takejin indai har shine zata iya yadda tai aure duk da cewar tana tunanin ƴan ƙannenta.

    Tun ɗazu ta kasa bacci hirarsu dashi take ta tunowa zumbur ta tashi zaune daga kwanciyar datai ledar da tunda taso ta aje bata kuma bi takanta ba wato wadda ya bata ta janyo.

  Ahankula ta hau buɗewa dan karta tashi ƴan biyu dan Muhammad nauyin bacci ne dashi in ba huɗu tayi ba ya tashi shan koko baya ko motsi in ta kwantar dashi.

     Alawowi ne masu tsada sai kwalin waya samsumg juya wayar tahau yi duk da cewar bata san kan wayoyi ba anman idanunta da kyan wayar sun sa tasan mai tsada ce.

  Ta kusa minti biyar tana juya wayar kamin zuciyarta ta angizata ta buɗe kwalin.

Da alamu ansa wayar acaji sai dai kana gani kasan sabuwa ce dan ko ledar sama ba'a ɗaye ba.

Ahankula ta kunna yayin da tahau dube dube babu komai akai bata fi minti biyu da kunnawa bs kira ya shigo.

   Ido kawai ta bi da wayar har kiran yakatse kamar tare suke wani kiran ya shigo ahankula ta ɗaga da ssllamarta Assalamu alaikum rana ta farko kenan da zamu ce ummu ta taɓa ɗaga waya kuma cikin dare.

  Ta ɗayan ɓangaren sai da yai ajiyar zuciya sannan ya amsa sallamar.

Faruk kenan tun zuwansa gidan su ummi tafiyar gaggawa ta sameshi dole ya tafi duk da zuciyarsa ds ruhinsa tattare yake da yarinyar da shi da kansa mamakin yadda ya mato kan karamar yarinya yake.

Shi ne sai yau kika ga damar duba kyautar tawa ko ya faɗa a shagwaɓance yadda yai maganar duk sai ya bata kunya.

Ummu mutun ce mai kunya da rashin son magana sai dai faruk ɗan duniya ne da yasan salo salo na tafi da mata tuni yai anfani da salon sa wanda yasa duk rashin son maganar ummu sai da ta biye masa.

Dakyar ya haƙura yabarta tai bacci dan shi inta shi ne tai ta magana yana ɗaya daga abinda yakeso da ita shine sanyin muryarta gata kuma Allah ya mata hikimar zance kamar kamar me.

    *********

Cikin ƴan watannin da ummu tai da Faruk tuni ta gama kamuwa da sonsa ga wata shakkarsa da take kai ka ce matar sa ce dan ko kaɗan bata kaucewa maganarsa.

  Tuni sun gama tsara batun aurensu dan kuwa har batun ƙannenta yasan dasu inda kuma ya amince zai zame musu uba kamar yadda ta zame su uwa wannan yasa ummu ta ƙara sonsa girmansa ya kuma ƙaruwa a idanunta.

   Abu ɗaya ke bata haushi dashi shine wayarsa ko yaushe yana duba waya ita faɗan da take masa ma shi ne idonsa anman ko zuwa gida yai kamin ta fito sai tai magana da karfi ko ta ɗan taɓa shi hankalin sa zai dawo gareta dan ya lula duniyar waya.

     Suna zaune suna hira yana shan lemon da tayi masa wanda yake masifar so dan kusan duk sanda zaizo sai yasa ta masa dan yana masa daɗi.

Ya ce albishirin ki ta ce goro jiya Abbanmu ya dawo na masa magana ya amince shida momi sun ce ma kawai in aka ɗaura auren sai mu tare a gida sabida su Muhd daɗi ya cika ummu ji take tamkar ta rungume shi sai dai ina ba wannan damar tama kasa magana sai murmushi take zubawa.

Lalle ma yarinyar nan shike na faɗa miki magana zaki hau taƙe ko kajika tsaya kaga yau zan nuna ma ina cikin farin ciki.

  Hannu tasa ta ɗauki wayarsa let have selfie ta ce.

Burin Faruk ne kamar yadda tasani suyi selfie tare kullum sai ta ce ina sai babban abu yazo.

  Buɗemin ta ce nuna mata fuskarsa yai alamar face lock ne ta haska yasa not recognize yace ok three full zero tana sawa waya ta buɗe inda video ɗin da ya tsayar ta cigaba.

  Sakin wayar da ummu tai ne ya tuna masa da yaufa asirin sa ya tonu wato porn video ɗin da yans kan kallo ummu ta fito ya sa pause suka hau hira shi ta gani.

  Girgiza kai kawai ummu tai ta suri muhd daga cinyar sa tai cikin gida inda ya hau kwala mata kira ina tayi ciki....

Ummu HaniWhere stories live. Discover now