29

454 41 2
                                    

Zagaye shi nayi na dawo gaban Mami ina ci gaba da magana sai ya funcikoni na koma baya musamman da ya ga yanda Mamin take sauke numfashi cikin wahala kamar me haďiyar allura.

Nayi taga taga zan faďi Ya Omar yayi sauri ya tsayar dani, sannan ya kama hannuna da niyyar barin falon dani naja na turje cikin wani irin karfin da fushin da nake ciki ya bani.

"Kyale ta Umar! Sake ta"

Dada tayi maganar a kausashe, sannan ta kalle ni tace

"Zara zo nan"

Bai sake nin ba sai da ya kaini har gaban Dada na tsuguna sannan ya nemi gefenta ya zauna hankalin kowa ya dawo kaina.

"Zara ki nutsu kiyi mun bayani me yake faruwa? Me Mamin tayi? Me kika ji ko kika gani?"

Sai naji zuciyata ta sake karyewa, but Dada ce take tambayar don haka ban ja lokaci ba na soma magana cikin dushewar muryar da taci kuka ta koshi.

"Dada kunsan cewa Mami tana ďauke da ciwon sugar da hawan jini?"

Cikin kaďuwa Dada ta zaro idanu tana kallona, bama ita kaďai ba babu wanda bai shiga mugun shock da jin wannan maganar ba.

"Dada Mami ta daďe cikin damuwa da bakin ciki a gidan ta amma cikin mu babu wanda ta ga ya cancanci ta gaya mi shi, babu wanda tayi sha'awar yin sharing damuwar ta da shi balle ya bata shawara not even A.laila. haka ta dinga rayuwa cikin tashin hankali da ciwon zuciya a karkashin azzalumin mutum irin Alhaji Mukhtar.............

"Wannan result ďin yayi watanni shida da futowa amma Mami bata gaya wa kowa komai a kan shi ba......tana cikin damuwa bata faďa ba, ta zauna a ciki to the extent ďin da damuwar ta haifar mata da manyan ciwuka irin wannan still bata gayawa kowa ba taci gaba da zama a ciki tana hakurin da watarana zai iya yin sanadin ranta......

"Dada Alhaji Mukhtar ya karbi kuďin Mami naira miliyan ďari biyu ya hana ta, still bata gayawa kowa ba, yayi mata barazana mai muni still bata gayawa kowa ba, ya nuna mata true colour ďin shi ya tabbatar mata da kowanne irin mutum ne shi amma Mami bata gayawa kowa ba.

"And finally Dada yau watanni biyu kenan da Alhaji Mukhtar ya rubuta takardar saki ya bata amma bata gaya wa kowa ba tana zaune cikin gidan.....
Dada yaushe Mami zata yi magana akan damuwar da take ciki?
So take sai ranar da bakin ciki ya kashe ta mu je gidan mu tsinci gawar ta? Me Mami take nufi da ajiye wannan sirrin a zuciyar ta ita kaďai?..........."

Salati Dada ta ďauka tare da fashewa da kuka, haka A.laila da Ya Nuratu,
Ya Mahmud ne yayi maza ya koma gefen  Mamin da jikinta yake wani irin rawa kamar ana kaďata ya rike ta sosai yana zubar da na shi hawayen.

And then........
Daga wannan rawar jikin tayi loosing balance daga zaunen ta faďi, Ya Mahmud ya tallafota yana kiran sunanta, amma ina....tuni ta futa daga hayyacinta.

A guje Ya Omar ya tashi yana cewa

"Mu tafi asibiti! Mu tafi asibiti!"

Dukan mu muka mike cikin tsantsar tashin hankali, Ya Sadik ya taimakawa Ya Mahmud suka ďaga Mami cak suka futa da ita zuwa mota.
This is something da bai taba faruwa ba, ban taba ganin Mami cikin halin matsananciyar rashin lafiya ba balle ta kai ga kwanciya a asibiti.
She is a strong woman! She is as strong as a rock........
Kullum tana tsaye da kafafunta akan iyalanta, kullum cikin hidima da mu take da dukkan karfin ta da aljihunta da kokarin ta da tunanin ta....
Burinta kawai ta ganmu cikin farin ciki da kwanciyar hankali ba tare da kallon kanta ko la'akari da nata farin cikin ba.
She always puts us first a kowanne hali a kowanne yanayi a kowanne lokaci.

Bamu taba tunanin zamu kai asibitin da ranta ba, musamman ni da na soma kukan danasanin tona wannan maganar, da nasan abinda zai faru kenan da ban bi ta wannan hanyar ba ko da zan faďa ďin.
Muna zuwa nurses suka ďauko gadon marasa lafiya aka shimfiďe ta kamar gawa aka shigar da ita emergency likitoci suka dukufa kanta suna bata taimakon gaggawa domin su kansu sun tsorata da halin da take ciki

HAUSA ARAB PART 2Место, где живут истории. Откройте их для себя