chapter 37

427 59 20
                                    

A maimakon a dauko likita Daddy umarni ya bayar a tafi da su asibiti gabadaya, cikin gaggawa aka saka su a mota aka yi asibiti da su, Daddyn ne kuma ya hana ayi zuga a tafi, Daga A.laila sai Ya Omar da Faisal ne suka tafi asibitin saboda he is sure shock ne kawai ya saka su cikin wannan halin, yana fatan kuma ana zuwa asibitin za'a shawo kan matsalar. sai dai ya kasa daina maimaita kalaman Mahmud na karshe, wai Zaran is pregnant kenan? me ya kai wannan labari dadi a cikin zuciya on this special day? lallai Allah Al-kareemu ne.

suna zuwa asibitin aka karbe su aka basu taimakon gaggawa, Mahmud ya riga farkawa domin Allah ya taimaka zuciyar tashi bata tabu ba, mamaki ne kawai ya kidima shi, Zara ma Allah yayi saving ta da cikinta, an yi mata duka taimakon da za'a yi mata amma doctor yace lallai ta samu kyakykyawan bed rest na sati biyu........

jin hakan da Daddy da yayi waya yace idan ta farka a sallamo su gabadaya, in yaso sai a samu nurse ta dinga zuwa gida tana kulawa da ita.

BAYAN AWANNI ASHIRIN DA HUDU
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Cikin dare Zara ta farka, tana bude ido ta ga A.laila a gefenta hannunta akan goshinta yana shafa mata kai.
ta lumshe idanu cikin kasala ta bude sannan tayi kokarin yin magana a sanyaye

"A.Laila dagaske ne? dagaske ba mafarki nake yi ba Baban Ya Mahmud ne da yar'uwarsa muka gani?"

murmushi A.laila tayi cikin farin ciki ta soma yi mata magana

"Duk abubuwan da suka faru Zara ba mafarki bane, everything is real, komai a gaske yake faruwa yau farin cikin da muke ciki ba kadan bane Zara, ga wani sabon farin cikin kuma da kuka sake taho mana da shi, me zamu yi wa Allah idan ba godiya ba?"

murmushi kawai Zara take yi, she is too weak to ask all the questions da suke ranta don haka ta koma ta gyara kwanciyar ta taci gaba da wannan mayataccen baccin da ya kasa barinta.

ba ita ta wartsake ba sai washegari da safe, Mahmud kam a gida ya kwana bayan an sha tataburza da shi don cewa yayi kafar shi kafar Zara sai da Daddy yasa baki.

Faisal ne ya dauke shi zuwa mississippi yana bashi labarin yanda zuwan bakin ya kasance

"Friend akwai matukar almara da mamakin cikin lamarin nan, Daddy has done duk wani kokari da zai yi wajen gano inda family din ka suke amma wallahi ko'ina aka bi babu nasara babu wani haske, duk wani taimako nigerian embassy da ke Lebanon sun baiwa Daddy amma an kasa binciko inda family din ku suke a Beiruit.
dalilin da ya sanya Daddy fara rashin lafiya mai tsanani kenan, don ya ga wankin hula na neman kai shi dare................

kwatsam rannan da yamma Daddy yayi recieving call daga Daddynka da kan shi, sumewa ne kawai bai yi ba don mamaki da dadi, wannan wayar ce sanadin warwarewar komai, har zuwa shekaranjiya da suka taho bakidaya suka sauka a Abuja bamu san komai game da yanda akai abubuwan suka faru ba.
Anyi tunanin wacce dabara za'a yi muku ace ku taho da gaggawa an rasa saboda kowa ya gane baka da niyyar dawowar a kusa, shine Mami tace maka Daddy ne bashi da lafiya yake bukatar ganin ka.

wannan zaman da akai na jiya saboda tarbar ku ne da kuma warware mana komai sai dai halin da kuka shiga ya katse wannan niyyar.
musamman wani sabon farin cikin da kuka taho mana da shi.................."

Faisal ya dara sannan yace

"friend an kusa zama Daddy!"

Mahmud ya harare shi yace

"duk yayan da kuka haifa mun basu isa a kira ni Daddy ba sai yanzu?"

Faisal yayi murmshi yace

"gumin ka ai gumin ka ne"

Mahmud ya kwada masa duka a kafada ya kyalkyale da dariyar farin ciki. a kullum addu'ar shi ga Mahmud itace Allah ya kawo masa farin ciki da walwala a rayuwar shi domin he has gone through alot, ya ga rayuwa kuma ya sha bacin rai, gashi Allah ya kawo mi shi mafuta a lokacin da aka kusan fidda rai da hakan.

HAUSA ARAB PART 2Where stories live. Discover now