34

415 44 2
                                    

Da sauri ya miƙe ya riƙo ta haba yaya bama haka da ke, kallon sa tayi kafin ta kwace hannun ta ai ba wannan zancen na faɗa maka zanyi tafiyane dan haka dole in tabbatar yarinyar ta tare na kuma yi yadda bazaka iya korar ta ba.

Naji wallahi na amince indai tarewa kike son tayi shine babban burina, abu ɗaya ne dan Allah karki faɗawa su Hajiya abinda kika gani badanni ba ko dan banason su sa ni, a'a sai dan ita yarinyar nasan bazata so ace surikanta sunji kan ta tare kuma a cikin gidan su tayi irin haka ba.

Shiru yaya Ummi ta yi naɗan mintina, kafin ta ce tom shikenan naji wannan bazan faɗa ba, Murmushi yayi yawwa yaya ta abar sona.

Hararar wasa ta watsa masa kafin ta mike bari inje nasan su Amira sun kusa gama haɗa kayan su tom shikenan sai naji yadda kukai da su Hajiyan.

  Faruk ne zaune gaban mahaifinsa inda Abban ke ce wa munyi magana jiya da yayar ka ta ce min ka takura kanason ayi magana yarinyar ta tare, aɗan sauri Faruk ya ɗago kai kafin ya sunkuyar da kan nasa kunya duk ta rufe shi wato tanan yaya ummi ta ɓullo.

Kafin yace wani Abu Abba ya kuma cewa na yanke shawara ko bata yaye yaron ba kawai zanwa kawun nan ta magana ta tare ɗin tunda ai daman ko ta yaye shi anyi tare da su zaku zauna.

Farin ciki ne ya cika Faruk har hakan ya kasa ɓoyuwa a fuskar sa sai dai ya kasa magana Fahintar haka yasa Abba cewa shikenan kaje kuyi magana da ita nanda sati uku sai ka faɗan ya kukayi in yaso sai muji yadda kukai daga baya.

  Kansa a kasa yake ta zuba godiya ɗadi ya cika Abba wai yau Faruk dinsa ne a nutse haka ya kuma yadda aure na kintsa mutun.

  Duk da Farin ciki ne fal cikin Faruk sai dai ɓari guda na ransa na tsoron yajewa da Ummu hani maganar tarewa musanman da ya tuna da har yanzu fa bata gama hucewa ba.

   *****
Fatima ce kwance abin duniya duk ya isheta ji take tamkar ta yi hauka kishi da haushin kanta ya cika ta, ta rasa ada wanne irin hauka ne yasata bawa Faruk kanta duk da kuwa tana mutuwar sonsa sai yanzu ta fahinci ba karamin kuskure tayi ba tunda kuwa gashi ya gujeta ya auri yarinya karama.

  Ganin ta rasa abinda take tunani yasa ta fitowa daga falon nata wayar ta da ta gani a center table da ke main falo yasa ta tuna rabon da ta kunna wayar ankai sati sai alokacin ta tuna da Mansur tsaki tayi yayin da afili ta ce ni na rasa ma uban me ya gani ajikina yake sona.

Har ta wuce kuma ta dawo ta kunna wayar kamar yadda ta zata sakon sa ta fara gani na ya sauka lafiya.

Har ta goge sakon sai kuma ta tsinci kanta da son tura masa da amsa

Ok sannu da sauka kawai ta iya cewa cikin saƙon nata kafin ta fi ce daga falon zuwa harabar gidan nasu.

  Ahankula take shawagi duk da ranta babu dadi sai dai iskar da take kaɗa bishiyun farfajiyar gidan ta sanya ta jin wani sanyi aranta bata san lokacin da ta hau kissima in da Faruk mijin ta ne a irin wannan lokacin suna tare da yaran su da Allah kaɗai yasan Farin cikin da zata shiga.

  Tuni Fatima tayi nisa a tunanin dokin rano sai ji tayi Ana cewa baby na lafiyar ki kuwa da hanzari ta dawo hankalin ta gami da ƙaƙalo murmushi Lah Dad sannu da zuwa.

Kallon ta Dady yayi cikin da damuwa meke damun ki ne duk kinyi baki, dariya ta yi kafin ta ce lah Dady weather din Nigeria ce fa, Kallon ta Dad ɗin yaɗan yi kafin ya girgiza kai nidai na faɗa miki ki faɗam ko mene karki samin kanki a damuwa, Murmushi tayi kafin ta ce Allah dad ba komi.

  Kin tabbata ya faɗa yana kallon ta eh Dad ta faɗa cikie da murmushi, ciki kawai ya shige yabar ta nan inda ta kuma komawa dunitar tunani.

*******
Ummu hani ce zaune ita da ƙawar ta Salma suna hira wadda kusan duk akan karatun Salma ne, yawwa ban faɗa miki ba, Salma ta fada ummu hani da ta miƙe dan zubda ruwan wankin salak din da ta gama yankawa ta ce inajin ki.
  
Admission ya fito na farko ba sunana, da hanzari Ummu hani ta dawo subhanallahi ta faɗa fuskar ta cike da damuwa.

Murmushi Salman ta yi kafin tace kema dai ai list ɗin farko ne, to Allah yasa asamu Salma ta ce amin.

  Anma zanwa Faruk ko Umar magama ɗaya daga cikin su ya taimaka ko yana da hanya inji Ummu hani.

A'a dan Allah karki musu magana Nasani bakyason nemam alfarma.

Tsuke fuska ummu hani tayi ni ɗin wace ce da zance banson neman alfarma bacin ma haka ai Faruk mijina ne karki damu ko me zakice sai na tambayeshi.

Murmushi Salma ta yi kafin ta ce tom mai miji angode suka sa dariya baki ɗaya.

Hasana da ta yi waje da gudu yasa Ummu hani cewa kinji ɗan halak ana maganar sa ya zo.

Kai ah lallai na yadda soyayyar nan ta gaske ce wato tun kan ya shigo kinsan shine wato har sautin motar sa kin sani.

Murmushi Ummu hani tayi wallahi bana ganewa wani zubin saima ya shigo nake sanin yazo Kawai fahinta nayi indai naga Hasana ko Muhammad wani yayi waje da sauri to nasan shine.

Hhh lallai matar nan ni zaki rufe cikin zani to mene aciki dan kinason mijin ki, ni kinga karki min sharri Ummu hani ta faɗa kafin tayi sauri ta ɗauko Muhammad da ke ƙoƙarin faɗuwa sai dai Faruk ya riga ta ɗaukan sa da tuni sun shigo inda yake rike da hannun Hasana.

Cin karon da sukai ne yasa ta dafe kai inda ta ɗago rike da gun yayi saurin ƙarasawa ya rikota mugani badai kiji ciwo ba ko ya faɗa a tsorace.....

Ummu HaniWhere stories live. Discover now