*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅
*DEEN NA DEENAH NE*
*CIGABAN*
*🤦♀️🤦♀️KOMAI NUFIN ALLAH NE🤦♀️🤦♀️*
*BOOK TWO*
*BY*
*KHADEEJAH SANI (Journalist)*
*MARUBUCIYAR*
*1-RASHIN UWA*
*2-RAYUWAR GIDAN KAWUNA*
*3-KALAR TAWA KADDARAR*
*4-RAYUWA TACE HAKA*
*5-KOMAI NUFIN ALLAH NE*AND NOW IS
*DEEN NA DEENAH NE*
🅿️3️⃣3️⃣-3️⃣4️⃣
Yau kimanin satin mu biyar kenan yara sunyi wayo sun kara girma kamar basu ba,
Nima bangare na nakara girma sosai gashi nayi wani kyau kamar banice na haifi su Amatullah ba,Momy tana yawan zuwa dubamu hakama deejah don duk kwana biyu zuwa uku zaka ganta agidan wai tazo wajen baby's dinta nidai sai dai nayi murmushi kawai,
Yauma zaune muke a falo muna hira da ita cikin raha sai ga Yaya ya shigo ranshi a bace da kyar ya Amsa gaisuwar da deejah me masa ya haye sama don ko sannu da zuwa na Bai Amsa ba,Ganin na Kara gyara zama ina dakko wani labarin ya sakata dakamin duka tace
"Ke bazaki tashi kije kiji abinda me damun mijinki ba kina ganin a halin daya wuce dai kinsan da gari kalau saiya tsaya munyi Dan rahan da muka Saba dai"
Yatsina fuska nayi nace
"Tab maizan masa babu Inda zanje nidai"
Haba ta rike tana kallona sannan tace
"Ke banason wulakanci fa menene hakan kuma don Allah"
Yatsina fuska na karayi nace"Ke nifa yanzu idon kinganni a sama to wallahi sai idon baya nan nake hawa na gyara dakin idon ma wani abun nakeso zanyi Amfani dashi yana can har saiya fita nake shiga don wlh naji kashedin da momy tayimin kuma kullum innar murja saita Kara yimin fada na kula da yarana karna dunga manne masa inje yara basu Isa yayeba a yayesu nima kuma ga matsalata ta dinkin Nan haka kawai tab" na karasa ina gyara zama na kalleta,
Gani nayi kawai tasaki baki tana kallona batace komai ba har nagama sannan tace
"Gaskiya kekuwa akwai sakara wallahi me kike nufi da hakan wai? Kina nufin bakya zuwa kidan rage masa zafi Amma wallahi Deenah baki taba bani haushi ba kamar yau saboda wulakanci shine kike guje masa hmmm wallahi wajema kika samu don kingansa bawan Allah babu ruwanshi ko?"
Murmushin nayi nace
"Nikuma baiwar mutane ko saina zauna a kasheni da raina ko to baki isaba wallahi"
Matsowa tayi kusa Dani tana fadin
"Don girman Allah kije ki sameshi ko yayane please kuma ai bacewa nayi kuyi wani abuba kawai kije ki kula dashi ya sami nutsuwa ke bakisan yadda ake yin yan dubaru bane to bari kiji yadda abun yake"
Nan tashiga koramin bayani,
Muna cikin haka wayana tayi kara na dakko don Jin ringing din dake tashi nasan shine,
Dagawa nayi tare da sallama Bai Amsa ba yake fadin
"Kawomin ruwan tea yanzu" shiru nayi Jin ban Amsa ba ya sakashi fadin
"Ko bakijini bane"
To kawai na fada ina ajiye wayan sannan na Mike tsaye ina fadin
"Please jirank ina zuwa zan kaimasa tea na dawo" kanta ta gyadamin da itama Amsa waya take,

ESTÁS LEYENDO
KOMAI NUFIN ALLAH NE
Fantasíalabarin da ya samu rubutowa daga DEEJAH UMMU FU'AD AND AFNAN, labari ne mai taba zuciya tare da sassanyar soyayya, karku bari a baku labari ku karanta kuyi vote ku comments