34

402 50 14
                                    

Sai da muka shiga parlour ya zaunar da ni akan ďaya daga cikin kujerun wajen sannan ya zauna a gefena.
Cikin nutsuwa ya soma yi mun magana

"Zara!"

Ban amsa ba ban kuma ďago na kalle shi ba saboda tsoron ganin yanda yanayin idanun shi ya koma.

"Zara"

Ya kira ni for the second time, shima ban ďago ba sai dai amsawa da nayi cikin sanyin murya.

"Wannan shi ne karo na farko da kika yi mun abinda ya bata mun rai ya kuma sanya mun shakku akan yardar da kika yi dani da kuma rayuwar da take gabanmu ni da ke! Idan har irin hakan zai sake faruwa ko yaci gaba da faruwa toh zaki yi matukar mamakin sauyin da zaki samu a tare da ni, I won't lie to you I cannot take this!

I don't know if I have ever told you this, amma yanzu zan sake gaya miki, for the last time, for the one last time Zara bana so wani dalili ya sanya ki kuma gangancin yi mun magana akan halittar jikina.

Ni mutum ne, mahaifina balarabe ne mahafiyata baturiya dalilin da ya sanya kamannina haka kenan ba zabo ni aka yi cikin hausawa ko fulani aka kebanceni da halitta daban ba, ba kuma wata matsala ko case irin wanda ake samu na jirkitar halitta ko sauyawar abin haihuwa a cikin mahaifiyar sa a dalilin wani condition ne ya faru da ni na zama haka ba. Na ďebo kamanni da siffa da jinin iyayen da suka haifeni ne kamar kowanne normal abun haihuwa saboda haka baki da wani dalili da zai sa ki dinga kallona a matsayin wata halitta daban.

Ni ba bahaushe bane, kaddara ce ta tsallako dani cikin hausawa ba don wannan kaddarar ba bazan taba zama cikin ku ba balle na zama alien.

Abu na biyu shi ne kyau ko farar fata ba sune mutum ba, addini da kyawun hali da tarbiyya da nagarta su suke baiwa mutum kowanne irin kyau, a wajen mutane ma asali sai yazo ya doke su gabaďaya, sau nawa kika ji Inna Badi'a tana cewa kyawun ďan maciji nayi? Sau nawa tana cewa mutum har mutum amma babu tsatso mai kyau? Sau nawa tana cewa Allah ya san niyyar jaki shiyasa bai ba bashi kawo ba? Ma'ana da ina da asali da girman kai da ďaga kan da zanyi sai yafi haka.
A gaban idon ki yarinyar da take sona kamar ranta ta turo mun sako tace ta fasa aurena saboda bata san me zata cewa ýaýan da zamu haifa akan asalin uban su ba........."

Ya dakata ya goge hawayen da suka sauko masa sannan yaci gaba

"A mutanen da nayi mu'amala da su ta gaskiya idan zasu yabe ni halina suke faďa ba siffa ta ba, nagarta ta suke kallo ba kyauna ba, kuma ba don halin nawa ba da ban samu shaida me kyau daga wajen waďannan mutanen ba.

"Ni da ke aure muka yi, rayuwar aure ba wasa bace ba zaman kwana biyu ko sati bane, rayuwa ce da ake fatan mutuwa ce kaďai zata yanke ta saboda haka babu zancen shigo da wasu al'amura daga fannin ďaya wanda ďayan ba zai lamunta ba.

"Zara kada ki kuma kallona da yanayin da kika kalleni ďazu, kada ki kuma yi mun lafazi makamancin wanda kika yi mun daźu banaso! Kuma ba zan lamunta ba, saboda wani abu ne wanda bashi da bambamci da kin soka mun kibiya a kirjina, it reminds me of who I am and where I belong , yana kuma kara mun jin cewa I do not belong a wajen da nake yanzu, yana sakawa naji duka habaice habaice da gorin da aka yi mun sun dawo zuciyata sabbi fil ina jin bukatar sanin inda mahaifina yake da zogin son kasancewa da shi cikin ahalinsa, ina kuma tsanar wanda yayi mun kalamai ko kallo irin wanda kika yi mun saboda haka Zara let it be the last time! Please!!"

Ya mike da sauri ya shige ďakin shi ya kullo kofar ya bar ni da sanyin jiki.
He completely misunderstood me, kuma hakan ya faru ne a dalilin halin da yake ciki na anxiety disorder da kuma depression, kowanne action kwakwalwar shi bata mi shi interpreting din shi dai dai da sauran kwakwalen mutane sai ta sauya mi shi meaning zuwa wani abu wanda ya shafe shi wanda zai dagula mi shi lissafi ya hayayyako da zuciyar shi.

HAUSA ARAB PART 2Where stories live. Discover now