19-20

325 27 8
                                    

🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅

*DEEN NA DEENAH NE*

            *CIGABAN*

*🤦‍♀️🤦‍♀️KOMAI NUFIN ALLAH NE🤦‍♀️🤦‍♀️*

*BOOK TWO*

*BY*

*KHADIJA SANI ( journalist)*

*MARUBUCIYAR*
*1-RASHIN UWA*
*2-RAYUWAR GIDAN KAWUNA*
*3-KALAR TAWA KADDARAR*
*4-RAYUWA TACE HAKA*
*5-KOMAI NUFIN ALLAH NE*

AND NOW IS

*DEEN NA DEENAH NE*

*KOMAI NUFIN ALLAH NE🤦‍♀️🤦‍♀️ BOOK TWO*

🅿️1️⃣9️⃣-2️⃣0️⃣


Momy ce tafito daga part din dady tayi hanyar kitchen batare da ta kalli muhseen dake zaune ba,
Tana kokarin dama kunu muhseen ya shigo Yana fadin
"Momy zantafi office nayi latti ma" batare da tajuyo ba tace
"Allah ya tsare hanya saika dawo, anan zakabar Fatima kenan?"
"Eh momy idon na dawo zanbiyo na daukesu insha Allah"
"Allah ya dawo dakai lafiya"
Tafada Tana fama garin kunun,
Jin bai fitaba Kuma bai amsa ba ya sakata ya sakata juyowa Tana fadin
  "Lafiya dai ko?"
Shafa Kai yayi sannan yace
"Amma momy sai nake ganin hukuncin da kikayiwa Yaya Kamar yayi tsauri da yawa please kibari yau deenah ta koma gidanta don Allah kibarshi da hukuncin hanashi Kara auren kawai ya isama kumafa yacemin wallahi shi bai daketa ba kawai anan gidan ne yaji Tana yimasa rashin kunya ya mareta Amma Babu wani Abu bayan nan please Mom kibarta koma bazai Kara ba"
Tunda ya Fara maganar ta saki Baki Tana kallon ikon Allah wato hada Mata Kai zasuyi su sakata a gaba kenan aikuwa duk zata iya dasu don haka ta hade rai tare da fadin
"Karka Kara sakamin bakinka a maganar nan kafita daga cikinta inba so kake laifinshi ya shafeka ba kaficemin daga nan"
Tana fada ta juya taci gaba da aikinta,

Ganin yadda tayi masane ya sakashi fita jiki babu kwari,
Tausayin yayan nashi na Kara shiga ranshi don ganin yadda momy ta dauki zafi dashi haka,

Bansan ko meke faruwa ba nidai ina daki kwance ina bacci sai Fatima da yarinyarta dake zaune a kujerar dake dakin Tana chatting a wayarta,

Ban tashiba sai bayan Azhar nayi sallah Nasha kunun da momy tayimin sosai sannan na koma na kwanta a kan kujerar falon,

Haka naci gaba da zama agidan momy Tana Kula Dani sosai ba kadanba bataso taga ina tunani ko nayi shiru yanzu zata Fara tambayata ko sokike ki koma gidanki idon kinaso kikoma kifadamin Babu alkunya tsakaninmu kinji diyata, saidai nayi murmushi nace
"Ahah momy wallahi Babu komai nanma nafijin dadin zama Akan can,
Munje gidan duba Abba tare da momy ranar nadanji karfin jikina tace muje mu dubashi tunda naji dama dama,
Aikuwa naji dadin hakan don dama inata tunaninshi a raina kawai dai inajin kunya ne bazan iya cewa zanje ba,
  Daga gida muka wuce gidansu deejah muka Kara ganin masu jego yarinyar tayi wayo sosai Mai sunan hajiyan su deejah Ana cemata mameesha,

Yau kimanin kwanana goma kenan agidan momy Amma Babu Deen babu alamarshi tun Randa aka kaini asibiti rabon da nasakashi a idona kenan ga wata iriyar kewarshi da nakeji inason ganinshi sosai Amma haka na dake nake nunawa momy Babu wata damuwa don nasan yancina takeson kwato min,
Ina falo a kwance na tashi zanje dakin dake jikin na momy don nanne inda na koma da zama gabaki daya,
Nazo shiga ne najiyo muryan momy Tana fadin
"Ai nizaka nunawa iyakata ko shine rabonka da kazo ka dubata tun ranar da mukaje asibiti kuma ina lure da ita baka kiranta a waya kaji yadda take shine yanzu zaka kirani kacemin wai kayi tafiya ne ko to wallahi......"
Iya nan naji nidai nashige dakin na koma saman gado na kwanta tare da daukar wayata wadda kullum idon naji kukanta sai nayi adduar Allah yasa shine naji muryarshi ko yayane Amma Ina dubawa sai naga bashidin bane,
Tunani nashiga yi batare da nasan yawan lokacin da na daukaba awurin,

KOMAI NUFIN ALLAH NEWhere stories live. Discover now