🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅
*🤦♀️🤦♀️KOMAI NUFIN ALLAH NE🤦♀️🤦♀️*
*By*
*DEEJAH*
*UMMU FU'AD & AFNAN)**MARUBUCIYAR*
*1_RASHIN UWA*
*2_RAYUWAR GIDAN KAWUNA*
*3_KALAR TAWA KADDARAR*
*4_RAYUWA TACE HAKA*AND NOW IS
*KOMAI NUFIN ALLAH NE🤦♀️*
🅿️3️⃣6️⃣
Wanka Naga yayo yazo yazauna tare da kallona yace
"Shafamin Mai " tashi nayi tare da dakko wani zani nadaura na karasa jikin madubi na dakko Mai,
Shafa Masa nayi sannan na dakko kayan na ajiye nakoma gefe na zauna,
Jawo rigata nayi nasaka tare da daura dankwalin nayi tagumi kawai,
Kallona yayi sannan ya tashi ya dauki kayan yasaka nidai Ina kallonsa bance komaiba Kuma banyi yunkurin tashiba har Saida ya Gama ya kalleni,
Nagane abinda yake nufi don haka natashi na dauki hulan da nafito da ita nasaka Masa nare da saka Masa agogo sannan na fesa Masa turare na dakko takalmi na ajiye a wurin kafarsa,
Duk yin aikin nakeyi don karyace nayi laifi afasa zuwan don haka naketayin kokai cikin nutsuwa,
Bayan na Gama yimasa komai nakoma jikin madubi na gyara fuskata na dauki mayafina na yafa sannan na rataya jakata da dauki waya natsaya Ina jiran Naji mezaice,
Kallona yaketayi har nagama natsaya saiji nayi yace
"Gaskiya kinyi kyaufa sosai" kasa nayi da kaina bance komaiba,
Murmushi yayi yace
"Muje ko" cikin sauri hade da zumudi nakama hanya ai jinake kamar natashi sama Banda murna Babu abinda ke Raina,Munshiga mota get man ya bude Mana muka dauki hanya sai murmushi nakeyi kamar me,
Kallona yayi yace
"Mezaki kaimusu tsaraba to"
Cike da dokk nace
"Ai wancan ledan cake nayi musu saikuma kajin da kace nasoya atafi dasu" kallona yayi yace
"Nasan dasu ai yakamata akara wani abun"
"To meza'a Kara" Shiru yayi baikara cewa komaiba,
Hakan yasa nagane yakai makura a magana kenan Nima shirun nayi,
Gani nayi yayi parking a kofar wani shop Nan muka shiga da kanshi ya zabo abubuwa akayi Leda biyu muka fito,
Muna zuwa kofar gida cike da doki nafara kokarin bude kofar mota Naji a kulle sai jinai yace
"Banason wannan abunfa da kikeyi Allah zamu juya" ai inajin haka na nutsu natsaya Ina kallonsa saikuma yayi murmushi yace
"Kigaidamin Ammi da sauran Yan gidan idon nadawo zanshiga mugaisa yanzu ina sauri zanje wudil zanyi wani abune Ina dawowa zanzo na daukeki" zaro idanu nayi nace
"Basai da dare zakazo ka daukeniba?"
Hararata yayi yace
"Kinmanta sai gobe zanzo na daukeki kina sane karfe Tara na dare jinginmu zai tashi Amma kike wannan maganar ko?"
Yatsina fuska nayi nace
"To saika dawo"
Murmushi kawai yayi da taune lebe yace
"Zan kamaki wallahi" sannan ya dakko Leda Daya cikin Wanda aka siyo yace
"Gashi nan wancan na Momy ne idon kikaje saiki kaimata" karba nayi tare da godiya sannan na sauka na bude bayan motar na dauki Leda Daya cikin biyun Dana taho dasu daga gida Ina fadin
"Yauwa gashi nan nabar ajiyata anan please kar atabamin fa" murmushi yayi yace
"Saidai kuwa idon banji yunwaba don idon kikayi wasa saidai kiga Babu komai aciki lokacin da zan dawo,
Murmushi nayi nima nafara tafi Ina fadin
"Allah da saika biyani kuwa" tada motar yayi Ina tsaye a kofar gida ya wuce nikuma nashiga da sauri sauri gudu gudu,Da sallama nashiga dakin Ammi da guduna Nan nasami deejah zaune tana cin tuwo aikuwa muka rungume juna sannan na koma wajen Ammi na rungumeta saikuma nafara hawaye,
Murmushi tayi tare da zaunar Dani a kusa da ita tace
"Menene na kukan Kuma kefa girma kikeyi kina cin kasa kullum"
Shiru nayi Ina goge hawayen sannan na gaidata ta amsa muka shiga Hira da deejah tanata tsokanata da idanu don Ammi na zaune,
Tsaraban na mikawa Ammi tashiga budewa Nan taga turaruruka da sabulai da yawan gaske kallona tayi tace
"Wannan duk acikin kayan lefan naki Kika debosu da yawan gaske?"
"Ahah Ammi yanzu muka biya aka siyosu" rike Baki tayi tana fadin
"Shidai Deen baya gajiya da kashe kudi wallahi shekaran jiyafa yazo da dare yakawo Mana kayan abinci harsu kaza namanta ban fada mikiba kiyi Masa godiya, Kuma shine yanzuma ya Kara yimana wannan siyayyar Allah sarki mungode sosai Allah ya saka da Alkairi ya Kara bude yabaku zaman lafiya dukkanku dake da Deejah" Amin muka amsa dashi Amma a cikin ranmu,
Nan tanunamin tsarabar da deejah ta kawo musu harda atamfa aikuwa nayi Mata godiya muka Kara lulawa fira Nan take fadamin Ashe hajiya batanan yanzu tatafi unguwa Wai taje dubiya can daura itada maman Salim,

YOU ARE READING
KOMAI NUFIN ALLAH NE
Fantasylabarin da ya samu rubutowa daga DEEJAH UMMU FU'AD AND AFNAN, labari ne mai taba zuciya tare da sassanyar soyayya, karku bari a baku labari ku karanta kuyi vote ku comments