HAUSA ARAB💫💫💫 PART2 PAGE24

392 36 5
                                    

Motsin Ya Nuratu ne ya katse mana hirar Mami ta futa ta kira nurse suka zo suka sake dubata sannan suka kara saka mata wani drip ďin.
Kwana muka yi da Mami muna hira irin wadda muka ďauki lokaci bamu samu nutsuwar yi ba. Ta daďe tana yabawa kokari da karamcin Imamu cikin wannan al'amari, da kuma mamakin chanjawar shi da shiryuwar shi.

Karfe uku Ya Nuratu ta farka, a lokacin ta dawo hayyacin ta sosai, muka yi mata sannu ta amsa a sanyaye, Mami ta ďauki babyn ta nuna mata amma sam babu wani karsashi da murna a tare da ita wanda na tabbatar akan abubuwan da suka faru ne. A karshe ta rufe idanunta kawai hawaye sirara na zirarowa kan kuncinta tana sharewa cikin dabara.

Mami ta tashi ta koma gefen kanta ta zauna a kan kujerar gaban gadon sannan ta dafa kanta ta soma yi mata magana a tausashe.

"Haba Nuratu! Kuka kuma? Ba zaki godewa Allah ba? Allah ya sauke ki lafiya kin haiwu da ran ki da lafiyar ki kin samu ďanki cikin koshin lafiya amma ki dinga kuka?
Idan maganar su Yaya Sulaiman da Badi'a ce Nuratu inda sabo ai yakamata ace mun saba da halin su! Tun suna kanana suke da wannan tsatstsaurar ďabi'ar har suka girma. Tsakanin mu da su kawai sai addu'ar shiriya, Allah ya ganar da su gaskiya ya mayar da su kan tafarki madaidaici!
Laifin Badi'a ba naki bane Nuratu kuma ba zai taba shafarki a idanun mu ba, haihuwar ki ce kawai ba zamu goge cewa ita yi ba amma komai naki namu ne! Billahil azeem baku da maraba da Zara a cikin zuciyata, ban taba kara ki da Badi'a ba sai a lokutan da nake miki nasiha akan biyayya a gare ta saboda haqqinta na uwa da yake kanki. Ban taba tunawa da alakar ki da ita ba idan na kalle ki kuma ban taba kawo wani tunani cewa wani abu tsakaninmu zai chanja saboda ita ba.
Yanzu ba gashi ita ta tafi nice nake zaune tare da ke ba? In ke ďin tata ce zamu zo mu zauna ne ko kuwa ita zata sa kafa ta tafi? Ki cire tunanin abubuwan da take yi kina alakanta kanki da su, baki da alaka da komai cikin wannan al'amarin. Nasan da ciwo, naka naka ne, kuma ba'a taba chanjawa tuwo suna, ba zaka taba jin daďin cewa mahaifinka ne yake aikata ayyuka irin waďannan ba.
Amma sai kiyi tauhidi ki saka a ran ki cewa kowannne bawa da irin rayuwar sa da kuma irin jarrabawar sa, ke taki irin taki kenan sai dai kiyi ta addu'a Allah ya shiryar da ita ya dawo da ita hanya madaidaiciya. Kuma dole kiyi mata biyayya ko yaya take domin ita din mahaifiyar ki ce komai lalacewar ta, kiyi kokari ki sauke wannan haqqin da take da shi a kanki bayan wannan duk wani abu da ýa take bukata a wajen uwa kizo wajena! A shirye nake a kowanne lokaci na baki dukkan gata da kulawar da kike bukata komai girmansu. Kada ki taba raba ďaya biyu tsakanin ki da zara a wajena, sharawara ce, damuwa ce, matsala ce, tallafi na gaba ko na kuďi ki gaya mun indai bai fi karfin ikona ba zanyi miki shi......

Don Allah ki cire wannan damuwar a ranki kinga yanayin da kike ciki ba'ason kina damuwa saboda gudun faruwar matsala! Ki tattara komai ki bar wa Allah kamar yanda muka yi, insha Allah komai zai warware cikin sauki albarkar fiyayyen halitta saw."

A kalla Mami ta ďauki awa daya tana yi wa Ya Nuratu nasiha da ban baki da kwantar da hankali kafin ta shawo kanta tayi shiru ta daina kukan tana rungume da hannun Mami tana sauke ajiyar zuciya. Daga nan kuma tace kanta ciwo yake yi, aka je aka gayawa likita, ya sake yi mata wata allurar sannan ta koma bacci.

Karfe takwas na safe Daddy da Baba ambasada suka zo asibitin, lokacin an tashe ta har anyi mata wanka an bata tea. Amma ciwon kan da bai sauka ba ya sanya suka ci gaba da saka mata drip da allurai, ta sake komawa bacci saboda hutun kawai take bukata a wannan lokaci.

Bayan mun gaisa da su na tashi na ďauko babyn cikin gadonsa an sake yi mi shi wanka an sauya mi shi kaya da wasu brown din colour na H and M. Kyawun shi da kamannin shi da su Baba ambasada ya kara futowa.
Daddy ya dinga shafa kansa yana cewa

"Masha Allah! Masha Allah! Ambasada yaron nan bai mun kara ba, sai yayo photocopying ka! Ko dai cin hanci kake bayarwa ne ni bansani ba?"

Mukayi dariya! Amsabasadan ya karbe shi shima yana murmushi sannan ya yayi mi shi addu'a. Ya sake mikawa Daddy shi yace

HAUSA ARAB PART 2Where stories live. Discover now