🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅
*🤦♀️🤦♀️KOMAI NUFIN ALLAH NE🤦♀️🤦♀️*
*By*
*DEEJAH*
*(UMMU FU'AD & AFNAN)**MARUBUCIYAR*
*1-RASHIN UWA*
*2-RAYUWAR GIDAN KAWONA*
*3-KALAR TAWA KADDARAR*
*4-RAYUWATACE HAKA*AND NOW IS
*KOMAI NUFIN ALLAH NE*🤦♀️
🅿️0️⃣4️⃣
Karasowa yayi ya shiga cikin motar ya zauna batare da yayi maganaba,
Babu Wanda yayiwa wani magana har suka dauki hanya saida ya nisa don kansa sannan ya saki ajiyar zuciya yace
"Please idon kazo wani store din katasaya zan siya wani abun please aboki"
Banza yayi dashi saida ya Kara kallonsa ya maimaita masa sannan yace
"Naji ai"
"Nazata kazama kurma ne ai"
Banza yayi dashi har suka karasa jujun labu store sannan ya Parker motar tare da komawa ya kishingida jikin kujerar,
"Wai kana nufin bazaka rakaniba ne?"
"Wallahi bazan shigaba idon kaima kafasa muwuce kawai don nakagu na karasa kana gani magrib ya kusa dai muje layin nasu musami sallah"
Kallonshi kawai yayi sannan ya sauka daga motar yana murmushiKaya ya siyawa deejah na alfarma Amma abinda ya bashi mamaki bayan ya gama siyan kayan shine yadda ya zauna ya dauki komai biyu kuma iri daya saidai kalane kawai ya banbantasu har ya dawo mota yana mamaki Wanda ya rakosa da kayan ya saka masa a bayan motar,
Shiga yayi ya zauna tare da kallon abokin nasa yace
"Aboki waikuwa deejah tanada kanwa ne?"
Kallon mamaki yayi masa sannan yace
"Saboda me kayimin wannan tambayar?"
"Kaji matsalarka mutum y tambayeka sannan kayi masa tambaya kaima"
Murmushi yayi sannan yace
"Bata da kanne ko kadan ita daya hajiya ta haifa kasan na fada maka da hajiya da mami iyayensu daya, to ita bata da kanwa bata da Yaya ita dayace a gidansu tana karama Abbanta ya rasu"
"Ayyah Allah sarki Allah yaji kansa yayi masa rahma, to yanzu saidai a kwashe sauran kayan don wlh bansan ko meyasaba na dunga dakko abubuwa na mutum biyu fah"Murmushi yayi yace"ai babu damuwa sai tabawa wata kawarta Deenah don tarema suka yimana abinci dazu da mukayi waya haka tacemin kilama tana gidan, kaga kawai saisu dauka su biyun ai"
Tsaki yayi yace
"Nibabu wata Deenah da nasiyawa Kaya kawai na siyawa deejah ne ba aata Deenah bah"
Dariya Salim yayi yace "shikenan mungode sosai Allah ya saka da alkairi ya Kara budi"
Banza yayi dashi don yagama bata masa rai wani Wai yabawa wata Deenah shiyawani San wata Deenah da za,a Raina masa hankali ace yawani bata Kaya Allah badan karya batawa abokinsa Raina dasaiya koma gida yanzu ya fasa zuwa,Yana cikin tunanin bai ankaraba yaji yayi parking ashe har sunkaraso,
Salim ne yace "oga ankaraso fah muje"
"Noooo kafara shiga before na shigo"
OkayFita yayi ya shiga cikin gidan tare dayin sallama suna falo kusa jiyoshi nan hajiya ta amsa masa tare da fadin "yarona karaso Mana"
Shiga yayi tare da zaunawa kusa da kafar hajiya yana gaidata Deenah ma gaidashi tayi ya amsa yana murmushi
Hajiya ce tayi magana tace
"Salim ya mamin taku tana lafiya, yasu Fatima da yusrah duk suna lafiya"
"Lafiya kalau hajiya sunce a gaidaku sosai, Mami tace tana nan zuwa insha Allah"
Murmushi tayi tace"to Masha Allah, Allah ya kawota lfy ai nima naje bata Nan nasami yusra ita kadai agidan"
"Eh haka tacemin wallahi"
Mikewa hajiya tayi tana fadin
"Bara naje daga ciki"
"Afito lafiya hajiya" yafada yana shafa kanshi,
Duk wannan abun da akeyi Deenah CE kadai zaune don Deejah ta gudu daki tunda taji sallamarsa tanaji hajiya ta shige daki ta fito cikin sanyinta tana tafiya a hankali,
Mikewa tsaye yayi yana kallonta yana sakin murmushi har takaraso kusa dashi tana gaidashi amsawa yayi yace
"Ina zuwa bara naje wajen wancan miskilin tare muke fah Wai bazai shigoba saina fara shiga"
Murmushi tayi tace
"Ashe yau anzomin da Yaya nah aikuwa tare Dani za'aje shigowa dashi"
Dariya yayi kadan yace
"Muje to"
Juyowa tayi ta kalleni tace
"Dear taso muje waje"
Girgiza kaina nayi nace
"Ah,ah kije kawai ina Nan sai kundawo"
Kallona Salim yayi yace
"Au bazakijeba?"
Daga Kai nayi kawai ina murmushi ganin haka yasa deejah fadin
"Muje kawai my love tunda tace haka nasan bazataba, Ni Allah miskilancin Deenah har mamaki yake bani"
Futa sukayi daga Nan bansan kome yace mataba,

YOU ARE READING
KOMAI NUFIN ALLAH NE
Fantasylabarin da ya samu rubutowa daga DEEJAH UMMU FU'AD AND AFNAN, labari ne mai taba zuciya tare da sassanyar soyayya, karku bari a baku labari ku karanta kuyi vote ku comments