🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅
*🤦♀️🤦♀️ KOMAI NUFIN ALLAH NE🤦♀️🤦♀️*
*BOOKS TWO*
*BY*
*KHADIJAH SANI ABDULHAMID🥰*
*(UMMU FU'AD & AFNAN)**MARUBUCIYAR*
*1_RASHIN UWA*
*2_RAYUWAR GIDAN KAWUNA*
*3_KALAR TAWA KADDARAR*
*4_RAYUWA TACE HAKA*
*5_KOMAI NUFIN ALLAH NE*AND NOW IS
*KOMAI NUFIN ALLAH NE🤦♀️🤦♀️ BOOKS TWO*
🅿️1️⃣0️⃣
Alhmdllh jikin deejah yayi sauki don kwananta uku a Bata sallama hakan yayiwa kowa dadi,
Gidan hajiya aka wuce da ita daga hospital din don dama haka maman Salim din tace ayi duk da baiso hakanba Amma haka ya hakura,
Shine yakaisu gida don da safe aka sallamesu,
Bansan da maganar sallamar ba nashiga kitchen ina kokarin Dora breakfast naji ya biyoni Yana fadin
"Baby karki Dora girkin nan yanzu don bada wuri Zan fitaba sukuma su Salim an sallamesu"
To kawai nace Ina maida tukunyar Dana dakko don har yanzu bana wani sake masa sosai,
Fita yayi na bisa da kallo sannan Nima na fito,
Dakin da nakoma da kwanciya nashiga na Fara gyarawa bayan nagama nadawo falon Shima na gyarashi sannan nakoma dakin,
Wanka kawai nayi sannan na koma saman gado na kwanta tare da lulawa duniyar tunani,
Gaskiya ni kaina nasani inada kishi sosai abin yaki fitarmin arai har yanzu ina gano yadda Deen yake kashewa wata murya Yana kwantar dakai hmmmm namiji kenan,
Nafada a fili ina gyara kwanciya kawai sai Jin mutum nayi na dungureshi kallonshi nayi tare da kauda kaina gefe ina niyyar tashi naji ya jawoni jikinsa Yana fadin
"Haba deenah dama haka kike da riko ban saniba yanzu abinda kikeyimin ya kamata kenan? Ke kanki kinsan bakya kyautawa shikenan hira Mai tsayi tadaina shiga tsakanina dake kin raba Mana daki, menayi Miki don Allah please kifadamin" ya karasa Yana hade hannuwanshi,Hawaye nafarayi sannan na bude Baki nace
"Nayi hakanne don nasaba da rashinka a kusa Dani don nasan nanbada jimawaba dole Zan iyayin kwanaki batare Dana gankaba kokuma najika akusa dani shiyasa nayi hakan" kallona yakeyi cike da mamaki sannan yace
"Sbd me kike fadar hakan?""Sbd nasan zaka yimin nisa haka nakeji ajikina duba da yanayinka dakuma abinda kake shirin dakkowa"
"Haba deenah kidunga yimin adalci don Allah..."
Katseshi nayi da fadin
"Nima kayimin adalci don Allah kaji tausayina karka muzantani karka gujeni banyi maka komaiba meyasa kakeson yimin haka wallahi ina sonka ina kaunarka banason abinda zai rabani dakai inaji ajikina zaa rabamu.....Kum......Kuma...d...d" nakasa karasa abinda Zan Fadi na fashe da kuka Mai cinrai,Kallona yakeyi jikinsa yayi sanyi zuwa can yace
"Kawai don kinganni da jawahir shikenan saiki tada hankalinki jawahir fa yar uwatace Kuma wadda nakeso na aura kamar yadda na aureki to menene abin daga hankali acikin wannan menene abin rabuwa ina sonki ina kaunarki haka itama sonta da nakeyi shine dalilin dayasa Zan aureta saidai saboda ke momy da dady sun hanani aurenta sunce basusan magana ba to ya kikeso nayi bayan a dalilinki an hanani auren wadda nakeso nake kauna haba deenah kiyimin adalci mana, kibarni da abinda yake damuna Amma kema sai kikara doramin wata damuwar kibarni naji da damuwar hanani auren jawahir da suke shirinyi ina sonta inaji ajikina idon ban sametaba Zan iya shiga matsala nikaina bansan lokacin Dana Fara sontaba please and please tawan kitaimaka min nasamu na aureta ko zanji sassauci acikin zuciya ta don Allah" yafada Yana had a hannu biyu,Kukan da nakeyi tun tuni yama tsaya nakasa cigaba da yinshi don ganin yadda yakeyin maganar kan gaskiyar shi ashema kuka waje yake samu,
Jin yadda yayine ya sakani kasa Koda digon hawaye natsaya inata binsa da kallo,

YOU ARE READING
KOMAI NUFIN ALLAH NE
Fantasylabarin da ya samu rubutowa daga DEEJAH UMMU FU'AD AND AFNAN, labari ne mai taba zuciya tare da sassanyar soyayya, karku bari a baku labari ku karanta kuyi vote ku comments