AƘIDA TA

666 42 0
                                    

_*AƘIDA TA*_

*PART1*
_Page 2_

*written and edited by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*

Bismillahir rahmanirrahim, da sunan Allah me Rahama me jin ƙai, Wannan littafi ƙirƙirarren labari ne banyi shi dan cin zarafi ko cin fuska ga wani ko wata ko wata ƙabila ba, idan har wani ko wata yaga wani abu daya yi kaman ceceniya da rayuwar sa ko ƙabilar sa Amin Afuwa banyi dan cin zarafin wani ko wata ba.
Wannan littafin mallaka tane, ban yadda a juyamin labari ta kowane fanni ba ba tare da izinina ba.

What's App : 07063065680
Watpad : Ayshercool7724
Gmail : Www.ayshertadam@gmail.com

************************************

Wata Babbar Mace ce Zaune a cikin wani katafaren falo me girma sosai, cike yake da kayan more Rayuwa, Aƙalla zata kai shakaru hamsin, Amma kaman 'yar shekara talatin da biyar saboda hutu idonta sanye da glashi ta nutsu sosai tana danna Computer tana shan tea.

Wata matsashiya ce ta shigo falon a ƙalla za ta kai shekaru Ashirin da bakwai, tazo ta zauna a kusa da Matar.
Ba tare da Matar ta ɗago ba tace "Ya a kayi ne? Nasan akwai damuwa tunda na ganki yanzu meya faru?" ta ƙarasa maganar tana kallon matashiyar.

Ta ɗan yatsuna fuska tace " Mummy kin san wani abu?"

"A'a sekin faɗa" matar ta bata Amsa

Cikin shagwaba tace "Mummy ki duba girman gidan nan da cikar sa, kalli dukiyar dake cikin gidan nan, Amma mota ɗaya tak na mallaka, ko ɗan direba ma ba'a sama min ba, Amma kalli 'yar masu gida motocin ta nawa? Direbobi nawa ta wulaƙanta ta sallama a dawowar nan tata? Har motocin me gidan nan take hawa in ta ga dama gaskiya ana nuna mana wariyar launin fata, banda cin fuska da wulakanci da muke fuskanta seka ce wasu Bayi"

Matar ta cire glashin fuskarta tace

"Ramlah me kike so inyi? Alhaji Baya jin magana ko ganin girman kowa sena 'yar sa, abunda take so shi yake yi, Sannan duk abubuwan nan da suke faruwa na ɗan lokaci ne, Amma me kike so ayi? "

"Mum Mota nake so a canzamin sannan nima a ɗaukar min direba, bama mota ba motoci nima in dinga kece raini yadda yakamata, kalli daular da muke ciki, Amma a ce se abunda yarinya ƙarama take so akeyi, Mummy ina son inyi birthday ina buƙatar kuɗaɗe masu yawa fa wanda zan burge ƙawaye na dasu, Sannan naji labarin Akwai filayen da gwamnati za ta yi gwanjonsu a GRA ya kamata ace kin mallaka"

"Hmm Ramlah kenan samun wannan abubuwane masu Sauƙin samu a hannun me gidan nan, Amma kin san seda izini kokuma ince yaddar 'yarsa ko?"

Ramlah tace "Amma Mummy ba yadda za' ayi in samu kuɗin a hannun ki? Kina matarsa amma ace se Abunda 'yarsa take so haba dan Allah, yakamata ace Akwai wata Dama da zaki dinga mallakar kuɗaɗe bayan wanda yake baki"

"babu wannan damar, dan duk kuɗin dazan fitar seda sanin Lawyern sa, dan haka ba yadda zanyi, Karki manta muna da kyakkyawan shiri a ƙasa shiyasa sam bana damuwa, ni yanzu so nake in lallaɓa shi Amal me ta tafi turkey ta ci gaba da karatu a can"

Ramlah tace
"shikenan Amma yakamata kiyi wani abu akai kar wannan damar ta wuce mu, Amma kafin wannan ya batun canza motarfa?"

Mummy tace "Wannan kuma sekin yi tsani da 'yar masu gida, tana magana ko mota goma kike so kamar kin samu, batun kuɗi kuma zan tura miki kuɗi Account ɗinki base munjira ba, Amma ki same ta in ta yadda za tayi masa magana a baki wata motar"

AƘIDA TAWhere stories live. Discover now