🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅
*🤦♀️🤦♀️KOMAI NUFIN ALLAH NE🤦♀️🤦♀️*
*By*
*DEEJAH*
*UMMU FU'AD & AFNAN)**MARUBUCIYAR*
*1_RASHIN UWA*
*2_RAYUWAR GIDAN KAWUNA*
*3_KALAR TAWA KADDARAR*
*4_RAYUWA TACE HAKA*AND NOW IS
*KOMAI NUFIN ALLAH NE🤦♀️*
🅿️3️⃣7️⃣
Mun sauka malesia lafiya kalau munsami wani abokinsa dayake zaune acan yazo ya daukemu yakaimu gidansa Wanda suke zaune shida matarshi sai yaranshi guda biyu,
A falo muka zaune matarshi Mai kirki tana yimana sannu da zuwa bayan mungaisa ne muka tashi mukashiga dakin da ta nuna Mana namu,
Nanma falone babba sai bedroom guda biyu don gidan babbane sosai na karamiba,
Abakin gadon dakin da muka shiga nazauna Ina fadin
"Washsh Allah nah" kallona yayi yace
"Sannu dear kingaji ko?"
Murmushi nayi nace
"Allah bayana ne ya gaji"
"Ayyah sannu Bari muyi wanka sai nayimiki tausa ko?" Murmushi kawai nayi,Tashi nayi nashiga bathroom na hada Masa ruwan wanka nafito,
Samunsa nayi kwance a bakin gado kafafunsa na kasa ko takalmi Bai cireba, na karaso wajen nace
"Ga ruwan wanka can nahada" kallona yayi yace
"Ok ciremin kayan sai muje muyi"
Dan zaro idanu nayi na kalleshi ganin bamani yake kallona yasakani karasawa na cire Masa takalmi, zaunawa nayi awajen nayi tagumi ganin hakan yasakashi tasowa ya zauna Yana nunamin wuyan rigar jikinsa hakan yasa na tashi na fara kokarin cire Masa,
Bayan nagama ne na koma na zauna sai kawai Jin mutum nayi Yana fadin
"Tashi na cire Miki rigarki muje muyi wanka muyi sallah" zaro idanu nayi Ina niyyar yin magana naji Yana fadin
"Allah sai munyi tare Donma kiji mundaina raba wanka indai Ina gida azaune Dole tare za'ayishi don haka kitashi kidaina Bata Mana lokaci" turo Baki nayi nace
"Ai ruwan na mutum daya na hada"
"Muyi ahakan kawai zai ishemu" hakan da yace yasakani tashi Dole banyi niyyaba,Bayan munyi wanka munyi sallah muka fita falo mukaci abinci sannan muka dawo daki muka kwanta muhuta,
******************************
Yau kwananmu hudu kenan Babu inda mukaje tunda mukazo shima Banda fita masallaci Babu abinda ke fiddashi don ko babban falon gidan ba sosai muke zamaba Saida dare muhadu mu hudun muyi fira sannan kowa ya shige daki,
Soyayya kawai mukesha ta ban mamaki don bantaba tunanin zan iya sakewa da Deen hakaba Amma sai gashi nasake dashi mutana zuba sha'anin mu,
Saidai abinda ke damuna wani lokacin idon na fita naje kitchen don na Taya matar gidan aiki sai nasameshi yanata tunani narasa tunanin me yakeyi Wanda da banga yanayin hakaba idon na tambayeshi sai yacemin Babu komai haka nake hakura na rabu dashi,Ta bangaran Deen kuwa yamajin Dadin yanayin zaman kasar gakuma madam a gefe anata zabga soyayya kamar ba gobe, Amma abinda yakasa ganewa yasan tunanin jawahir da yakeyi ga wat irin soyayyarta da yakeji acikin zuciyarshi Wanda yakeji bazai iya dadewar da zasuyiba batare da yaji Koda muryar taba, wannan abun shikadaine yake damunsa,
Yanzuma zaune yake Yana zabga tunaninta yakasa aikata komai da system dinsa dake gabansa, wayarsa ce tayi Kara hakan yasa ya dauki wayan don ganin Mai Kiran,
Salim ne bayan sungaisa ne suka Fara fira Nan Salim ke tambayarsa yaushe zai dawo kuwa yafara kewarshi,
Cikin sanyin murya yace
"Nafasa dadewar da nace zanyi Salim saboda wata Yar matsala wallahi" cikin sauri yace
"Meya faru dama Naji muryanka wani iri lafiya?" Cikin kasa da murya don gudun kar Deenah tajishi don tana kitchen suna girkin dare yace
"Salim ina cikin tashin hankali narasa yadda zanyi da rayuwata tunda nazo kasarnan Banda tunanin jawahir yarinyar Alhaji sammani Babu abinda nakeyi wallahi nakasa samun saukin abun acikin zuciya ta kullum abun gaba yakeyi cikin dare Koda nafara bacci sainaji kawai natshi saidai nayita tunaninta jinake dama tana kusa Dani inajin wani irin sonta a raina, tun ina kaucewa kar Deenah ta gane harta gane don jiya Saida tasakani gaba infada Mata abinda ke damuna harda kukanta narasa amsar da zan Bata bansan me zan fada mataba please abokina kabani shawara" ajiyan zuciya Salim ya sauke yadan nisa tare da kallo deejah dake kwance kanta na Kan cinyarsa don itacema tasakasa Kiran Wai zata gaisa da Deenah Saida ya Gama kallonta tana kallonsa sannan yace
"Innalillahi wa'inna Ilaihir raji'un, abokina menene hakan to mehakan yake nufi kenan?"
Cikin sanyin murya yace
"Wlh Nima banganeba inason Deenah banason abinda zai Bata Mata rai banaso tagane halin da nake ciki ace yau baifi sati ukuba da aurenmu Amma nafara tunanin wata, haba ai abun Babu Dadi gaskiya kabani shawara Don Allah don wlh jinake idon ban gantaba cikin kwanakin nan kamar bazan iya rayuwaba"
Ganin yadda deejah keta kallonsa yasakashi cewa,
"Kabari zamuyi waya gobe insha Allah"
Allah ya kaimu yace sanann Salim ya tambayi Deenah yace
"Tana kitchen suna girki kasanta batason zama waje Daya" murmushi yayi yace
"Agaudata idon tazo kace Mata nakira zasuyi magana da deejah takirata idon tazo" to yace tare da fadin
"Agaida deejah da baby nah please"
Saida yayi murmushi Yana shafa cikin deejah yace
"Gasu nan suna jinka suna amsawa" sallama sukayi,

YOU ARE READING
KOMAI NUFIN ALLAH NE
Fantasylabarin da ya samu rubutowa daga DEEJAH UMMU FU'AD AND AFNAN, labari ne mai taba zuciya tare da sassanyar soyayya, karku bari a baku labari ku karanta kuyi vote ku comments