p5

247 21 0
                                    

🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅🍅

     💔 *DEEN NA DEENAH NE*💔

🤦‍♀️🤦‍♀️ ( _Ci gaba komai nufin Allah ne_🤦‍♀️🤦‍♀️

*BOOK TWO*

*BY*

*KHADIJAH SANI ABDULHAMID🥰*
  *(UMMU FU'AD & AFNAN)*

*MARUBUCIYAR*
*1_RASHIN UWA*
*2_RAYUWAR GIDAN KAWUNA*
*3_KALAR TAWA KADDARAR*
*4_RAYUWA TACE HAKA*
*5_KOMAI NUFIN ALLAH NE*

AND NOW IS

*DEEN NA DEENAH NE*

*CI GABAN KOMAI NUFIN ALLAY NE, BOOK TWO*

*ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH*

*INA KARA GODIYA GA ALLAH SUBHANAHU WATA ALAH DAYA KAWONI WANNAN LOKACI DA RAINA DA LAFIYATA FATAN MUNYI SALLAH LAFIYA, ALLAH YA KARBI IBADUNMU YAKUMA TSAREMU DAGA DUKKAN SHARRI, INA MAI KARA GODIYA GA ALLAH DAYA BANI DAMAR CIGABA DA RUBUTA WANNAN LITTAFI, YA RABBIS SAMAWATI WAL ARDI, ALLAH YADDA KABANI IKON FARASHI ALLAH KABANI IKON GAMASHI LAFIYA, ALLAH KA KARAMIN LAFIYA AKAN WADDA NAKE DA ITA, ALLAH KA YAYEMIN DUKKAN DAMUWATA DA TAKE DAMUNA, ALLAH KASAKAWA IYAYENMU DA MAFIFICIN ALKAIRI, ALLAH KA YAFEMIN DUKKAN KURA KURAN DA ZANYI ACIKIN WANNAN RUBUTU DA WANDA NASANI DA WANDA BAN SANIBA, ALLAH KA BANI IKON KAMMALAWA LAFIYA👏*

*Wannan littafi sadaukarwane ga mahaifiyata da mahaifina taurarina abun alfaharina, Allah ya saka muku da Alkairi, Allah ya jamin da ranku, Allah ya kara muku lafiya da nisan kwana Amin*

*Wannan labari na DEEN NA DEENAH NE cigaban (KOMAI NUFIN ALLAH NE) labarine kirkirarre banyishi don tozarta waniba ko wulakanci*

*Wannan littafi kashi na biyu na kudine akan FARASHI mai sauki* #100 kacal👌🏻

*Gamai bukatar wannan littafi zai iya neman wannan number din kamar haka* 07067750885
*Domin sanin ta yadda zaku biyu kudin karatu dakuma shiga group*

*FREE PAGE 5*

Buga kofar falon da akayi ne yasakani tashi na bude ganin momy ya sakani fadada fara'a ta ina fadin
"Sannu da zuwa momy" murmushi tayi tana fadin
"Yauwa diyata ya gida ya zaman kadaici Kuma" murmushi nayi ina bude firij nace
"Alhmdllh momy" nafada ina ajeye drinks da cups na zuba mata aciki ina gaidata,

Amsawa tayi tana fadin
"Tashi a kasa kidawo kusa Dani nan kizauna" tashi nayi cike da kunya na dawo kusa da ita nazauna ina murmushi,

"Daga gidan mus'ab nake nace Bari na biyo naganki kwana biyu babana Bai kawomin keba naganki"
Murmushi nayi nace
"Aikuwa momy naji dadin ziyarar nan nagode sosai"
Tashi nayi na kawo mata drinks da cake na ajiye tare da zuba mata lemo na zauna,
  Kallona tayi sosai sannan tace

"Deejah inason kifadamin tsakaninki da Allah, menene yake faruwa tsakaninki da mijinki a gidan nan?" Gaba nane ya fadi dajin abinda tace nidai nasan babu abinda ya hadani dashi sai ma kwanciyar hankali sabo da nake fuskanta Acikin gidan don bayason abinda zai batamin Kai saidai abinda ya bani tsoro kardai ko nice nayi masa laifi ban saniba,
Shirin da nayine yasa momy dafani tana fadin
"Na daukeki a matsayin 'yar Dana haifa inajin sonki acikin zuciyata don haka karki boyemin abinda ke faruwa a gidan nan don Allah ki fadamin gaskiya" kallon momy nayi wadda ta dawo kujerar danake zaune ta zauna bude baki nayi a hankali Ina fadin
   "Momy wallahi Allah kuwa babu abinda yake faruwa saidai ban saniba Kila nayi masa wani laifin ne bai fadamin ba ya fada Miki Amma ko yau dazai fita lafiya kalau muka rabu" saikuma na fara hawaye ina fadin
"Momy don Allah kifadamin laifin da nayi masa wallahi zan gyara Kuma zan bashi hakuri akan laifin da nayi masa har saiya yafemin"
Murmushi Naga Momy tayi tace
  "Karki damu kinji diyata babu abinda mijinki yace kinyi masa Allah yayi Miki Albarka, kawai dai na tambayeki ne ko akwai wata matsalar Amma babu abinda mijinki yace kinyi" shiru kawai nayi Amma jikina yayi sanyi bansan abinda na aikatawa Deen ba Wanda ya kasa fadamin saidai ya fadawa momy a jikin nakejin akwai abinda ya faru kokuma yake shirin faruwa,

Ganin yadda momy take ta yimin kalamai  masu dadi yasaka na saki Raina mukasha hira har Saida tayi sallahr Azhar da la'asar sannan tace zata tafi,
Daki nashiga na dakko turaren wuta da humra cikin Wanda momyn deejah ya bani danaje na kawo mata aikiwa taji dadi tana sakamin albarka,

Har wajen motarta na rakata ta wuce nan nadawo ciki nafara sabon tunani akan maganar momy gashi tace karna nunawa Deen komai game da maganar da mukayi da ita,

********************************

Bangaran momy kuwa tafe take tana tunanin wannan lamarin itadai tana kan bakanta bazata taba yadda da bukatar Deen na ko kadan,
Abinda ya faru da safe tafara tunawa,
Suna zaune ita da dady saiga Deen ya shigo bayan ya gaidasu ne sun amsa suna tambayar deenah yace tana lafiya nan yafara fadin
  "Dady dama inason na fada maka ..........ummmm......umm to kuma" sai yayi shiru shidai dady idanu ya zuba masa kawai,
Momy kuwa ganin hakan yasa tace
"To babana kodai na fita nabaku wajene sirri zakuyi" murmushi yayi yana Sosa Kai yace
"Ah'ah momy AI maganar harda ke duk ina neman amince warku"
"To babana muna jinka kayi bayanin ka Kai tsaye"
Saida ya Kara sunkiyar da Kai sannan yace
"Dama maganar jawahir ne dadynta yace kaje ayi magana a saka Rana" cikin mamaki dady yace
"Ranar me Kuma za'a saka babana?"
Cikin sanyin murya yace
"Bikinmu da ita don mungama daidaita kanku kum....."momy ce ta katseshi da fadin
"Babana Anya kuwa kanada hankali kasan me kake fada kuwa banma gane maganar da kakeba kwata kwata watanka nawa da aure shine zakazo da wata magana, watanka bakwai fa da aure ko shekara Daya bakayiba kake wani maganar aure"
Shiru yayi ya kasa magana,
Dady yayi gyaran murya Yana fadin
"Babana bangane maganar da kakeba kana nufin aure zaka Kara kenan?"
Cikin kasa da Kai ya dagawa dady Kai sannan ya Dora da fadin
"Kuyi hakuri dady da momy wlh bansan meyasa nakeson auren jawahir ba, tun washegarin ranar da muka bar kasarnan nafara tunaninta inaji idon ban aure taba bazan iya Ray......." Momy ce ta katseshi cikin daka masa tsawa tace
"Dallah rufemin baki nizaka zowa da maganar banza da wofi kana wani sunkuyar da Kai na munafurci to wallahi baka isaba baza ayi wannan haukan daniba kwata kwata watanka nawa da auren yarinyar can zakazo da wata magana Mana to nidai ban aminceba kaji na fada maka" tana kaiwa nan tamike tabar falon,

Kallonshi kawai dadi ya cigaba dayi zuwa can yace

"Naji abinda ka fada yanzu mekake bukata daga wajenmu nida momynka" cikin sanyin murya yace
"Amince warku nake bukata"
Murmushi yayi irin nasu na manya tare da mikewa tsaye yace
  "To ban aminceba sai ayi gaba Kuma"
Yana fadin hakan yayi shigewar sa bedroom,

  Ya Dade zaune dafe da Kai sannan ya tashi ya tafi,
Haka yayi yinin yau a hospital babu dadi gashi aiki yayi masa yawa ga Salim baizoba deejah batajin dadi,

Wannan dalilin shine abinda yasa momy zuwa gidan deenah don taji abinda ke faruwa saidai Kuma taji akasin haka don ta yarda da yarinyar nan dari bisa dari ta yarda da abinda tafada,

Haka taita driving tana tunanin wannan lamarin har taje gida.


*Please my fans kuyi hakuri da rashin jina kwana biyu wallahi abubuwa sunmin yawa shiyasa bana samun yimuku typing, dalilin da yasa kenan banfara karbar kudin kowa ba don akwai mutane da dama da sukayimin magana zasu biya kudi na dakatar dasu please kuyi hakuri insha Allah zuwa bayan sallah komai zai warware nagode da soyayyar ku gareni👏*

*ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH*

*Another beautiful year of my life has come, I'm over the moon as today is my birthday🎂🎂🎂*

  *I'm so grateful to almighty Allah for the opportunity to see another birthday, the miracle of life is a gift from Allah, so I pray today with thankful words🙏🙏*

*🎂🎂 Happy birthday to me🎂🎂*

*By*

*Khadija(UMMU FU'AD & AFNAN)*

*Allah kasa mudace duniya da lahira😢*

KOMAI NUFIN ALLAH NEWhere stories live. Discover now