27

400 45 5
                                    

Tare muka shiga cikin asibitin, sai da ya kai ni har barandar da zata sadani da ďakin sannan yayi mun sallama.

"Ba za ka shiga ba?"

Girgiza kai yayi sannan yace

"Ki shiga ina kallon ki sannan na tafi! Dare yayi"

A sanyaye na juya na tafi, na san saboda Mami ne baya son shiga, saboda irin shakulatin bangaro da take mi shi, saboda rashin sakin fuskarta gare shi idan ba haka ba, ai nasan Ya Mahmud mai zama ya kwana a asibitin nan ne ko don saboda wannan jaririn na Ya Nuratu.

Sai da na muŕďa handle ďin kofar zan shiga sannan na juyo na kalle shi, murmushi yayi mun sannan ya ďago mun hannu alamar "bye bye"
Na mayar mi shi da murmushin tare da sa kaina cikin ďakin.

Daga Mami sai Ya Nuratu, kowa ya tafi kasancewar dare yayi. Na gaishe da Mami tare da yi wa Ya Nuratu sannu da jiki.
Mami tace

"Waye ya dawo da ke?"

Cikin sanyi nace

"Ya Mahmud ne"

Ya Nuratu tayi murmushi amma Mamin bata ce komai ba. Bana jin daďin abinda yake faruwa don haka nayi alkawarin gyara matsalar da yardar Allah.

Kwanaki biyu bayan nan aka sallami Ya Nuratu da Asad muka tattara zuwa gidan Dada. Ďakin da yake kusa da nawa aka buďe aka gyara tsab sannan aka kawo kayan bukatar mai jego da jariri aka shirya. Baba Rabi ce take yi wa Ya Nuratu wanka, A.laila ta shirya baby ta kula da shi tare da taimakona.
Ba'ayi wani taron suna ba domin duk ýan'uwa suna nan lokacin da akayi haihuwar, kafin sunan kuma kowa ya kama hanyar garin su ciki kuwa har da Inna Badi'a da family ďin Kawu Sulaiman. Don haka gidan yayi matukar daďi, musamman wannan baby da ya shige raina yayi kane kane. Amal na can Kano babanta ya tafi da ita don haka babu kiriya a gidan, wani lokacin har twins ďin Ya Omar Asim(Daddy) da Arif(Daddyn A.sofy) nake ďaukowa su taya mu jin daďin gidan.

Ina cikin baccin da na kwanta bayan azahar naji ringing wayata, na buďe idanu cikin sauri na saka hannuna kan drawer na ďauko wayar, mamaki ya kamani ganin sunan Imamu, domin tunda yayi tafiyar nan bamu sake magana da shi ba, time to time Ya Mahmud ya kan ce Imamu yana gaishe ni, ni kuma ban taba tambayar shi yana ina ko yaushe zai dawo ba saboda duk su biyun haushi suke bani.

"Hello"

Ya sake maimaitawa for the third time ina can ina tunani. Sannan na nutsu nayi mi shi sallama muka gaisa. Ya ďora da cewa

"Kin ji ni shiru ko?"

Nace

"Ai na ďauka yanzu me karamin karfi ba ya ganin ku"

Yayi dariya sosai sannan yace

"Lallai Zahra baki da kirki amma ba kya jin sakon gaisuwa ta a wajen Mahmud?"

Nace

"Ya Mahmud ne ya haďa ni da kai?"

"No! Ki fahimce ni, I don't want to cause misunderstanding a tsakanin ku! Duk yanda abubuwa suka sauya tsakanin mu ai ba'a chanjawa tuwo suna, it will never erase the relationship we had. So wasu abubuwan sai mutum yana yi yana takatsantsan."

Nayi ajiyar zuciya nace

"Ya Mahmud ba shi da matsala Imamu"

Cikin kaguwa yace

"I know that better! Well yanzu dai ba wannan na kira mu tattauna a kai ba. Akwai important maganar da nake so muyi."

Sai da gabana ya faďi domin ni Imamu tsoro yake bani, abubuwan da yake zuwa yana zakulowa kuma masu matukar nauyi da ďaga hankali ne.

HAUSA ARAB PART 2Where stories live. Discover now