HAUSA ARAB💫💫💫 PART2 PAGE 1 BY CUTYFANTASIA

1.3K 63 14
                                    

Wata zabura Daddy yayi daga zaune kamar zai kifa don tsananin dimuwa da tashin hankali! Mami ma saura kadan glass cup din ta ya subuce daga hannunta, tai maza ta taro shi jikinta na tsuma kamar sabon kamun zazzabi.
Kamar saukar aradu haka maganar Mahmud ta rufto musu a ka babu zato babu tsammani babu tunanin ta yanda zai iya sanin hakan.

Halin da suka shiga ya sanya Mahmud jin wani irin tausayin kansa da na iyayen na shi. Shi kansa ba'a son ransa zai nuna musu ya san wannan maganar ba. Amma matukar muhimmancinta a wajen sa ya sanya ba zai shiru a tafi a haka ba musamman da yaji cewa Dada ta tayar da balli akan hakan. Wai yau an wayi gari mutumin da yake tunkaho da shi yake jin sanyi da salama da peace of mind idan ya tuna shi a mahaifin shi ya subuce masa ya koma bare gare shi. Yasan Mami bata haife shi ba kuma sanin mahaifiyarsa bai taba bashi sha'awa ba a ganinsa so da kulawa da tsantsar kaunar da Mamin take masa sun ishe shi a rayuwa. Idan da bukatar yasan wadda ta kawo shi duniya watarana zai sani. Tana raye ko bata raye bai sani ba kuma bai damu ya nemi sanin inda take ba tunda bai taba jin ta neme shi ko wani daga cikin danginta sun neme shi ba.
Gaskiya yana bukatar sanin gaskiyar al'amari game da rayuwar shi. Yana so yasan asalin shi da duk wanda ya shafe shi.

Dakyar ya samu sukunin sarrafa busassun lebbansa ya soma magana cikin taushin sauti.

"Daddy kayi hakuri! Ban nemi jin wannan sirrin domin na tada maka hankali ba, ba kuma don sanin asalina yafi ku muhimmanci ba. Daddy saboda halin rayuwa da kalubalen da ke iya fuskanto ni a dalilin haka. Bazan taba iya chanza ku ba Daddy, ku din iyayena ne na hakika wadanda har abada sunanku ba zai chanza ba a zuciyata. Bazan taba jin feeling din da nake ji gare ku ga wasu mutane ba a duniya. Daddy kune gatana, farin cikina, da kwanciyar hankalina.
Nasan za kai mamakin yanda akai naji wannan maganar zaka so sanin wanene ya gaya mun? A lokacin da kake gaban gadona ranar da kazo kuke waya da Mami Allah ya farkar dani daga halin da nake ciki na dawo hayyacina. Sai dai kafin na samu sukunin bude idanuna kunnena yaci karo da munanan kalaman da har abada nasan bazan sake jin kalamai masu muni irin su ba. Wannan ya sakani cikin halin da na fada na tsakanin rayuwa da mutuwa. Babban dalilin da ya sanya ni rufe idanu na tambayeka Daddy saboda naji cewa Dada ta dau maganar da zafi, tana jin bacin ran yanda ta aje ni a matsayin data dade tana bani a matsayina na bare ba jininta ba. Sannan tayi fushi da ku.
Daddy nasan da wahala but i really  have to go through this! Dole mu fuskanci wannan kalubalen mu warware shi mu kuma fahimtar da duk wanda ya cancanci sanin wannan al'amari yanda komai yake kafin ranar da duniya zata fallasa asirin da kanta.
Daddy you can never keep a secret for a lifetime. You can't! Idan kai ba ka bayyana da kanka ba toh tabbas wataran asirin da kanshi zai tona kansa. Hakan kuma yafi komai tozarshi da tashin hankali! Please Daddy ka nutsu ka kwantar da hankalin ka kayi mun bayanin komai dalla dalla. "

Ajiyar zuciya mai karfi Daddy ya sauke kafin ya soma magana cikin zubar hawaye masu radadi da kunan rai da fallasa asirin halin bakin cikin da zuciyarsa take ciki. MAHMUD shine abinda yafi komai muhimmanci a rayuwar shi domin shine silar mayar da rayuwarshi ingantacciyar da ta zama yanzu. Shine farin cikin da Allah bashi a dunkule, kullum yake warwarewa yana alfanuwa da ni'imar da ke cikin shi. Mahmud is a gift from God!! Allah ne ya bashi ba wani Dan'Adam ba kuma Shi kadai yasan hikimar sa akan hakan.

Mami kam kuka kawai takeyi mai cin rai da tsuma zuciya cikin wani irin tashin hankali da bakin ciki mara misali. Ita kanta ba Daddy ba Mahmud na daya daga cikin rahamomin ubangiji a rayuwarta. Ya shigo rayuwarta tun kafin tasan yanda iyaye suke yi su so Dan da suka haifa, sannan ya hanata maraici da jin zafin matsalar haihuwa ya kuma debe mata kewa. Taci sa'a zamanin akwai tsantsar kara da sanin ya kamata, domin bayan Inna Badi'a babu wanda ya taba furta mata kalmar gori akan Mahmud.
Babu wani bambamcin da take ji tsakanin Zara da Mahmud, kai idan tsantsar shakuwa da soyayya ce ma zata iya bugar kirji tace Mahmud ya doke Zara. Tana watanni bata tuna cewa wai ba ita ta haife shi ba ko tunanin yanda yazo gare ta saboda shagala da tayi cikin kaunarsa.

HAUSA ARAB PART 2Where stories live. Discover now